Leadership News Hausa:
2025-09-18@00:57:07 GMT

Munafunci Dodo Ya Kan Ci Mai Shi

Published: 7th, March 2025 GMT

Munafunci Dodo Ya Kan Ci Mai Shi

Bayan da Amurka ta sanar da sanya karin haraji, kasashen Canada da Mexico da ma Sin dukkan sun dauki matakan ramuwar gayya. A ranar 4 ga wata, bi da bi ne ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin da ma kwamitin kula da dokokin harajin kwastan na majalisar gudanarwar kasar sun sanar da jerin matakai na tinkarar matakan haraji na Amurka.

Kakakin ma’aikatar wajen kasar Sin ya kuma jaddada cewa, nuna fin karfi ba shi da amfani da kasar Sin, kuma matsawa da barazana ba hanya ce ta cudanya da kasar. Hakikanin abubuwan da suka faru a shekarun baya ma sun shaida yadda kasar Sin ke mai da matsawa da aka yi mata a matsayin karfin da ke sa ci gabanta, bisa ga juriyar masana’antunta da kirkire-kirkiren fasahohi da ma hadin gwiwarta da sassa daban daban, har ma ta yi ta murkushe makircin Amurka.

 

A hakika, al’ummar kasar Amurka suna sane da me matakan haraji da Trump ya dauka za su haifar musu. Kamar yadda wani dan kasar ya ce, “idan an samu hauhawar farashi na kaso 25%, mu kanmu ne za mu biya kudin, a maimakon gwamnati ko mutanen kasar Mexico.” Abin hakan yake, duk da cewa matakin haraji ya lalata dokokin cinikin kasa da kasa tare da haifar da rashin tabbas ga farfadowar tattalin arzikin duniya, amma daga karshe, kamfanonin kasar Amurka da ma al’ummar kasar ne za su dandana kudarsa. Daidai kamar yadda Ben Ayers, masanin ilmin tattalin arziki na kasar Amurka ya ce, “Karin iyalai a Amurka za su kara kimtsa wa shiga yanayin tattalin arziki mara tabbas da za su fuskanta a shekarar 2025.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu Ya Taya Amusan Da Gumel Murnar Samun Nasarori A Ɓangarori Daban-daban

 

Shugaban ya yaba da abinda ya kira kwarewa da juriya irin na Amusan, tare da cewa aikinta ya sake misalta irin daukakar da yan Nijeriya za su iya samu ta hanyar aiki tukuru da nuna kwazo, Tinubu ya yi fatan Gumel da Amusan su ci gaba da samun nasara a ayyukansu tare da ba su tabbacin gwamnati za ta ba su cikakken goyon baya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ya Kamata A Kiyaye Nasarorin Da Aka Cimma A Shawarwarin Sin Da Amurka 
  • Yakin Haraji Da Cinikayya Ba Zai Gurgunta Fifikon Da Sin Ke Da Shi A Fannin Raya Masana’antun Sarrafa Hajoji Da Kasar Ta Gina A Tsawon Lokaci Ba
  • Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo
  • Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani
  • Tinubu Ya Taya Amusan Da Gumel Murnar Samun Nasarori A Ɓangarori Daban-daban
  • Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila
  • Ministan Tsaron Kasar venezuela Ya Gargadi Amurka Dangane Da Kokarin Juyin Mulki A Kasar
  • Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
  • Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa