Hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta bada sanarwan cewa, sauye –sauye na asasi dake faruwa a kasar Amurka, zai shafi hukumar da ma MDD.

Kwamishinan hukumar Volker Turk ya bayyana cewa fadar ‘White House’ a halin yanzu ta na gudanar da sauye-sauye na asasi a cikin hukumomi da ma’aikatu a Amurka, wadanda kuma za su shafi al-amura da dama a cikin gida da kuma sauran kasashen  duniya.

Volker Turk ya ce al-amura da suka shafi nuna wariya ne, mai yuwa su zama akasin haka nan gaba, bayan wadannan sauye sauye sun fara aiki. Wannan dai shi ne jawabi mai muhimmancin da wani jami'an MDD ya gabatar dangane da abubuwan da ke faruwa a sabuwar gwamnatin Amurka. Turk ya kuma kara da cewa tasirin sauye-sauyen zasu kara bayyana nan gaba, a lokacinda matakan da gwamnatin Amurka ta Donal Trump ta fara aiwatar da su a kasa.  

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Araghchi : Za’ayi Tattaunawar Iran da Amurka ta gaba a Rome bayan taron E3

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a yi taro karo na hudu na shawarwari tsakanin Tehran da Washington kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Rome na kasar Italiya a ranar Asabar mai zuwa.

M. Araghchi ya fadawa manema labarai a gefen taron majalisar ministocin gwamnatin kasar na mako-mako yau Laraba cewa, inda ya ce taron na Rome zai kasance gabanin wani taro a ranar Juma’a na tsakanin Tehran da kasashen Turan nan uku da ake wa lakabi da E3 wato – Ingila, Faransa da kuma Jamus wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015.

Ya ce rawar da kasashen Turai uku ke takawa ta ragu sakamakon manufofinsu a tattaunawar da aka dade ana yi, don haka a shirye muke mu gudanar da zagaye na gaba na shawarwari da su a birnin Rome.

Babban jami’in diflomasiyyar ya kara da cewa, Tehran na da burin warware batun nukiliyarta cikin lumana.”

Da aka tambaye shi game da halin da ake ciki na baya-bayan nan na kudaden da Iran ta toshe saboda takunkumin da kasashen yamma suka kakaba mata, Araghchi ya ce daskararrun kudaden na daga cikin takunkumin da ya zama dole a dagewa iran.

Kawo yanzu Iran da Amurka sun yi tattaunawa har uku ta farko a Oman, ta biyu a Italiya sai kuma wace aka gudanar a ranar Asabar data gabata a Oman.

Dukkanin bangarorin na cewa akwai fata mai kyau a jerin tattaunawar da suka gabata.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Araghchi : Za’ayi Tattaunawar Iran da Amurka ta gaba a Rome bayan taron E3
  • Sabbin Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci: Nan Ba Da Jimawa Ba, ‘Yan Ta’adda Za Su Ɗanɗana Kuɗarsu – COAS
  • Da Alamu Amurka Ta Fara Dandana Kudarta
  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Shirya Fara Tantance ‘Yan Fansho
  • Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Na Iran Ya Ce: Maganar ‘Yan Sahayoniyya Rudu Ne Maras Amfani
  • Kungiyar Amnesty International Ta Kafa Hujja Kan Ta’asar’Yan Sahayoniyya A Gaza
  • Hajjin 2025: An Fara Yi Wa Maniyyata Allurar Rigakafi A Jigawa
  • Hajjin 2025: Jihar Kwara Ta Fara Allurar Rigakafi Ga Maniyyata
  • Jiragen Yakin Amurka Sun Kashe Mutane Da Dama A lardin Sa’ada Na Kasar Yemen
  • Lebanon:  Isra’ila Ta Kai Hari Akan Unguwar Dhahiya A Birnin Beirut