Aminiya:
2025-11-02@17:01:42 GMT

Gobara ta kashe manyan jami’an hukumar FIRS 4 a Legas

Published: 18th, September 2025 GMT

Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa (FIRS) ta ce ma’aikatanta hudu sun mutu a gobarar da ta tashi a ginin Afriland Towers da ke titin Broad da ke Legas, a ranar Talata.

Aminiya ta rawaito yadda gobara ta mamaye ginin da ke dauke da banki, hukumomi da wasu kamfanoni.

Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas?

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, mai magana da yawun Shugaban FIRS, Zaach Adedeji, wato Dare Adekanmbi, ya ce hukumar na cikin jimami da alhini kan rasuwar ma’aikatan nata.

Sanarwar ta ce, “Cike da alhini da bakin ciki, FIRS na sanar da rasuwar ma’aikatanta hudu a gobarar da ta tashi a ginin Afriland Towers da ke titin Broad, Legas, a ranar Talata. FIRS na daya daga cikin masu haya a ginin, inda Ofishin Binciken Matsakaicin Haraji da Ofishin Haraji na Onikan ke a bene na shida da na bakwai.”

“Jami’an tsaro da na kula da lafiya na hukumar sun gaggauta tuntubar hukumar kashe gobara lokacin da aka sanar da su. Amma da suka isa wurin, hayaki mai kauri da duhu ya turnuke ginin.”

“Hukumar da dukkan ma’aikatanta na cikin alhini kan wannan lamari. Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda suka rasu, kuma muna tare da su a wannan lokaci mai wahala. Za mu ba su dukkan goyon baya da tallafi da ake bukata.”

“Muna aiki tare da dukkan hukumomin da suka dace a Legas domin gano musabbabin wannan mummunan al’amari. A yayin da ake ci gaba da bincike, za mu duba matakan kiyaye lafiyar dukkan ofisoshin FIRS da ke fadin ƙasa, ko na haya ne ko wanda ta mallaka.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gobara

এছাড়াও পড়ুন:

Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa

Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isa, ta ƙaryata labarin da wata jaridar intanet ta yaɗa cewa wai tana son ta auri shahararren dan TikTok, Ashiru Mai Wushirya, wanda ya yi tashe a kafafen sada zumunta a ’yan kwanakin nan.

A wani saƙo da ta wallafa, Mansurah ta ce labarin ƙarya ne kuma ya jefa ta da iyalinta cikin ruɗani da damuwa.

Ta ce, “Na shiga firgici bayan na ga wannan labarin. Ba ni da wata alaka da Mai Wushirya. Wannan sharri ne tsagwaron karya.”

Rahoton da aka yada a jaridar AMC Hausa ya yi iƙirarin cewa wai Mansurah ta ce ta shirya auren Mai Wushirya idan har yana son ta da gaske.

Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa a kan Naira miliyan 1.5m An yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi

Amma jarumar ta yi watsi da wannan iƙirarin, tana mai cewa jaridar ta ɓata mata suna kuma ta karya ƙa’idojin aikin jarida.

Ta ce, “Na kira su, na ba su awa 24 su sauke labarin, amma har yanzu ba su yi hakan ba. Sun kira ni sun ba ni hakuri a waya, amma labarin har yanzu yana nan. Wannan abu ya zubar min da mutunci kuma ya saka iyalina cikin tashin hankali,” ina ji ta.

Mansurah ta bayyana cewa yanzu tana cikin shirin ‘WalkAwayCancer’, wani gagarumin shiri na wayar da kan jama’a kan mcutar daji, amma wannan labarin karya ya yi ƙoƙarin karkatar da hankalin mutane daga ainihin aikinta.

“Kun hana ni barci da kwanciyar hankali saboda labarin da babu gaskiya a cikinsa. Amma in sha Allahu, za ku ji daga gare mu,” in ji ta cikin fushi.

Har zuwa lokacin da muka kammala wannan labarin dai, kamfanin AMC Hausa bai fitar da wata sanarwa ba dangane da ƙarar da Mansurah ke shirin kai musu bisa zargin yaɗa labarin ƙarya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?
  • Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa
  • An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
  • Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori
  • Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami
  • Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa
  • Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFA
  • Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki
  • An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m
  • Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda