Najeriya ta daɗe tana fama da shugabanni marasa nagarta — Sanusi II
Published: 14th, September 2025 GMT
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce Najeriya ta daɗe tana fama da shugabanni waɗanda ba su da nagarta.
Ya bayyana haka ne a bikin “Kano International Poetry Festival” da aka yi a Kano a ranar Asabar.
Gini mai hawa 3 ya rufta kan mutane a Legas HOTUNA: Mahaifiyar Dangote ta halarci gasar karatun Alƙur’ani ta Shetty a KanoSarkin ya ce matsalolin ƙasar nan sun samo asali ne daga rashin shugabanci na gari.
“Ƙasar nan tana tashi da faɗuwa bisa ingancin shugabanni. Najeriya ta daɗe tana fama da shugabanni marasa nagarta.
“Kowace rana kuna gani a jaridu da labarai, ’yan majalisa suna ɓata lokaci kan abubuwan da ba su da amfani, yayin da sauran ƙasashe suke tattauna abubuwa kamar sauyin yanayi da fasahar zamani,”in ji shi.
Ya ƙara da cewar: “Amma mu har yanzu muna ta gardamar kan ƙabilanci da addini kamar yadda aka yi tun a shekarun 1960,” in ji shi.
Sanusi ya roki matasa da su tashi tsaye su ɗauki ragamar shugabanci daga hannun tsofaffin da suka daɗe suna riƙe da mulki.
Ya kuma kare cire tallafin man fetur, inda ya ce Najeriya da ta ci gaba da biyan tallafin da tuni ƙasar ta yi rauni.
Ya bayyana cewa tallafin man bai amfanar da Najeriya ba, face ƙara bunƙasa masana’antun ƙasashen waje maimakon a gyara na cikin gida.
“Da biliyoyin da aka kashe wajen biyan tallafi da su aka saka a gyaran matatun mai tun 2012, da yanzu Najeriya ta fi haka,” in ji shi.
Sanusi ya kuma yi gargaɗin cewa yawan karɓo bashi da kuma ɓatar da shi da gwamnati ke yi zai iya jefa tattalin arziƙin Najeriya cikin mawuyacin hali a nan gaba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Najeriya Sarkin Kano Najeriya ta
এছাড়াও পড়ুন:
An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
Majiyar ta kara da cewa, bayan yunkurinsu bai yi nasara ba a Tsanyawa, maharan sun sake wani sabon shiri, inda suka kai hari a kauyen Yar Tsamiya da ke gundumar Faruruwa, karamar hukumar Shanono, da misalin karfe 1:30 na dare, inda suka kashe mutane uku suka, tare da sace wasu uku.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA