Ayatullah Khatami: Tattaunawa Da Amurka Kaskanci Ne
Published: 7th, March 2025 GMT
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran ya bayyana cewa; Tattaunawa da Amurka kaskanci ne, ga shi kuwa al’ummar Iran tana da tunani ne irin na Ashura, ba ta karbar kaskanci.
Limamin na Tehran ya yi ishara da yadda duniya ta ga yadda Donald Trump ya wulakanta shugaban kasar Ukiraniya, don haka ya kamata masu dogaro da Amurka su kwana da sanin cewa, haka makomarsu za ta kasance, domin haka halayyar girman kai take.
Haka nan kuma limamin na Tehran ya ce; tare da cewa jagoran juyin musulunci na Iran ya sha jaddada cewa, babu aiki da tunani a cikin tattaunawa da Amurka, kuma ba abu ne na girma ba, sai dai kuma da akwai wadanda ba su nuna rashin jin dadinsu, to amma yanzu da su ka ga abinda ya faru da shugaban kasar Ukiraniya,sun amince da cewa tattaunawa da Amurkan ba abu ne da ya dace da mutumincin al’ummar Iran ba.
Dangane da barazanar kasashen Amurka, Fransa, Birtaniya da Jamus, akan aiki da kuduri mai lamba; 2231, Limamin na Tehran ya ce; Tun a tsawon shekaru 45 da su ka gabata ne wadannan kasashen suke maimaita magana daya, don haka babu wani alfanu da za su samu. Ayatullah Khatami ya kuma ce; Idan kuma wadannan kasashen ba su daina yi wa Iran baraza ba, to al’ummar Iran din za su yi maganinsu.
Da limamin ya tabo furucin ministan harkokin wajen Turkiya akan Iran, Ayatullah Khatami ya ce; Alakar Iran da makwabtanta ta ginu ne akan kyakkyawar makwabtaka, kuma Iran din ba ta da niyyar yin fada da makwabtanta, wannan shi ne abinda yake kunshe a cikin tsarin mulkin Iran.
Ayatullah Khatami ya kuma ce; Siyasar Turkiya a cikin wannan yankin tana cin karo da kyakkyawar makwabtaka, kuma ya kamata ‘yan siyasar Turkiya su fahimci cewa furucin da su ka yi akan Iran zai cutar da su.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp