Leadership News Hausa:
2025-11-02@20:54:36 GMT

Tarihin Ƴan Majalisar Farko Kafin Da Kuma Zamanin Mulkin Mallaka (3)

Published: 15th, September 2025 GMT

Tarihin Ƴan Majalisar Farko Kafin Da Kuma Zamanin Mulkin Mallaka (3)

Sarakunan suna bada haɗin kai wajen tafiyar da harkokin gwamnatin ƙasarsu, suna kuma jin basu tare da wata matsala ba tare da matsayinsu. Yawancin Sarakuna da kuma wasu manyan msu Sarautar gargajiya bugu da ƙari suna cikin majlisar dattawa a lokacin.

Duk kuma wani lokaci da Sarakunan gargajiya suka fahimci suna fuskantar barazana dangane da tsaronsu, ta haka ne za su fara wasu tafiye- tafiye basu nan basu can, wanda idan ba sa’a aka yi ba, kusan ƙarshen ƙasar ke nan a matsayinta na tarayyar Nijeriya a lokacin.

Duk wani ƙoƙarin da Abubbakar Tafawa Balewa ya yi na kasancewa ya zama kamar yadda Kwame Nkrumah na Ghana, wanda a zamaninsa kome ya ce daidai ne sai an bi ko amfani da shi, irin hakan ba zai iya haifar da ɗa mai ido ba.

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Siyasa Tarihi

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare

A ranar 30 ga wata ne shugabannin kasashen Sin da Amurka suka gana da juna a birnin Busan na kasar Koriya ta Kudu, lamarin da ya jawo hankulan kasa da kasa, inda shugabannin 2 suka yi musayar ra’ayoyi dangane da huldar da ke tsakanin kasashen 2 da al’amuran da suka jawo hankulansu. Sun amince da inganta hadin gwiwar kasashen 2 a fannonin tattalin arziki da cinikayya da makamashi da kyautata mu’amalar al’adu.

A yayin ganawar, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya jaddada cewa, yana son hada kai da shugaba Donald Trump na Amurka wajen aza harsashi mai kyau na raya huldar da ke tsakanin kasashen 2, tare da samar wa juna kyakkyawan yanayin samun ci gaba. A nasa bangaren, shugaba Trump ya ce, kasar Sin, abokiyar Amurka ce mafi girma. Kasashen 2 za su hada kansu wajen samun nasarar gudanar da manyan ayyuka da dama a duniya. Nan gaba Amurka da Sin za su kara samun nasara a hadin gwiwarsu. Shugabannin 2 sun amince su rika yin mu’amala da juna. Shugaba Trump yana sa ran kai ziyara a kasar Sin a farkon shekara mai zuwa, ya kuma gayyaci shugaba Xi ya ziyarci Amurka.

Masharhanta sun yi nuni da cewa, ganawar shugabannin 2 ta sanya tagomashi kan kyautatuwar huldar da ke tsakanin Sin da Amurka, ta kuma tsara manufar raya huldar kasashen 2 a nan gaba, tare da kwantar da hankulan kasashen duniya.

Abubuwan tarihi da kuma hakikanin abubuwa sun nuna cewa, wajibi ne Sin da Amurka su zama abokan juna. A wannan muhimmin lokaci, ganawar da shugabannin kasashen 2 suka yi ta sake tsara manufar kyautata da raya huldar da ke tsakanin kasashen 2. Muddin kasashen 2 suka aiwatar da muhimman daidaito da shugabannin 2 suka cimma, da mutunta ruhin adalci, tare da martaba juna da samun moriyar juna, to, za a raya huldar da ke tsakanin kasashen 2 ba tare da wata matsala ba, da kuma kara samar da kwanciyar hankali da tabbaci a duniya. (Tasallah Yuan)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi October 31, 2025 Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo October 30, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma  October 30, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan
  • Dan Majalisar Jema’a/Sanga, Daniel Amos, Ya Koma Jam’iyyar APC
  • Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa a kan Naira miliyan 1.5m
  • Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi
  • Barcelona ta shiga zarwacin Victor Osimhen
  • Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
  • Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma
  • Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC
  • Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare