2025-11-22@22:07:00 GMT
إجمالي نتائج البحث: 8043
«da asusun ajiya»:
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce matsalar tsaro a yankin Arewa na damunsa matuƙa saboda tana kawo cikas ga zaman lafiya da ci gaban Najeriya. Ya bayyana haka ne a Jihar Kaduna, yayin bikin cikar Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), wanda Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya wakilce shi. ’Yan sanda sun daƙile harin ’yan bindiga, sun ceto mutum 25 a Zamfara Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya Tinubu, ya ce gwamnatinsa ta gaji matsalolin tsaro masu yawan gaske, amma tana aiki tuƙuru don magance su. Ya yi gargaɗin cewa Najeriya ba za ta ci gaba ba idan al’ummarta suka ci gaba da fuskantar hare-hare, talauci, da tsoro. “Ba abin da ke damuna kamar...
Mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya gana da Sakataren Yakin Amurka, Pete Hegseth, a Washington, inda gwamnatin Trump ta nuna damuwarta kan karin hare-haren da ake kai wa mabiya addinin Kirista a Nijeriya. Hegseth ya tabbatar da ganawar a shafinsa na X, yana mai cewa bangarorin biyu sun tattauna kan “mummunan tashin hankalin da Kiristoci ke fuskanta,” tare da bayyana cewa Amurka na aiki da gaggawa da Nijeriya wajen rage hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi. Ganawar ta gudana ne a daidai lokacin da Amurka ke kara nuna damuwa game da tsaro a Arewaci da tsakiyar Nijeriya, inda Boko Haram da ISWAP da kungiyoyin ƴan bindiga ke ci gaba da kai hare-hare a kauyuka, da...
Majalisar Dattijai ta nuna damuwa kan tabarbarewar yanayin tsaro a kasar sannan ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta amincewa da daukar akalla matasa 100,000 cikin rundunar sojoji domin karfafa tsarin tsaro na Nijeriya da yake fuskantar kalu bale. ‘Yan majalisar sun kuma yanke shawarar kafa kwamitin musamman domin bincikar yadda aka yi amfani da kudaden da aka ware shekaru da dama don Shirin Makarantu Masu Tsaro (Safe School Programme), a yayin da ake sake nuna damuwa cewa makarantun Nijeriya na ci gaba da kasancewa cikin hadari, inda a baya-bayan nan aka sace ‘yan mata a Jihar Kebbi. Wadannan kudurori sun biyo bayan tayin da Sanata Abdullahi Yahaya (APC, Kebbi North) ya gabatar, wanda ya yi...
Daga Aminu Dalhatu Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Zamfara ta ce ta samu nasarar ceto mutune 25 da aka yi yunkurin sacewa, bayan wani hari da ’yan bindiga suka kai wa kauyen Kuraje da ke yankin Damba a Karamar Hukumar Gusau. Wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren Juma’a 21 ga watan Nuwamban 2025, da misalin karfe 10 saura kwara, lokacin da gungun ‘yan bindiga dauke da makamai suka mamaye yankin, suna harbe-harbe tare da tasa keyar mata 10 da yara 15 domin tafiyada su. Sanarwar ta ce bayan samun kiran gaggawa, tawagar sintiri ta ’yan sanda daga sashen Damba da Sashen Ayyuka...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, ta daƙile wani hari da ’yan bindiga suka kai wa al’ummar Kuraje da ke gefen birnin Gusau. Wasu gungun ’yan bindiga, ɗauke da makamai ne, suka kutsa cikin ƙauyen suna harbi, lamarin da ya jefa mazauna Kuraje da maƙotan ƙauyukan cikin tashin hankali. Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya Mutane 315 ne suka ɓace bayan hari a makaranta Neja A yayin harin, sun yi awon gaba da mata 10 da yara 15. Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce ’yan sanda sun ɗauki mataki bayan samun kiran gaggawa. Ya ce tawagar haɗin gwiwa daga sashen Damba, Sashen Ayyuka da kuma Rundunar Tsaron Al’umma (CPG) sun isa ƙauyen cikin gaggawa. Sun...
