Aminiya:
2025-09-17@20:30:19 GMT

Ambaliya: NEDC ta raba wa mutum 2,200 kayan agaji a Yobe

Published: 14th, September 2025 GMT

Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC), ta raba wa mutum 2,261 da ambaliyar ruwa ta shafa a Potiskum, Nangere da Jakusko a Jihar Yobe, kayan agaji.

An raba kayan ne a unguwanni 21 na Potiskum, ƙauyukan Kolo da Ajim a Nangere, da kuma kauyukan Dachia, Yim, Saminaka, Garin Maji da Amshi a Jakusko.

Gwamnati ta gargaɗi jihohi 11 kan yiwuwar afkuwar ambaliya a wannan makon Ban taɓa nadamar shiga Kannywood ba — Kabiru Nakwango

Kayan da aka bayar sun haɗa da shinkafa, taliya, man girki, da kuma tufafi, kayan mata da shadda.

Sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), Dokta Mohammed Goje, ya ce Gwamna Mai Mala Buni ya ba da umarnin gaggauta tallafa wa al’ummar da ambaliyar ta shafa.

Ya kuma roƙi jama’a da su yi amfani da kayan agajin yadda ya dace.

A nasa jawabin, babban daraktan NEDC, Mohammed Goni Alkali wanda Dokta Ali Ibrahim Abbas ya wakilta, ya gode wa gwamnatin Yobe bisa shirin.

Ya ce wannan tallafi wani ɓangare ne na manufar NEDC na taimaka wa al’ummar Arewa Maso Gabas wajen magance matsalolin yankin.

An sa ran wannan tallafin zai rage wa jama’a wahalhalun da ambaliyar ruwa ta jawo a jihar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: kayan agaji

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun sace mutum 40 a masallaci a Zamfara

Aƙalla masallata 40 ’yan bindiga suka sace a wani masallaci da ke Gidan Turbe a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara da safiyar wannan Litinin.

Majiyoyi sun ce an yi awon gaba da masallatan ne zuwa dazukan Gohori da ke yankin Tsafe.

Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas

Wannan harin dai kai tsaye masu ruwa da tsaki na kallonsa a matsayin kawo ƙarshen yarjejeniyar sulhu tsakanin ’yan bindigar da mahukuntan jihohin Zamfara da Katsina.

A baya-bayan nan ne jihohin Katsina da Zamfara suka ƙulla yarjejeniyar sulhu tsakaninsu da ’yan bindigar da suka addabi al’ummar jihohin arewa maso yammacin Najeriyar.

Yarjejeniyar sulhu da aka cimma a dajin Wurma ta samu halartan manyan ’yan bindiga irinsu Alhaji Usman Kachalla Ruga da Muhindinge da Yahaya Sani ( Hayyu ) da kuma Shu’aibu.

A ɓangaren mahukunta, akwai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi da kuma shugaban ƙaramar hukuma Babangida Abdullahi Kurfi.

’Yan bindiga sun saki wasu mutane da suke garkuwa da su a lokacin yarjejeniyar sulhun, tare da barin al’umma zuwa gonakinsu ba tare da wata fargaba ko tsangwama.

To sai dai kuma, ƙasa da wata guda bayan cimma wannan yarjejeniya, rahotanni sun ce ’yan bindiga sun kutsawa wani ƙauye a Zamfara tare da awon gaba da masallata.

Shaidun gani da ido sun ce, maharan sun yi wa masallacin ƙawanya da misalin ƙarfe 5:30 na safe, daidai lokacin da jama’a ke sallar asuba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
  • ’Yan sanda sun kama mutum 6 kan satar zinarin N109m a Kebbi
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 40 a masallaci a Zamfara
  • Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa