HausaTv:
2025-11-02@17:03:40 GMT

Eslami: Dole ne IAEA ta zama mai cikakken ‘yancin cin gashin kai

Published: 18th, September 2025 GMT

Shugaban Hukumar Nukiliya ta Iran ya ce barazanar da makiya Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke ci gaba da yi tun bayan harin ba-zata da Isra’ila da Amurka suka kai kan cibiyoyin nukiliyar kasar, na kara nuni da cewa dole ne hukumar IAEA ta zama mai cikakken ‘yancin cin gashin kai, ba wurin aiwatar da siyasar adawa da kasar Iran ba.

Mohammad Eslami, wanda shi ne shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran (AEOI), ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na Kyodo na Japan a wata rubutacciyar hira da aka buga a ranar Laraba.

Ya kara da cewa halin da ake ciki na tsaro na cikin hadari, domin kuwa yanayi da ya yi kama da lokacin yaki saboda irin barazana da gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da yi a kan Iran.” in ji shi.

A cikin watan Yuni ne gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila  ta kallafa wa Iran yaki, inda ta kai munanan hare-hare kan cibiyoyin nukiliyarta, da kayayyakin kariya, da jami’an soji, da masana kimiyyar nukiliya, da kuma fararen hula.

Kimanin mutane 935 da suka hada da kananan yara ne suka yi shahada a yakin da aka kwashe kwanaki 12 ana yi.

Amurka ta shiga tsaka mai wuya, bayan da ta kai hari kan wasu muhimman cibiyoyin nukiliyar Iran.

A cewar Eslami, “Wannan shi ne karo na farko a tarihi da aka kai wa tashoshin nukiliyar kasar hare-haren soji.”

Ya sake jaddada cewa, wannan zaluncin ya sanya Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta iya ci gaba da yin hadin gwiwa da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) kamar yadda ya gabata ba.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Rahoto: An yi tattaunawa mai tsawo tsakanin Syria da Isra’ila a Landan September 18, 2025 Sheikh Qassem: Harin Pager jarabawa ce wadda ta kara wa masu gwagwarmaya kwarin gwiwa September 18, 2025 Pezeshkian: Iran da Masar suna da tsohon tarihi a duniya September 18, 2025 Iran ta samu Zinariya, Azurfa, da Tagulla a Gasar Kokawa ta Duniya September 18, 2025 Iran Ta Yi Nasarar Gwajin Tauraron Dan’adam Da Zai Samar Da “Internet” Ga Yankunan Karkara September 17, 2025 Za A Kada Kuri’ar Raba Gardama Akan Sabon Tsarin Mulki A Kasar Guinea September 17, 2025 Larijani: Iran Da Saudiyya Za Su Bunkasa Aiki Tare A Fagagen Kasuwanci Da Tsaro September 17, 2025 Hukumar Tarayyar Turai Ta Gabatar Da Shawarar Jingine Aiki Da Yarjejeniyar Kasuwanci Da HKI September 17, 2025  Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Falasdinawa  Kisan Kiyashi A Gaza September 17, 2025 Ma’aikatar Shari’ar Iran Ta Sanar Da Rataye Dan Leken Asirin Hukumar Mossad Ta Isra’ila September 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya yi gargadi a matsayin martani ga sanarwar Washington na ci gaba da gwajin makaman nukiliya, yana mai kiran hakan a matsayin wani mataki na koma-baya da Rashin yin da’a ga dokokin kasa da kasa.

Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya soki Washington saboda sauya wa Ma’aikatar Tsaron kasar  suna zuwa Ma’aikatar Yaki, kuma ya yi Allah Wadai da Shirin Amurka na yin gwajin makaman nukiliya, tare da bayyana hakan a matsayin yunkurin tayar da zaune tsaye da jefa duniya a cikin bala’i.

Wanda yake aikata irin wannan halayya ne ke ci gaba da yin barazanar sake kai hari kan cibiyoyin nukiliya na Iran bisa hujjar hana Iran mallakar makaman nukiliya da sunan kare kansu daga Iran domin kada ta mallaki makaman kare dangi.” in ji ministan harkokin wajen Iran.

Ya yi Allah wadai da Amurka saboda sukar da ta dade tana yi wa shirin nukiliya na zaman lafiya na Iran yayin da ita kuma take ci gaba da gwajin makamanta na nukiliya, wanda hakan ya saba wa dokokin duniya.

Shugaban Amurka Donald Trump a ranar Laraba ya bayyana cewa makaman nukiliya na Washington su ne mafi girma a duniya, kuma ya danganta wannan matsayin da gyare-gyare da aka yi a lokacin gwamnatinsa.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya
  • Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran
  • Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya
  • Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar
  • Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan
  • Iran Ta Sanya  Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3
  • Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda
  • Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya
  • Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa
  • Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta