Bikin hada-hadar ba da hidima na Sin wato CIFTIS na bana da ya kare a jiya a nan Beijing ya jawo hankalin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 85 da suka gudanar da baje koli da tarurruka, kusan kamfanoni 500, ciki hadda wasu daga cikin manyan kamfanoni 500 dake sahun gaba a duniya da manyan kamfanoni masu jagorantar bangarorinsu, sun halarci bikin, kuma an cimma nasara a fannoni sama da 900.

A yayin da duniya ke fuskantar rashin tabbas, bikin CIFTIS ya karfafa mu’amala da kuma samun riba da juna.

Alkaluma na nuna cewa, a shekara ta 2024, jimillar cinikin ba da hidima na Sin ya fara wuce dala tiriliyan 1 a karon farko, wanda ya zama sabon tarihi, kuma ya kasance na biyu a duniya.

Masu zuba jari na waje suna kara zuba jari a Sin saboda babbar kasuwa. A halin yanzu, Sin ta zama abokiyar ciniki ta uku mafi girma a kasashe da yankuna 157, kuma ita ce kasa ta farko a fannin cinikin kayayyaki da ta biyu a fannin cinikin ba da hidima a duniya. A gun bikin na wannan shekara, Sin ta sanar da matakai da yawa, ciki har da “hanzarta aikin gwaji a yankunan gwajin ciniki cikin ’yanci da kuma yankunan ba da misali kan ayyukan ba da hidima na kasa” da “gaggauta bude kasuwar hada-hadar ba da hidima”. Wannan ya samu karbuwa sosai a wajen kamfanonin kasashen waje.

Ta hanyar tarurrukan baje kolin, duniya ba kawai ta ga sabbin abubuwa na tattalin arzikin Sin ba, har ma ta fahimci azamar Sin na hadin gwiwa da duniya da gina tattalin arzikin duniya mai bude kofa cikin hadin gwiwa. (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Tarihin Ƴan Majalisar Farko Kafin Da Kuma Zamanin Mulkin Mallaka (3)

Sarakunan suna bada haɗin kai wajen tafiyar da harkokin gwamnatin ƙasarsu, suna kuma jin basu tare da wata matsala ba tare da matsayinsu. Yawancin Sarakuna da kuma wasu manyan msu Sarautar gargajiya bugu da ƙari suna cikin majlisar dattawa a lokacin.

Duk kuma wani lokaci da Sarakunan gargajiya suka fahimci suna fuskantar barazana dangane da tsaronsu, ta haka ne za su fara wasu tafiye- tafiye basu nan basu can, wanda idan ba sa’a aka yi ba, kusan ƙarshen ƙasar ke nan a matsayinta na tarayyar Nijeriya a lokacin. Duk wani ƙoƙarin da Abubbakar Tafawa Balewa ya yi na kasancewa ya zama kamar yadda Kwame Nkrumah na Ghana, wanda a zamaninsa kome ya ce daidai ne sai an bi ko amfani da shi, irin hakan ba zai iya haifar da ɗa mai ido ba.

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Al’ajabi: Yadda Aka Shirya Bikin Haihuwar ‘Ya’yan Awaki Biyar A Garin Dakasoye
  • Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya
  • Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza
  • Sin Da Ghana Na Fadada Hadin Gwiwa A Bangaren Ciniki Da Zuba Jari
  • Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci
  • Espania Ta Soke Cinikin Makamai Na EUR Miliyon 700 Da HKI Saboda Kissan Kiyashi A Gaza
  • Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 
  • An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin
  • Tarihin Ƴan Majalisar Farko Kafin Da Kuma Zamanin Mulkin Mallaka (3)