Zulum: Boko Haram na sake kwace iko da wasu yankuna a Borno
Published: 9th, April 2025 GMT
Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwa kan hare-haren da kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram suke kai wa manyan sojoji a baya-bayan nan.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake jagorantar taron kwamitin tsaro da aka gudanar a zauren majalisar, gidan gwamnati, Maiduguri, yana mai cewa jihar na fuskantar barazanar komawa cikin tashin hankali.
“An gurgunta matsugunan soji da dama musamman a garuruwan Wulgo, Sabongari, Wajirko da sauransu. Alamu na nuna ‘yan ta’adda sun fara nasara akanmu. Don haka wannan abu ne mai matuƙar muhimmanci da muke buƙatar tattaunawa.
“Daga shekaru uku baya zuwa yanzu a hankali zaman lafiya ya fara dawowa Borno, amma lamarin ya sauya a ‘yan kwanakin nan,” in ji shi
Zulum ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tura jiragen yaƙi masu saukar ungulu, da sabbin jirage marasa matuka da aka saya domin tallafawa ayyukan soja a wuraren da abin ya shafa.
“Duk da muna yaba wa sojojin Najeriya, ‘yan sanda, da jami’an DSS kan kiyaye doka da oda a Borno, dole ne mu kuma faɗi gaskiya, in ba haka ba, duk nasarorin da aka samu ya zuwa yanzu za su tafi a wofi,” a cewarsa
Gwamnan, wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jajirce waje. Tabbatar da yankin arewa maso gabashin kasar ya samu kulawar da ta kamata.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar
Gwamna Inuwa ya kuma jaddada bukatar bin ka’idojin kariya a harkokin sufurin ruwa, inda ya yi kira ga shugabannin kananan hukumomi, da shugabannin al’umma, da direbobin kwale-kwale da hukumomin da ke da ruwa da tsaki da sauran wadanda suka dace su kara kaimi wajen ganin ana kiyaye duk ka’idojin kariya don magance sake afkuwar ibtila’in a nan gaba.
Ya umurci Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA) da Majalisar. Karamar Hukumar Nafada su bayar da duk wani tallafin da ya dace ga iyalan da abin ya shafa tare da hada hannu da hukumomin da abin ya shafa don inganta tsaro da wayar da kan al’ummomin da ke yankunan kogi.
Gwamna Inuwa Yahaya ya yi addu’a yana mai cewa “A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Gombe, ina mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalan mamatan tare da addu’ar Allah ya jikansu da rahama ya gafarta musu kurakuransu, ya kuma saka musu da Aljannar Firdaus”.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA