Gwamnan Neja Ya Musanta Rikici Da Mataimakinsa.
Published: 2nd, May 2025 GMT
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago ya bayyana dangantakarsa da mataimakinsa, Kwamared Yakubu Garba a matsayin cikakkiya da jituwa.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai kan dangantakarsa da mataimakinsa bayan bikin ranar ma’aikata a Minna.
A cewarsa, “mu kungiya ce, ba za su iya karya mu ba, hankalinmu yana kan manufa, kuma za mu cimma ta.
Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da marawa gwamnatinsa baya, tare da tabbatar da cewa wata sabuwar Nijar za ta yiwu.
Binciken da aka gudanar ya nuna cewa mataimakin gwamnan jihar Neja, Kwamared Yakubu Garba bai halarci bikin ranar ma’aikata ta bana a Minna ba wanda wasu al’ummar Nejar din suka yi zargin cewa rashin jituwar da ke tsakanin gwamnan jihar Neja da mataimakinsa tayi tsamari.
KARSHEN ALIYU LAWAL.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gwamna
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Zamfara Ya Naɗa Abdulkadir Ibrahim A Matsayin Sabon Sarkin Katsinan Gusau Na 16
Gwamna Lawal ya taya sabon sarki murna, tare da roƙon Allah Ya bashi hikima da ikon yin jagoranci na gari.
Ya kuma buƙace shi da ya ci gaba da bin kyawawan ɗabi’u da tafarkin tsofaffin sarakuna domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a masarautar Gusau.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp