Iran Ta Kaddamarda Sabbin Magunguna Har 23 Tare Riga Kafin HPV A Karon Farko A Kasar
Published: 31st, May 2025 GMT
Kamfanin Barakat, mai samar da magunguna a nan JMI ya kaddamarda sabbin magunguna har 23 wanda kamfanin ya samar a cikin gida daga ciki har da riga kafi mai suna HPV.
Kamfanin dilancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan ci gaban da kamfanin Barakat ya samu mataki ne mai girma a fagen samar da magungunan da kasar Iran take bukata a cikin gida.
Ministan kiwon lafiya na JMI Mohammad Reza Zafarqandi, a jawabinda da ya gabatar a bikin gabatar da magungunan ya ce, gamayyar kamfanonin samar da magunguna na kasar Iran wato ‘Barakat Group’ ya samar da magani wanda ake kira Gardisan, wanda yake yake magance cutar HPV ko daji, farashinsa a cikin gida rabin wanda ake shigo da shi daga waje ne.
Shugaban kamfanonin ya bayyana cewa wadannan magunguna zasu shiga kasuwa ne bayan an kammala dukkan tsare-tsare da yakamata a bi don yin hakan. Ya kuma mkara da cewa samar da wadan nan magunguna ya tserawa kasar asarar dalar Amurka $43 don shigoda su daga kasashen waje a ko wace shekara.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: samar da magunguna
এছাড়াও পড়ুন:
Babban Hafsan Sojin Iran Ya Ce: Iran Zata Sanya Duk Wanda Ya Dauki Matakin Wuce Gona Kanta Nadama
Babban Hafsan Hafsoshin Sojan Iran ya jaddada cewa: Idan makiya suka sake yin kuskure, za su fuskanci mayar da martani da karfi
Babban hafsan hafsoshin sojan kasar Iran Manjo Janar Abdulrahim Mousavi ya jaddada cewa: Idan makiya suka sake yin wani kuskure, to za su fuskanci mayar da martani mai karfi da zai wurga su cikin nadama kuma martini mai gauni ne fiye da na baya.
A yayin ganawarsa da gungun mayakan sojojin sama, Manjo Janar Mousavi ya mika sakon jinjina ga shahidan daukaka da karfin Jamhuriyar Musulunci musamman shahidi Major Janar Hajizadeh. Ya yaba da rawar da ya taka wajen ciyar da shirye-shiryen rundunar Sojan sararin samaniya da bunkasa karfin makamai masu linzami da jirage marasa matuki ciki na kasar, ya kuma yi la’akari da kokarinsa a matsayin mai karfi da zaburarwa ga al’ummomi masu zuwa kuma masu dauke da ruhin kare kasarsu.
Mousavi ya bayyana rundunar Dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta IRGC a matsayin rundunar da ke haifar da alfahari da mutuntawa, yana mai cewa, “Bayyana wannan karfin da sojojin sararin samaniya suka gwada a lokacin yakin kwanaki 12 da aka kakaba wa Iran ya zarce duk abin da aka tsammata, kuma girman kokari da suka nuna ya fi muhimmanci fiye da manyan ayyukan da aka yi a lokacin tsaro mai alfarma.”