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa za a rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya daga ranar 24 ga watan Nuwamba, 2025. A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, ma’aikatar ta ce labarin ƙarya ne, ba shi da tushe daga Gwamnatin Tarayya, Ma’aikatar Ilimi ko kuma wata hukuma ta tsaro. Obi ya yi watsi da hukuncin ɗaurin rai da rai da aka yi wa Kanu Mutane 315 ne suka ɓace bayan hari a makaranta Neja Mai magana da yawun ma’aikatar, Folasade Boriowo, ta shawarci jama’a da su yi watsi da duk wata sanarwa da ba ta fito daga hukumomin gwamnati ba. Ta ƙara da cewa jama’a su riƙa tantance gaskiyar...
Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta shirya fara mayar da rarar kuɗin ga maniyyata, sakamakon rage kudin kujerun Hajjin 2026 da Hukumar Alhazai ta Kasa, NAHCON, ta sanar. A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Habibu Yusuf Babura, ya rabawa manema labarai, ya ce Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana cewa za a mayar da rarar kuɗin ne ga maniyyatan da suka kammala biyan kudadensu a fadin jihar kafin a sanar da rage kudaden. Ahmed Labbo ya ce NAHCON ta bayyana sabon farashin cewa yankin Arewa zai biya sama da Naira Miliyan 7.6, yayin da waɗanda za su tashi daga yankin Kudu za su biya sama...
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya soki hukuncin da kotu ta yanke wa jagoran ’yan awaren ƙungiyar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu. Obi ya bayyana hukuncin matsayin “abun takaici” kuma alamar gazawar jagoranci. Sace ɗalibai: An rufe makarantu a Katsina da Taraba Gobara ta lalata gidaje 40 a sansanin ’yan gudun a Borno A ranar Alhamis ne wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai bayan samun sa da laifukan ta’addanci. Sai dai Obi ya ce Gwamnatin Tarayya ta yi kuskure tun daga farko wajen tafiyar da lamarin, kuma bai kamata ya kai wannan mataki ba. Ya ce Najeriya na fuskantar matsaloli da dama ciki har da...
Hukumar Kula da Tsaftace Muhalli da Ababen Hawa ta Jihar Kaduna (KASTELEA) ta ƙaddamar da yaƙin wayar da kan jama’a na watannin ƙarshen shekara na shekarar 2025 a Tashar Motoci ta Malam Nasiru El-Rufa’i da ke ’Yan Ƙarfe, Sabon Gari, Zariya. Taron yaƙin wayar da kan jama’a na ‘Watannin Ember’ na shekarar 2025 mai taken: “Tafiyar aminci ana cimma ta ta hanyar tuƙi cikin tsaro,” ya samu halartar hukumomin tsaro daban-daban da ke da ƙudirin rage haɗurra a kan manyan hanyoyin jihar A wajen taron, Sarkin Zazzau, Malam Ahmad Nuhu Bamalli, ya jaddada muhimmancin rawar da kowa a cikin al’umma zai taka wajen tabbatar da tsaron hanya da kuma tuƙi cikin natsuwa. Wakilin Sarkin a taron, Injiniya Ibrahim Balarabe Musa, ya...
Fira Ministan kasar Madagascar Herintsalama Rajaonarivelo ya gabatar da jadawalin ayyukan siyasa a gaban majalisar kasar, da a ciki ya kunshi yadda zaman gwamnatin rikon kwarya zai kasance da yadda zai kai ga yin manyan zabukan kasar a cikin shekara daya da rabi. Fira ministan kasar ta Madagascar ya kuma ce; A karshen watan farko na gwamantin rikon kwarya ne za a bude ttataunawa a fadin kasar, wanda kuma zai ci gaba har tsawon watanni shida. Daga nan kuma za a bude tataunawa akan madogarar shari’a da yi wa hukumar zaben kasar kwaskwarima. Bugu da kari, fira ministan ya ce, gwamantin rikon kwaryar za ta so shirya zabuka bayan watanni 14 zuwa 20 daga hawanta karagar Mulki. Dangane da matsalolin...
