Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar Sin ya gudanar da taron manema labarai da misalin karfe 10 na safiyar yau Litinin, inda kakakin hukumar kididdiga ta kasar, kuma babban masanin tattalin arziki, kana daraktan sashen kididdigar tattalin arziki na kasar, Fu Linghui ya yi karin haske kan ayyukan tattalin arzikin kasar cikin watan Agustan bana, tare da amsa tambayoyin manema labarai.

A cewar bayanan da aka gabatar a yayin taron, ayyukan tattalin arzikin kasar a watan Agusta sun samu ci gaba ba tare da tangarda ba. Kuma hakan ya bayyana ne ta hanyoyi daban-daban kamar haka: masana’antu sun habaka cikin sauri, masana’antar kera kayayyakin aiki da masana’antar fasaha sun samu ci gaba mai kyau. Kana ayyukan bayar da hidima su ma sun bunkasa cikin sauri. Baya ga haka, an samu ci gaba mai kyau a bangaren bayar da hidimomi na zamani. Harkokin kasuwanci sun samu ci gaba cikin natsuwa, inda harkokin sayar da kayayyaki ga masu sayayya suka kara habaka. Har ila yau, kadarorin jari sun ci gaba da karuwa, jarin masana’antu ya habaka cikin sauri, harkokin fice da shigen kayayyaki sun ci gaba da girma, tsarin kasuwanci ya ci gaba da ingantuwa, kana yanayin samar da guraben aikin yi, ya kasance kan wani mataki mai daidaito. Sai dai kuma saboda yanayin da ake ciki, adadin marasa aikin yi a birane ya karu, ma’aunin Core CPI ya ci gaba da hauhawa, kana faduwar farashin kayayyakin masana’antu ya ragu.

Bayanan sun kara da cewa, akwai bukatar lura da cewa, ana fuskantar yanayin rashin tabbas a waje, kuma tattalin arzikin kasar Sin yana fuskantar kalubale da hadari da yawa. (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Chadi:  Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa  damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa

Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da gyare-gyaren kundin tsarin mulkin kasar da zai tsawaita wa’adin shugabancin kasar daga shekaru biyar zuwa bakwai da kuma baiwa shugaban kasar damar ci gaba da mulki na tsawon wa’adi maras iyaka.

Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar a ranar Litinin da kuri’u 171, yayin da aka kada kuri’a daya tilo da taki amincewa da hakan.

A ranar 13 ga watan Oktoba ne aka shirya kada kuri’ar karshe a majalisar dattawa, a cewar sanarwar da shugaban majalisar Ali Koloto Chaimi ya fitar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito. Sannan  kuma shugaban kasar zai sanya hannu kan kundin tsarin mulkin sannan ya zama doka.

Shugaban kasar Chadi, Mahamat Idriss Deby ya karbi mulkin kasar ne bayan kisan mahaifinsa tsohon shugaba Idriss Deby, a lokacin da ya ziyarci sojojin da ke yaki da mayakan ‘yan tawaye a arewacin kasar a shekarar 2021.

Deby ya yi ikirarin samun nasara bayan zaben da aka gudanar bayan shekaru uku na mulkin soja a watan Mayun 2024, sannan kuma aka gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki a watan Disamba, wanda ya bai wa jam’iyya mai mulki rinjayen kujeru.

An samu cece-kuce game da sakamakon zaben, bayan da madugun ‘yan adawa kuma firaministan kasar Succe Massara ya yi ikirarin samun nasara, ikirarin da hukumar zaben kasar ta yi watsi da shi.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila September 17, 2025 Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza September 17, 2025 Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan Musulmi game da halin da ake a yankin September 17, 2025 Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza September 17, 2025 Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza September 17, 2025 Akalla Falsdinawa 78 Ne Suka Yi Shahada A Yau A Gaza. September 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari A Tashar Jirgin Ruwan Hudaida Dake Yamen September 16, 2025 Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki 5 A Wajen Taron kere-kere . September 16, 2025 Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta. September 16, 2025 Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana September 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • Chadi:  Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa  damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa
  • Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani
  • ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
  • Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
  • Hadin Gwiwar Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Makamashi Tsakanin Sin Da Rasha Ba Abun Zargi Ba Ne
  • Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS
  • Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 
  • Sarki Sanusi II ya koka kan yawan cin bashin Najeriya