Gwamnatin Jigawa Za Ta Biya Diyar Sama Da N1.5 Biliyan Ga Wadanda Aikin Tituna Ya Shafa
Published: 26th, February 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari biyar domin biyan diyya ga wadanda aikin gina tituna a cikin gari ya shafa.
Kwamishinan yada labarai da matasa da wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse.
A cewarsa, aikin titin ya shafi garuruwa musamman Fagam, da Kila da Jugwa, da Sakuwa, da Gwaram, da Sankara, da Ringim da Bulangu, da Kafin Hausa, da Gandun Sarki, da Hadejia, da Dansure, da Roni, da Aujara, da Jahun da kuma karamar hukumar Dutse, kamar yadda ma’aikatar filaye, da gidaje, da raya birane da tsare-tsare na yanki suka gabatar.
Ya ce, majalisar ta kuma amince da kashe sama da naira biliyan takwas da miliyan dari biyu a matsayin kashi 30 bisa na kudaden shirin noman rani na shinkafa na shekarar 2025.
Ya kuma yi bayanin cewa, an amince da hakan ne da nufin samar da wadataccen abinci da inganta rayuwar miliyoyin al’ummar Jigawa ta hanyar bai wa Manoma 58,500 rance, don noma hekta 50,000 na shinkafa a fadin yankunan da ake noman shinkafa, kamar yadda ma’aikatar noma da albarkatun kasa ta gabatar.
Kwamishinan ya ce, majalisar zartaswa ta jihar ta kuma amince da sanya hannu kan yarjejeniyar tsawaita wa’adin shekaru 2 tsakanin ma’aikatar lafiya ta gwamnatin jihar Jigawa da kungiya mai zaman kanta ta Medicins San Frontiers (MSF) da ke kasar Faransa.
A cewarsa, rattaba hannu kan yarjejeniyar na da nufin karfafa kokarin jihar na rage mace-macen mata masu juna biyu da jarirai, ta hanyar samar da ingantacciyar kula ga masu juna biyu a babban asibitin Jahun da kuma cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na Miga da Ajura.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Nada Aisha Mujaddadi Sabuwar Shugabar Hukumar InvestJigawa
Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya amince da nadin Aisha Shehu Mujaddadi a matsayin shugabar Hukumar Kula da Zuba Jari ta Jihar Jigawa (InvestJigawa).
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar ga manema labarai.
Sanarwar ta ce “Aisha Mujaddadi ta samu digirinta na farko a fannin tattalin arziki a Jami’ar Maiduguri a shekarar 1996, ta kara inganta iliminta da samun digiri na biyu a fannin Gudanar da Kasuwanci (MBA) daga Jami’ar Bayero, Kano a shekarar 2011.“
Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa Aisha Mujaddadi ta samu gogewa na tsawon shekaru 19 a fannin aikin shawarwari na ci gaban kasa da kasa, inda ta yi aiki a kan muhimman ayyuka da shirye-shirye tare da Bankin Duniya, Ma’aikatar Harkokin Waje, Harkokin kungiyar kasashen renon Ingila da Ci Gaban Birtaniya (FCDO), da Tarayyar Turai (EU), wanda hakan ya bata kwarewar da ta dace da sabon mukaminta.
Ya kara da cewa, Aisha Mujaddadi ta kasance a cikin kwamitoci da dama a matakin jiha da na tarayya, kuma ta taba zama memba a kwamitin gudanarwa na Hukumar Tara Haraji ta Jihar Kaduna.
Sakataren Gwamnatin a jaddada cewa an yi nadin ne bisa cancanta, kwarewa da gaskiya, wanda ke nuna amincewar wannan gwamnati da kwarewar Aisha Mujaddadi.
Ya bayyana fatan cewa sabuwar Darakta Janar din za ta sauke nauyin da aka dora a kanta tare da kawo ci gaba mai ma’ana ga Jihar Jigawa.
Ya kara da cewa, nadin Aisha Shehu Mujaddadi a matsayin Darakta Janar na InvestJigawa ya fara aiki nan take.
Usman Muhammad Zaria