Shugaban Cocin Katolika reshen Kontagora, ƙarƙashin ya ce ɗalibai 88 da aka yi zaton sun tsere yayin harin da ’yan ta’adda suka kai a makarantar St Mary Secondary School da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwara ta Jihar Neja, har yanzu ba a san inda suke ba. A cewar majiyoyi, iyaye da dama sun garzaya makarantar domin kwashe ’ya’yansu bayan harin, amma ba ba su yaran ba. A baya Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindiga sun kutsa cikin makarantar da daddare a ranar Juma’a, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da ma’aikatan makarantar. Shugaban Cocin Katolika ta Kontagora, Mai Girma Bishop Bulus Dauwa Yohanna, ya sanar ta hannun mai taimaka masa, Daniel Atori, cewa an yi garkuwa da ɗalibai 303, malamai...
Wata gobara ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Mafa da Jihar Borno ta lalata matsugunan wucin gadi guda 40 tare da kayan abinci da sauran kayan gida. Kamar yadda rahoton ke nunawa cewar, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:20 na safiyar Laraba. An tuntuɓi hukumar kashe gobara ta tarayya da ta Jiha nan take, yayin da ƙungiyoyin sintiri ƙarƙashin jagorancin DPO na Mafa suka taimaka wajen daƙile cunkoson jama’a da kuma hana satar kayayyaki. Daga ƙarshe rahoton da ke garin na nuna cewar an kashe gobarar ba tare da an samu rahoton raunuka ko asarar rayuka ba. Har yanzu ba a tantance adadin kadarorin da suka lalace ba, kuma ana ci gaba da bincike kan musabbabin...
160-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku, kissoshi wadanda suka zo cikin Alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Mrtada Muttahari, ko kuma cikin littafan Mathnawa na maulana Jalaluddeen Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau. ////… Ma dalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Haddan dan Aliyu (a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata. Mun bayyana yadda Imam...
Yawan ɗaliban da aka sace a makarantar Sakandaren St. Mary’s da ke Jihar Neja ya kai 215 da kuma ma’aikata 12 a cewar Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN). Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Reshen Jihar Neja, Rabaran Bulus Dauwa Yohanna, ya ce mutum 227 aka sace a makarantar, ɗalibai 215 da kuma malamai 15. A safiyar Juma’a ne ’yan bindiga suka kutsa makarantar da ke yankin Papiri da ke Karamar Hukumar Agwara ta jihar Neja suka yi awon gaba da su. Da yake jawabi bayan ziyartar makarantar, ya bayyana cewa, “Na gana da iyayen ɗaliban kuma mun tabbatar musu cewa muna aiki tare da gwamnati da jami’an tsaro domin ganin an ceto yaran. Gwamnati ta ba da umarnin rufe...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau. Shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka shafi siyasa, tattalin, arziki, zamantakewa tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au /////… Madalla, masu sauraro zamu fara shirimmu da labarimmu na farko wanda yake cewa majalisar gwamnoni a hukumar IAEA ta amince da wani kuduri na takurawa JMI a taron da ta yi a ranar Alhamis 22 ga watan Nuwamban da muke ciki. Kuduri wanda kasashen E3 ko Traiko na...
Kakakin majalisar dokokin kasar Iran mohammad Bhakir Qalibaf ya bayyana cewa makiya JMI sun sawya salon yakaar kasar kamar yadda suka saba, a halin yanzu sun fibada karfi kan takurawa tattalin arziki da rikita al-adu da kuma zamantakewa tsakaninmutanen kasar. Kamfanin dillancin labaran IP nakasar Iran ya nakalto Qalibaf yana fadar haka a jiya jumm’a a wani taro na mayakan sa kai a nan birnin Tehran a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa, da wannan dalilin ne gwamnatin kasar ta ke karfafa kira ga mutanen kasar su kiyaye hadin kan da suke da shi, su kara dankon zumunci da ke tsakanin kabilu da bangarorin kasar don hana makiya cimma manufofinsu a wannan yakin da ke yi da kasar. Yayi...
Wani tsohon ma’aikacin hukumar leken asiri ta CIA ta kasar Amurka John Kiriakou ba ce a yakin kwanaki 12 tsakanin HKI da JMI, Isra’ila ta yi barazanar jefawa JMI makaman Nukliya idan har Amurka bata kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar Iran ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya nakalto Mr John Kiriakou yana fadar haka a cikin makon da ya gabata. Ya kuma kara da cewa saboda wannan barazanar ce gwamnatin shugaba Trump ta kaiwa cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar Iran wadanda suke Fordo, Natanz da kuma Esfahan. Ya ce shugaban yana ganin hare-haren da ya kaiwa cibiyoyin yafi sauki idan an kwatanta da makaman nukliya wadanda HKI ta yi barazanar zata yi amfani da...
A ranar Alhamis da ta gabata ce karamin kwamiti mai kula da al-amuran nahiyar afirka a majalisar dokokin kasar Amurka ya bude tattaunawa dangane da zargin da shugaban kasar Donal Trump yake yin a cewa ana kashe kiristoci a tarayyar Najeriya fiye da duk wata kasa a duniya. Wanda hakan ya say a yi barazanar daukar matakan soje idan akwai bukatar haka don kawo karshen kissan. Jaridar Premium times ta nakalto Chris Smith dan majalisan da ya jagoranci taron yana fadar cewa zargin Trump gaskiya ne kuma shi a karan kansa ya kai ziyara tarayyar Najeriya har sau uku a baya inda sakamakon ya tabbatar da hakan. Sannan Bishop Wilfred Anagbe daga jihar Benue wanda ya halarci taron ta kafar...
Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana 47 da ke faɗin Najeriya. Gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne bayan hare-haren da ’yan bindiga suka kai makarantu a jihohin Kebbi da Neja, inda suka sace ɗalibai da ma’aikata, suka kashe mutum ɗaya. Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja A wata takarda da aka aike wa shugabannin makarantu a ranar Juma’a, Daraktar Makarantun Sakandare, Hajiya Binta Abdulkadir, ta ce Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya amince da rufe makarantun na wucin gadi saboda barazanar matsalolin tsaro. Takardar ta bayyana cewa an rufe makarantun ne domin kare ɗalibai da malamai daga hare-haren ’yan bindiga, da...
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta ayyana dokar ta-ɓaci saboda yawaitar sace-sacen ɗalibai da malamai a Najeriya. Atiku, ya yi wannan kira ne bayan harin da “yan bindiga suka kai yankin Papiri da ke Ƙaramar Hukumar Agwara ta Jihar Neja. Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi Maharan sun sace ɗalibai da ma’aikatan makarantar St. Mary’s Catholic. Har yanzu hukumomi ba su tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba. Harin ya auku ne bayan sace ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka a Ƙaramar Hukumar Maga, a Jihar Kebbi, lamarin da ya nuna yadda rashin tsaro ya...
Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi, ya nemi ƙarin bayani kan dalilin ɗauke sojojin da ke gadin makarantar GGCSS Maga, gabanin harin da ’yan bindiga suka kai tare da sace ɗalibai 25. Gwamnan, ya ce gwamnati ta riga ta sanar da hukumomin tsaro game da yiwuwar kai hari, amma sojojin suka bar makarantar da misalin ƙarfe 3 na dare. Zargi: Majalisar Kano ta dawo da shugaban ƙaramar hukumar Rano kan kujerarsa Gwamnatin Neja ta zargi makarantar da aka sace wa dalibai da kin bin umarninta “An tura sojoji, amma sun bar makarantar da misalin ƙarfe 3 na dare, sannan ƙarfe 3:45 harin ya faru. Wa ya bayar da izinin su bar makarantar a wannan lokaci mai muhimmanci?” in ji Idris. Ya...
