HausaTv:
2025-04-30@23:26:15 GMT

Iran ta ce an dage tattaunawar matakin kwararru da Amurka zuwa ranar Asabar

Published: 23rd, April 2025 GMT

Iran ta sanar da dage tattaunawar da aka shirya gudanarwa yau Laraba tsakanin tawagar kwararu ta kasar da kuma na Amurka a kasar Oman a wani bangare na ci gaba da tattaunawar da ake tsakanin kasashen biyu kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya bayyana cewa, an dage tattaunawar ta matakin kwararru tsakanin Iran da Amurka kan cikakkun bayanai na fasaha na yiwuwar maye gurbin yarjejeniyar nukiliyar shekarar 2015, wadda aka shirya yi a yau ranar Laraba, zuwa ranar mai zuwa 26 ga watan Afrilu.

Esmaeil Baghaei ya bayyana cewa, za a gudanar da taron a daidai lokacin zagaye na gaba na tattaunawar tsakanin jagororin tawagogin guda biyu.

Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi da Steve Witkoff, manzon musamman na shugaban Amurka kan harkokin yankin gabas ta tsakiya, sun jagoranci tattaunawar wacce ba ta kai tsaye ba har sau  biyu kan shirin nukiliyar Iran da kuma dage takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran a babban birnin Oman na Muscat da babban birnin Italiya, Roma, a ranakun 12 da 19 ga watan Afrilun nan, a shiga tsakanin Ministan harkokin wajen Omani Badr bin Hamad Al Busaidi ne ya shiga tsakani tattaunawar.

A ranar 26 ga watan Afrilu ne ake sa ran gudanar da zagaye na uku na shawarwarin kai tsaye tsakanin Araghchi da Witkoff a kasar Oman domin tantance sakamakon tarukan da masana suka yi da kuma auna yadda suke kusa da cimma matsaya.

A wani labara kuma, ministan harkokin wajen Iran, Araghchi ya tattauna da shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, ta IAEA, jiya Talata

Inda ya yi masa bayani kan sabbin abubuwan da suka faru game da tattaunawar da Amurka, yana mai jaddada kudurin Iran na yin shawarwarin bil hakki.

Shi ma Grossi, ya yaba da matakin da Iran ta dauka, ya kuma bayyana shirin hukumar na bayar da duk wani taimako a cikin wannan tsari, daidai da ayyukanta da ikonta kamar yadda dokar hukumar ta IAEA ta ayyana.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: harkokin wajen

এছাড়াও পড়ুন:

Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa Gabon

Kungiyar Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa kasar Gabon tare da maida ta a cikin cibiyoyinta.

AU, ta sanar da hakan ne yayin taron kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar yau Laraba a Addis Ababa.

Hakan dai ya karshen dakatarwar da aka yi wa kasar ta Gaban daga kungiyar, watanni 20 bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Agustan 2023.

Kwamitin zaman lafiya da tsaro na AU, ya yi la’akari da mika mulki da ya hambarar da Ali Bongo “gaba daya cikin nasara,” saboda haka ya yanke shawarar dage takunkumin nan take.

‘’Tsarin siyasar Gabon yana da ” gamsarwa” inji sanarwar kungiyar.

Wannan matakin na AU ya zo ne kwanaki uku gabanin rantsar da Janar Brice Oligui Nguema, wanda aka zaba a matsayin shugaban kasar a ranar 12 ga Afrilu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu gobe Alhamis
  • Araghchi : Za’ayi Tattaunawar Iran da Amurka ta gaba a Rome bayan taron E3
  • Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa Gabon
  • Amurka ta sake laftawa wasu kamfaninin mai na Iran takunkumi
  • Iran Da Iraki Sun Ce An Kammala Shimfida Layin Dogo Daga Shalamcheh Zuwa Basra
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jadadda Cewa: Duk Wani Harin Wuce Gona Da Iri Kan Iran Zai Fuskanci Mayar Da Martani
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Ci Gaba Da Killace Gaza Da Kashe Mutane, Laifi Ne Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba
  • Aikin Hajji: Za A Fara Jigilar Alhazan Jihar Kwara A Ranar 12 Ga Watan Mayu
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA
  • Takht Ravanji: Iran Ba Za Ta Taba Yin Tattaunawa Akan Dakatar Da Tace Sanadarin Uranium Ba