Ina Fatan Watsi Da Harkar Fim Nan Gaba —Umar Hassan
Published: 14th, September 2025 GMT
Masana’antar Kannywood Na Tsananin Buqatar Addu’a – Hauwa Garba Dole Mu Hada Kai Da ‘Yan Siyasa Don Ciyar Da Masana’antar Kannywood Gaba -Shugaban MOPPAN
Ko za ka faɗawa masu karatu ɗan taƙaitaccen tarihinka?
Ni haifaffen ɗan Zaria ne, wani gari da ake cewa, Samaru ana yi masa laƙabi da Samarun Zaria.
Ka yi maganar cewa ruwa ya kusa haɗiye ka, shin me ya janyo hakan, kuma ya abun ya kasance?
Lokacin da na je makarantar Allo muna zuwa mu yi ice mu zo mu siyar, domin mu samu kuɗin omo da na kashewa. Dajin da muke yo icen ya zamo akwai birrai a ciki, abu na biyu sai an tsallaka ruwa sannan muke zuwa dajin mi yo icen. Wata rana mun je mun dawo muka tarar da kwale-kwalen da yake ɗaukar mu, gabaɗaya ranar ba mu tarar da kwale-kwale koɗaya ba. Daga ƙarshe waɗanda suka iya ruwa suka yi iyo suka tsallaka ruwan, wasu kuma suka ɗan hau galan, wasu kuma suka hau kwarya. To, ni kuma ban iya ba, kawai sai na hau kan itacen nan irin ni ma ya tsallako da ni to, daga nan ne ruwan ya kife da ni Allah ya taƙaita ban mutu ba aka zo aka tsamo ni.
Da yawan mutane za su yi mamakin ganin yadda ka ke malami mahaddacin alƙur’ani, kuma ka tsunduma harkar fim, me za ka ce akan hakan?
Eh, gaskiya mutane suna wannan mamakin sosai. Wasu sukan ce asiri ne, wasu kuma sukan ce ai hau ne ma ya faɗa min, in ban da haka babu yadda za a ce mahaddacin alƙur’ani kuma marubucin alƙur’ani, ya zamana yana wannan harkar. A ‘yan fim ɗin ma akwai jarumai da yawa da sun sha faɗa min kaf! ‘yan fim babu kamata. Akwai masu ilimin addini sosai amma wanda za a ce ya haddace alƙur’ani har ya rubuta shi kaf ‘yan fim babu kamata. Wasu daga cikin mutane waɗanda ba su zauna da ni ba suna ganin kamar ma ni ba musulmin kirki bane, irin ana ɗan kyama ta, ana kyara ta sosai. Ina fuskantar baƙaƙen maganganu, dan ko kwanan nan wani ya kafa hoto na ya zaga da makamancin haka. Amma duk masu zagin idan mun zauna haka sai suka fuskance ni, kuma duk wanda ya zauna da ni a gaske ya san na fi baiwa karatu mahimmanci fiye da waɗannan harkokin, sai kuma a ga waccen kyamar ta ragu. Har yanzu dai akwai mutanen da ba su fahimce ni ba, kuma mutane da yawa sun tsane ni, sun guje ni a kan hakan. Dan har wata yarinya na taɓa so wanda a raina ina jin ina so na aure ta, amma sakamakon wannan rigar ta fim ɗin yarinyar ta nuna ba ta yi. Kamar yadda mahaifinta ya nunan cewa, da zarar ina wannan harkar fim ɗin ba za su ba ni ita ba.
Lokacin da ake faɗar munanan kalamai a kanka game da fim, shin baka ji a zuciyarka kana son barin harkar fim ba?
Nii yadda na tashi inada dakakkiyar zuciya, saboda ina da kyakkyawar manufa ina da yaƙinin ni dai fim bai sa ni na yi shaye-shaye ba, kuma bai sa ni nayi hulɗar mata ba, bai sa ni na sauka daga kan asalin tarbiyyata ba. Saboda haka tunda ni na san tsakanina ga Allah na iya aktin ne kawai, kuma rayuwata ce ta gaske nake yinta, ban taɓa cewa zan bari ba. Lokacin da na ce zan bar fim shi ne lokacin da yarinyar da zan aura ta nuna bata so, sai na yanke hukuncin zan bar fim. A ranar ‘yan jarida sun gayyace ni za su yi hira da ni a kan hakan, wani fim an gayyacen na ce na daina, me ya jaho hakan?. Sai mahaifiyata ta kira ni take cewa “me ya sa za ka bar fim”, na faɗa mata yadda muka yi. Take ce min bata yarda ba, na tambaye ta me ya sa? ta ce ai duk abin da zan daina ta fi son in bari lillahi billahi ne, ba ta son saboda mace ya zamana na daina. Mun yi wannan ma ba da daɗewa ba sai ga kiran Lawan Ahmad da Ali Nuhu da sauransu kan wani sabon aiki da za mu fitar.
Za ka yi kamar shekara nawa da fara fim?
Zan yi kamar shekara uku da fara fim, amma na fara waƙa kusan shekara takwas kenan, duk da cewa na fi yin aktin yanzu, amma am fi sanina a fim.
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?
Gaskiya babu wani abu da zan ce ya ja hankali na, kawai dai tun ina yaro irin yadda in za a aiki yaro an san ba zai dawo da wuri ba, sai ace “Idan ka dawo da wuri zan kunna maka kallo ko zan saka maka waƙa” to, da haka ake yi min wayo sai na yi sauri na dawo. Idan na dawo sai a yi min hakan kuma ina jin daɗi tun ina ƙarami ban ma san mene fim da waƙa ba, amma na taso da mafarkin hakan. Kuma daman duk me son fim da waƙa zan iya cewa, wannan cuta ce kamar ta me soyayya. Wanda yake soyayya in bai sami cikon muradinsa ba, to, ba zai samu nutsuwa a soyayya ba to, haka ma fim da waƙa.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
Na tashi ina ta budin-budimina, duk inda ake yahon dj, yahon kaɗe-kaɗe, garkuwa lokacin ana yahon Ajo da sauransu dai ina wajen. To, Allah dai bai sa da ni da wani mawaƙi ko ɗan fim ba, saboda ban tashi a garinsu ba. Wataran na je Katsina ina makaranta na fara biye-biyensu a ‘studio’, a nan na fara Ido. Bayan na yi ido a nan sai Allah ya sa na dawo Kaduna da zama, lokacin an ɗauke ni koyarwa a Kaduna. A nan ne na fara haɗuwa da ‘yan fim da mawaƙa, na fara alaƙa da su nake ganin yadda harkar take. Daga nan na ga ina da sha’awa. Bayan na fara tafiya ta yi tafiya har malamaina waɗanda suka kai ni makarantar dan na karantar suka ankara na fara ƙarfi a harkar aka ce an kore ni gabaɗaya makaranta. Nan dai na daina karantarwar na dawo a ƙarshe na koma makaranta na cigaba da karatuna. Inda na je ina haddato alƙur’ani na samu ɗan abin da na samu na ilimin alƙur’ani, sai na dawo. Sai kuma Allah ya kai ni Kano, daman Kano inada furodusas da daraktos da ake mutunci da su, sai na sauka a gidan ɗan fim kuma furodusa wato Muddasir Isyaku Dutsenma. Duk inda zai je harkar fim da ni yake tafiya, daman a Kaduna na fara da waƙa, daga baya ne na juye na koma fim.
Ya batun iyaye lokacin da za ka sanar musu kana son shiga harkar fim, shin ka fuskanci wani ƙalubale daga gare su ko kuwa?
Eh! Na fuskanci ƙalubale me yawa, saboda ni gidan da na tashi gidan almajirai ne. Ba a ma san mene waƙa ba, dan gidan mu ba TV har yau maganar da nake yi yanzu ba a san mene TV ba. Babbanmu ba ya riƙe babbar waya har yanzu, haka mahaifiyar mu to, ba su san mene kallo ba. Saboda haka ni na fuskance su na faɗa musu zan fara waƙa ko fim gaskiya wani abu ne me rauni gare ni, na dai fara ba su sani ba, da suka sani kuma a taƙaice an taɓa kora na daga gida saboda wannan harkar. An nuna min ɓacin rai sosai, sun nuna babu ruwansu da ni a gida, kuma a hakan na cigaba da yi. Saboda ni na san ina da kyakkyawan manufa, dan da na fara yi ɗin sai na gane akwai rawar da zan iya takawa ta iya fannin waƙa ko fannin fim. Amma inada zuciya mai kyau tunda na sami cikakken tarbiyya. Bayan lokacin korar da aka yi min a gida, iyaye suka kira suka ce, ‘To, tunda dai mun fahimci abun nan bai ɓata maka tarbiyya ba, baka lalace ba, ba ka daina karatu ba, in za ka yi fim ko waƙa ace ɗan mu ya tashi a mawaƙi gara ya zama jarumi irin yadda su Malam Inuwa suke yi ko Kabiru na Kango, tunda kana da ilimin addini ka zamo me bayar da gudun mawa ta wannan fannin. Sai na ga tunda iyaye su suka bayar da wannan shawarar sai na cigaba da tafiyar a haka. Za mu ci gaba a mako mai zuwa in sha Allah.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Kannywoo
এছাড়াও পড়ুন:
NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025
Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa (NECO), ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare (SSCE) na shekarar 2025.
Daga cikin ɗaliban da suka zana jarabawar guda 818,492, kashi 60.26 sun ci aƙalla darusa biyar da suka haɗa da Lissafi da Turanci.
Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu KanoShugaban NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ya ce ɗalibai 1,367,210 suka yi rajistar jarabawar; maza 685,514 da kuma mata 681,696.
Amma daga cikinsu, ɗalibai 1,358,339 ne suka zana jarabawar.
Ya ce ɗalibai 1,144,496, wanda ya kai adadin kashi 84.26, sun samu darusa biyar ba tare da cin Lissafi da Turanci ba.
Sai dai an dakatar da sakin sakamakon makarantu takwas a Ƙaramar Hukumar Lamorde ta Jihar Adamawa saboda rikicin ƙabilanci da ya auku tsakanin 7 zuwa 25 ga watan Yuli, 2025.
Rikicin ya yi sanadin wanda ya hana zana jarabawar darusa 13 da takardu 29.
Hukumar na tattaunawa da gwamnati don sake bai wa ɗaliban damar rubuta jarabawar.
NECO ta kuma bayyana cewa an samu makarantu 38 daga jihohi 13 ds laifin aikatar satar amsa yayin zana jarabawa.
Za a gayyace su zuwa babban ofishin NECO kafin ɗaukar mataki a kansu.
Haka kuma, hukumar ta dakatar da mutum tara da ke aikin sanya ido sake kula da jarabawa saboda gazawarsu wajen hana satar amsa.
Mutanen da aka dakatar, uku sun fito daga Jihar Ribas, uku daga Babban Birnin Tarayya, da kuma mutum ɗai-ɗai daga Jihohin Neja, Kano da Osun.