Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza
Published: 17th, September 2025 GMT
Kwamitin bincike mai zaman kansa na Majalisar Dinkin Duniya, ya fitar da wani rahoto mai zargin Isra’ila da laifin aikata kisan kiyashi a zirin Gaza.
A cikin sabon rahoto da ta gabatar a ranar Talata, MDD ta zargi shugaban kasar Isra’ila Isaac Herzog, da firaministan kasar Benjamin Netanyahu, da kuma tsohon ministan tsaro Yoav Gallant da “kimsa kisan kiyashi.
Rahoton ya tattara batutuwan da suka shafi farar hula kai tsaye, ciki har da yara, ya kuma bayyana cewa kisan kiyashin da ake yi ya fi yawa fiye da yadda aka yi tashe-tashen hankula a baya.
Masu binciken sun kuma tabbatar da cewa da gangan Isra’ila ta haifar da yanayin da ke barazana ga rayuwar Falasdinawa ta hanyar toshe hanyoyin samun muhimman kayayyaki na wannan al’umma.
Rahoton ya biyo bayan wani bincike da aka yi na tsawon shekaru biyu, kuma ya yi nuni da yadda ayyukan Isra’ila ke a matsayin kisan kare dangi.
A martanin da ta mayar, Isra’ila ta yi watsi da sakamakon binciken da cewa “karya ce “, ta kuma bukaci da a rusa hukumar nan take.
A sa’i daya kuma, kwamitin bincike na MDD ya yi kira ga kasashe da su daina baiwa Isra’ila makamai da kayan aikin da za a iya amfani da su wajen aikata kisan kare dangi.
Fitar da rahoton na zuwa ne mako guda gabanin babban taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, inda ake sa ran kasashe da dama za su amince da kasar Falasdinu a hukumance.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran da Saudiyya sun bukaci hadin Musulmi game da halin da ake ci a yankin September 17, 2025 Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza September 17, 2025 Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza September 17, 2025 Akalla Falsdinawa 78 Ne Suka Yi Shahada A Yau A Gaza. September 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari A Tashar Jirgin Ruwan Hudaida Dake Yamen September 16, 2025 Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki 5 A Wajen Taron kere-kere . September 16, 2025 Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta. September 16, 2025 Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana September 16, 2025 Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi September 16, 2025 Pezeshkian: Ta’addancin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Kan Kasar Qatar Zalunci Ne Ga Diflomasiyya September 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Isra ila ta
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi
Gwamnatin Amurka ƙarƙashin Donald Trump ta sake sanya Najeriya cikin jerin “Ƙasashe Masu Matsala ta Musamman” saboda zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi.
Wannan zargi ya biyo bayan jawabin da Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya yi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya a kwanan baya.
Barcelona ta shiga zarwacin Victor Osimhen Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDPA lokacin taron Shettima ya bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin abin tausayawa, inda ya hi kira da a tabbatar da zaman lafiya ta hanyar kafa ƙasashe biyu masu zaman kansu.
Bayan jawabin nasa, wasu ƙungiyoyi suka fara yaɗa labarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya, duk da cewa mutane da dama sun ƙaryata jita-jitar.
A ranar Juma’a, Trump ya wallafa wani rubutu a shafinsa na X, cewa Kiristoci na fuskantar barazana a Najeriya.
Ya yi iƙirarin cewar masu tsattsauran ra’ayi suna yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya .
Ya umarci ɗan Majalisar Amurka, Riley Moore da shugaban kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar, Tom Cole, su binciki lamarin, sannan su gabatar masa da rahoto.
Shugaban ya ƙara da cewa ƙasarsa ba za ta zuba ido yayin da irin wannan “ta’addanci” ke faruwa a Najeriya da sauran ƙasashe ba.
Ya lashi takobin cewar Amurka za ta ci gaba da kare Kiristoci a duniya baki ɗaya.
Bayan wannan furuci, wasu sun zargi Trump da amfani da matsalar tsaron Najeriya don samun goyon bayan siyasa.
Har yanzu Gwamnatin Najeriya ba ta yi martani a kan lamarin ba, amma jami’an gwamnati a baya sun bayyana cewa rikice-rikicen da ake fama da su a ƙasar suna da nasaba da ayyukan ta’addanci, fashi, da rikicin ƙabilanci, ba addini ba.
Kalmar “Ƙasa Mai Matsala Ta Musamman” na nufin ƙasashen da Amurka ke ganin suna take haƙƙin ’yancin addini, kuma hakan na iya sa wa ta ƙaƙaba wa Najeriya takunkumai.
Idan ba a manta Najeriya ta fara shiga jerin irin waɗanda ƙasashe tun a shekarar 2020.