Babu Kuɗin Fansar Da Aka Biya Wajen Ceto Janar Tsiga – DHQ
Published: 9th, April 2025 GMT
Rundunar Sojin Nijeriya ta ce ba a biya kuɗin fansa ba kafin a ceto tsohon shugaban NYSC, Janar Mahrazu Tsiga (mai ritaya), daga hannun ‘yan bindiga.
A wata sanarwa da Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, ya bayyana cewa an yi amfani da bayanan sirri da kuma dabarun soji wajen ceto Janar Tsiga.
Dole Dukkanin Masu Umrah Su Fice Daga Saudiyya Kafin 29 Ga Afrilu – Hukumomi An Buɗe Sabbin Cibiyoyin Kula Da Masu Cutar Sankarau A Jihohi 6An yi garkuwa da shi ne a mahaifarsa Tsiga da ke ƙaramar hukumar Bakori a Jihar Katsina, ranar 5 ga watan Fabrairu, tare da wasu mutane 13.
Sojoji sun gudanar da samame a yankunan Ɗanmusa, Faskari da Kankara, inda ake tunanin ‘yan bindigar ke ɓuya, har suka samu nasarar ceto shi ba tare da biyan fansa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Janar Tsiya
এছাড়াও পড়ুন:
Fiye Da Kamfanoni 30,000 Masu Zuba Jari Daga Waje Aka Kafa A Sin A Rabin Farkon Bana
Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bayyana cewa, a cikin watanni shidan farko na bana, an kafa sabbin kamfanoni 30,014 na masu zuba jari daga kasashen waje a babban yankin kasar Sin, wanda ya nuna karuwar hakan da kashi 11.7 cikin dari a mizanin duk shekara.
Kazalika, bayanai sun nuna cewa, saka hannun jari daga kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya ya karu da kaso 8.8 cikin dari a tsakanin lokacin.
Har ila yau, jarin da aka zuba daga kasar Switzerland ya karu da kaso 68.6, na Japan ya karu da kashi 59.1, na Birtaniya ya karu da kaso 37.6, sai kuma na Jamus da ya karu da kashi 6.3, kana wanda aka zuba daga Jamhuriyar Koriya kuma ya karu da kashi 2.7 bisa dari. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp