2025-08-01@09:55:00 GMT
إجمالي نتائج البحث: 24

«raya kasa na»:

    Kwanan baya, kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya shirya taron bita tare da wadanda ba ’yan jam’iyyar ba, dangane da yanayin tattalin arzikin kasar, da kuma ayyukan tattalin arziki da za a aiwatar a rabin shekarar bana ta biyu, domin sauraren ra’ayoyinsu. Xi Jinping, babban sakataren jam’iyyar ne ya shugabanci taron tare da ba da muhimmin jawabi, inda ya ce, dole ne a zage damtse wajen gudanar da ayyukan tattalin arziki a rabin shekarar bana ta biyu, kuma a tabbatar da gudanar da ayyukan ba tare da tangarda ba, kana a aiwatar da cikakken sabon tunanin raya kasa daga dukkan fannoni, da gaggauta kafa tsarin raya kasa, da kiyaye aiwatar da manufofi ba tare da matsala ba, da...
    Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Zhao Leji, da shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Wang Huning, sun gana da shugaban majalisar dattijan kasar Madagascar Richard Ravalomanana. Yayin ganawar, Zhao Leji ya bayyana cewa, Sin tana fatan yin kokari tare da Madagascar, don sa kaimi ga raya hadin gwiwa, da sada zumunta a tsakaninsu, da samar da gudummawa ga raya kyakkyawar makomar Sin da Afirka a sabon zamani. Kana yana fatan hukumomin kafa dokoki na kasashen biyu, za su kara yin mu’amala, da hadin gwiwa da juna, don taimakawa wajen raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da Madagascar a dukkan fannoni. Yayin ganawar tsakanin Wang Huning da Ravalomanana, Wang ya...
    Yau Talata, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai na jerin taruka masu jigon “Kammala shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14 mai inganci”. Yayin taron, jami’in kungiyar nakasassu ta Sin ya bayyana cewa, yayin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14, an kiyaye hakki da moriyar nakasassu na kasar yadda ya kamata. A halin yanzu, kasar tana da dokoki da ka’idoji sama da 180 da suka shafi kare nakasassu, ciki har da “Dokar gina muhalli marar shinge”, kuma akwai dokoki da ka’idoji 41 na kasa da suka kara tanade-tanade don kare hakkoki da muradun nakasassu a lokacin tsarawa da gyara abubuwan da suka shafi muhalli. Bugu da kari,...
    A nasa bangaren, Abiy ya ce Habasha da Sin amintattun kawaye ne na manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, kuma kasarsa tana mika tsantsar godiya ga kasar Sin saboda goyon bayan da ta dade tana bai wa Habasha a fannin raya tattalin arziki da zamantakewa. Yayin da yake nuni da irin muhimmiyar rawar da kasar Sin take takawa a harkokin kasa da kasa, musamman a fannin raya ci gaban duniya, Abiy ya ce Habasha a shirye take ta rubanya mu’amala a matakin koli da kasar Sin da kuma zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa. (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    Zaunannen wakilin Sin dake ofishin MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa a birnin Geneva Che Xu, ya yi jawabi a gun taron tattaunawa na shekara-shekara, kan gudummawar fasahohi karo na 59, na majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD a jiya Juma’a, a madadin walikan kasashe fiye da 70, game da raya hidimomi ga nakasassu ta hanyar fasahar AI, inda ya yi kira ga raya fasahar AI don inganta fasahohi, da karfin hidimomin da ake samarwa nakasassu, da kuma sa kaimi ga sassan kasa da kasa, ta yadda za su iya more fasahohin bunkasa fasahar AI. A cikin jawabin nasa, ya gabatar da shawarwari uku. Na farko ya ce kamata ya yi a mai da hankali ga bukatun dan...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yau cewa, a shekarun baya-baya nan, an gwada sabbin kayayyayin fasahohin zamani kamar mutum-mutumin inji mai siffar dan Adam, da gilas na zamani, da na’urorin ba da jinya dake hade da kwakwalwa da inji da sauransu, a dandalin bikin baje koli na kayayyakin shige da fice na Guangzhou wato Canton Fair, da bikin baje koli na kayayyakin sayayya na kasa da kasa, da bikin baje koli na kayayyakin da ake samarwa na kasa da kasa wato CISCE da sauransu. Wadannan bukukuwan baje koli sun shaida sabon karfin Sin na samar da hajoji da hidimomi masu karko, kana sun kasance muhimmin gadar dake hade sassan kasa da kasa kan mu’amalar...
    “Za a sauƙaƙe hakan ne ta hanyar Bankin Raya kasa na KfW da Asusun Kalubalan Kasuwancin Afirka.”   An gudanar da bikin sanya hannun ne a ofishin ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Abubakar Bagudu, wanda ya wakilci Nijeriya.   Sakatare na farko kuma shugaban hadin gwiwar raya kasa a ofishin jakadancin Jamus a Nijeriya, Dr Karin Jansen, da wakilin bankin raya kasa na KfW, Gerald Keuhnemund, duk sun halarci rattaba hannun. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yayin taron shekara-shekara na tattaunawar CBD na shekarar 2025 da aka rufe a yau Juma’a 13 ga wata, mashawarci kana kwararre a hukumar kasuwancin kasar Sin ta kasar Birtaniya, kuma shugaban cibiyar bunkasa kasuwanci tsakanin Birtaniya da Sin mista John Mclean, ya bayyana yayin da yake hira da wakilin CMG cewa, kasuwar kasar Sin tana cike da damammaki, don haka dole ne ya shiga a dama da shi a cikinta. A ganinsa, yayin da ake tinkarar tashe-tashen hankula da rashin tabbaci a duniya, babbar baiwar da Sin take da ita, da muhalli mai aminci da bude kofa ga kowa, sun samarwa kamfanonin Birtaniya da ma duniya baki daya damammaki. Tun bayan kafuwarsa a shekarar 2000 zuwa yanzu, taron ya kasance...
    A yau Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Myanmar Min Aung Hlaing, sun mikawa juna sakon murnar cika shekaru 75, da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu. Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, cikin shekaru 75 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Myanmar, bangarorin biyu sun bi ka’idoji 5 na zama tare cikin lumana, da kuma tunanin Bandung, da sada zumunta, da zurfafa hadin gwiwar samun moriyar juna, da nuna goyon baya ga juna kan manyan batutuwan dake shafar moriyarsu, sun kuma kasance abun koyi a fannin sada zumunta tsakanin kasa da kasa. Ya ce, kasar Sin tana fatan ci gaba da kokari tare da Myanmar, don gaggauta raya hadin gwiwa mai...
    A kwanan baya, tsohuwar firaministar kasar New Zealand, Madam Jennifer Shipley, ta yi hira da wakilin CMG, inda ta ce, ya dace a koyi ingantattun dabarun kasar Sin a fannin raya kasa. Ta ce yadda kasar Sin ta gabatar da shawarar tabbatar da ci gaban duniya, da bai wa sauran kasashe dabaru da fasahohin da ta samu na da ma’ana matuka. Saboda kasar tana kan gaba a duniya, a fannin raya al’umma, da ci gaban tattalin arziki mai dorewa. A cewar Madam Shipley, ya kamata a dora muhimmanci kan basirar kasar Sin, saboda an samu isassun shaidun dake nuna cewa, idan an yi amfani da dabarun Sin yadda ya kamata, to, za a samu nasarar raya aikin ilimi, da samar...
    Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban kasar, Mr. Xi Jinping, a kwanakin baya ya yi muhimmin bayani game da aikin raya harkoki masu nasaba da wayewar kai a kasarsa, inda ya ce, ci gaban dukkanin fannonin samar da ababen more rayuwa da kuma wayewar kai, muhimmiyar alama ce ta zamantarwa mai salon kasar Sin. Shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata a karfafa hadin kan jama’a bisa tunanin tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin na sabon zamani, da mai da hankali kan wayar da kan al’umma, da sa kaimin raya al’adu da kuma da’a a tsakanin al’umma, sa’an nan kuma a karfafa ayyukan ba da jagoranci, da zurfafa yin gyare-gyare...
    Iran ta sha alwashin ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Jamhuriyar Nijar. Mataimakin shugaban kasar na farko Mohammad-Reza Aref ya ce Iran na ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Nijar da sauran kasashen nahiyar Afirka bisa tsarin juyin juya halin Musulunci. Aref ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da ministan man fetur na kasar Nijar Sahabi Oumarou wanda ke Tehran, inda yake jagorantar wata tawaga, domin halartar taron hadin gwiwar tattalin arzikin Iran da Afirka karo na uku. Ya ce da gaske ne gwamnatin Iran mai ci a yanzu tana son raya dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afirka ciki har da Nijar dangane da batutuwan da suka dace....
    Haka kuma za a aiwatar da dukkan abubuwan da aka dade ana yinsu cikin shirin raya kasa a hukumance.   Ana sa ran dokar za ta kara inganta tsare-tsaren da za su tabbatar da aiwatar da shirye-shiryen raya kasa da karfafa dacewar manufofin da suka shafi dukkan bangarorin tattalin arziki da juna. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An gudanar da taro na farko na kwamitin raya cinikayya da kiyaye muhalli na hukumar kula da cinikayya ta duniya wato WTO na shekarar 2025 a birnin Geneva dake kasar Switzerland a kwanakin baya, inda tawagar wakilan kasar Sin ta karbi bakuncin taron tattaunawa kan hadin gwiwar fasaha da cinikayya da sana’o’i masu kiyaye muhalli, inda aka gabatar da dabarun Sin na raya sana’o’i da fasaha masu kiyaye muhalli. A cikin jawabansu, masanan Sin sun yi amfani da ayyukan samar da makamashin da ake iya sake amfani da su, a kasashen Habasha da Sri Lanka da kuma aikin daidaita matsalar wutar lantarki na Afirka da sauransu a matsayin misalan dabarun Sin na hadin gwiwar fasaha. Fasahohin Sin sun kunshi fannnoni...
    Yayin ziyararsa kasar Sin kwanan nan, babban mashawarcin gwammatin wucin-gadi ta kasar Bangladesh, Muhammad Yunus, ya tattauna da wakiliyar CMG, wato babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, inda a cewarsa, a matsayin kasa ta farko a kudancin nahiyar Asiya, wadda ta rattaba hannu tare da kasar Sin kan takardar bayanin hadin-gwiwa game da raya shawarar “ziri daya da hanya daya”, Bangladesh na matukar bukatar shawarar nan, ganin yadda aikin raya shawarar ke da muhimmanci sosai. Muhammad Yunus ya ce, Bangladesh na matukar bukatar cudanyar sassa daban-daban. Hanyoyin mota na taka rawar gani wajen jigilar hajoji, don haka kasar na bukatar kara shimfida hanyoyin mota. Hanyoyi su ne tamkar manyan jijiyoyin tattalin arzikin kasa, shi ya sa ya...
    A yau Lahadi ne aka bude taron shekara-shekara na dandalin tattauna raya kasa na kasar Sin na 2025 a nan birnin Beijing, taron da cibiyar binciken raya kasa ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta shirya tare da hadin gwiwar asusun binciken raya kasa na kasar Sin. Firaministan kasar Sin Li Qiang ya halarci bikin bude taron, inda ya gabatar da muhimmin jawabi, wanda a cikinsa ya jaddada aniyar kasar Sin ta kara bude kofa ga kasashen waje. Shi ma mataimakin darektan ofishin kula da harkokin yau da kullum na hukumar kudi da tattalin arziki ta kwamitin kolin JKS Han Wenxiu, wanda ya halarci taron na shekara-shekara, ya ce kasar Sin za ta dauki dukkan matakai na habaka kashe kudi, da...
    Zaunannen wakilin Sin dake ofishin MDD a Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa a kasa Switzerland Chen Xu ya yi jawabi a gun taron hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 58 kan batun kare hakkin dan Adam na kasa da kasa, inda ya yi bayani game da tunanin Sin kan kare hakkin dan Adam da kin amincewa da siyasantar da batutuwan da suka shafi hakkin dan Adam. Chen Xu ya yi nuni da cewa, ana bukatar bin ra’ayin bangarori daban daban da tunanin kare hakkin dan Adam da yin hadin gwiwa mai amfani don sa kaimi ga raya sha’anin kare hakkin dan Adam. Wasu kasashe sun yi amfani da dalilin kare hakkin dan Adam wajen tsoma...
    Kasashen Nijar da Burkina Faso da kuma Mali kowannensu sun sanar da ficewa daga kungiyar kasashe renon faransa ta (OIF). Nijar ta sanar da ficewa daga kungiyar a ranar Litini, yayin da Mali ta bi sahu a ranar Talata, aa daidai lokacin da ake raya makon kungiyar. Babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen kasar Laouali Labo, a wata wasika da ya aikewa jakadun kasar ya ce: “Gwamnatin Nijar ta yanke shawarar ficewa daga kungiyar ta OIF.” Nijar dai na daga cikin kasashen da suka asassa kungiyar ta OIF, wacce aka kafa a Yamai babban birinin kasar a ranar 20 ga watan Maris na shekarar 1970, kuma tsohon shugaban kasar Dojori Hamani na waccen lokacin na daga cikin jagororin da suka kafa...
    Ministar kula da ma’aikata da al’umma ta kasar Sin Wang Xiaoping, ta ce kasar za ta kara albarkatu da kudi domin tallafawa samar da ayyukan yi a bana, a wani yunkuri na gina wani tsarin raya kasa mai samar da ayyukan yi. Wang Xiaoping ta bayyana haka ne a yau Lahadi, yayin wani taron manema labarai kan yanayin rayuwar jama’a da taro na 3 na Majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, ya gudanar. Manchester United Na Son Lashe Firimiya A Shekarar 2028 A Mai Da Duniya Ta Zama Ta Kasa Da Kasa A cewarta, rahoton aikin gwamnati na bana ya tsara tare da kara shirya aiwatar da manufofin raya tattalin arziki da kara zuba kudi wajen bunkasa harkokin...
    Dubban Falasdinawa ne suka halarci masallacin al-aksa a cikin kwanakin Ramadan da suka wace. Inda yawansu yake kaiwa kimani 80,000. Mafi yawansu matasa ne wanda suke sallar asham da isha’I wannan duk tare da bincike mai tsananin da HKI take yi a kan hanyoyin shigar masallacin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, halartan Falasdinawa sallah a masallacin a cikin wannan watan mai al-farma yana raya al-amuran addini a cikinsa, duk tare da gwamnatin yahudawan suna sanya shingaye masu yawa don hana Falasdinawa raya masallacin. Sheikh Ikramah Sabri limamin masallacin ya na kwadaitar da Falasdinawan kan halattar sallah a masallzacin don raya shi. Banda matsayin masallacin a addinin musulunci dai, haduwar falasdinawa a masallacin alamace ta hadin...
    Jakadan Sin dake kasar Najeriya Yu Dunhai ya gana da karamar ministar harkokin waje ta kasar Bianca Odumegu-Ojukwu. Jakada Yu ya bayyana cewa, a shekarar bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu, sun sanar da inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, wanda ya zama babban ci gaba ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. A farkon shekarar bana kuma, memban hukumar kula da harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya kai ziyara Najeriya cikin nasara, hakan ya kara kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa sabon matsayi. A cewar jakadan, Sin tana son...
    A karshe dai, ya nanata muhimancin raya karfin kasa da kasa ta hanyar aiwatar da ayyuka masu alaka da hakan. Wang Yi ya jaddada cewa, kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da sassa daban daban, domin bude sabon babin raya huldar cude-ni-in-cude-ka, tare da kafa tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa mai inganci. Bayan taron, ya kuma amsa tambayoyin ‘yan jaridu, game da yadda kwamitin sulhu na MDD zai karfafa kwarewarsa ta gudanar da ayyuka, da matsayin kasar Sin kan batun Gaza da dai sauransu. (Mai Fassara: Maryam Yang)    
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A kwanakin baya ne dai Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙirƙiro sababbin hukumomin raya shiyyoyin ƙasar nan da nufin kawo musu ci-gaba. Gabanin ƙirƙirar waɗannan hukumomin, gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ce ta fara kirkirar hukumar raya yankin Neja Delta bayan wasu ƙalubale da suka dabaibaye yankin. Na baya-bayan nan ita ce Hukumar Raya yankin Arewa ta Tsakiyar ƙasar nan bayan da ’yan yankin suka nace da yin ƙorafin cewa an mayar da su saniyar ware. NAJERIYA A YAU: Dalilan Saukar Farashin Kayan Masarufi A Kaswanni DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan...
      Kayan hadi: ”Yayan Hulba (gongoni 2, Aya (gongoni 3), Ridi (gongoni 1)   Ga kuma Yadda za ku hada: Wadannan kayan hadin ku soya su duka amma sama-sama sai ku bar su su huce sanna ku daka ko ku nika ku tankade.   Yadda ake amfani da ita: Za ku dinga diban cokali 2 ko 3 kusa madara cokali 2 kusa ruwan zafi ku gauraya ku shanye, sannan ana sha ne safe da rana da dare na tsawon sati 3 ko 4. Kazalika ku nemi garin hulba ku debi kadan kusa ruwan zafi ku gauraya sai ku sanya wani abu ku dinga dandanar ruwan kuna gasa shi, sannan ku samu man hulba da man zaitun da man ridi ku...
۱