Jami’an rundunar ’yan sanda ta Jihar Delta sun kama wani fasto na cocin Omega da ke Sapele bisa zargin lalata, fyade da kuma cin zarafin mata uku. Ana zargin Faston, wanda aka bayyana sunansa da Daniel Ololo mazaunin garin Sapele da yin lalata da ’yan mata uku ’ya’yan uwa ɗaya waɗanda mambobin cocinsa ne. Gwamnatin Neja ta zargi makarantar da aka sace wa dalibai da kin bin umarninta ’Yan bindiga sun sace dalibai a wata makarantar Neja Mai magana da yawun rundunar a jihar, Bright Edafe, ya ce ’yan sanda sun samu ƙorafi a kan faston bisa zargin lalata, fyade da cin zarafi. Ya ce a ranar 17 ga watan Nuwamba, an kama wanda ake zargi a harabar cocinsa. Edafe...
’Yan bindigar da suka yi garkuwa da masu ibada a cocin Christ Apostolic Church da ke Eruku, a jihar Kwara, sun nemi Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansar kowanne mutum da suka kama. A cewar Faston cocin, Lawrence Bamidele, tsakanin mutane 30 zuwa 35 aka yi garkuwa da su a daren Talata lokacin da aka kai musu mummunan hari suna tsaka da ibada a cocin. Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi Muna roƙon Tinubu ya ƙawo ƙarshen taƙaddamar gwamnati da ASUU — Ɗalibai Majiyoyi daga iyalai da shugabannin al’umma sun tabbatar a ranar Alhamis cewa masu garkuwar sun fara kiran ’yan uwan waɗanda aka sace ta hanyar amfani da wayoyinsu. Sakataren cocin, Josiah...
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da ya koma jihar Kebbi da aiki sakamakon sace ɗalibai ’yan mata 25 da wasu ’yan bindiga suka yi a jihar. Tinubu ya umurci Matawalle, wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a Kebbi domin sa ido kan dukkan matakan tsaro da ake ɗauka domin kuɓutar da ɗaliban da aka sace. Babu wani addini da matsalar tsaron Nijeriya ta ƙyale — Fafaroma Za a aurar da marayu 200 a Zamfara ’Yan bindiga sun sace ɗalibai 25 a Makarantar Sakandiren Mata da ke garin Maga na Jihar Kebbi da misalin ƙarfe 4 na Asubahin ranar Litinin. A cewar mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga wanda...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hukuncin da kotun tarayya ta Abuja ta yanke wa shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, ya sake tayar da kura a tsakanin magoya bayansa, ‘yan yankin Kudu maso Gabas, da al’ummar Najeriya gaba ɗaya. Yayin da gwamnati ke cewa hukuncin ya biyo bayan dogon shari’a da hujjoji da suka tabbatar da aikata laifukan da ake tuhumarsa da su, wasu na ganin batun na da matuƙar sarkakiya musamman ma yadda iyalansa da magoya bayansa ke kallon wannan hukunci. NAJERIYA A YAU: Halin Kunci Da Matan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ke Tsintar Kansu A Ciki DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Shin...
Rundunar ƴansandan jihar Neja ta ce tuni ta aika jami’ai yankin da aka sace wasu ɗalibai da ba a san adadin su ba har yanzu domin kuɓutar da su. Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP W. A Abiodun ya fitar, ya ce an aika jami’an tsaro da haɗin gwiwar sojoji da sauran jami’an tsaro zuwa yankin da lamarin ya faru. Sanarwar ta ambato kwamishinan ƴansandan jihar, CP Adamu Abdullahi Elleman na jaddada ƙudirin rundunar na kuɓutar da ɗaliban ba tare da ji musu ciwo ba. Kwamishinan ƴansandan ya kuma yi kira ga al’umma su kwantar da hankali tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai a ƙoƙarin da suke yi na kuɓutar da ɗaliban. Ya kuma ce...
Ƙaramin kwamitin majalisar dokokin Amurka kan harkokin kasashen Afirka ya yi wani zama kan batun zargin kisan kiyashin da ake yi wa Kiristoci a Nijeriya da batun yadda Shugaba Donald Trump ya ayyana kasar a matsayin “wadda Amurka ke nuna damuwa a kanta kan walwalar addini,” sai dai kawunan mambobin majalisar sun rarrabu a kan batun na Nijeriya. Zaman, wanda aka yi a Majalisar Dokokin Amurka da ke birnin Washington a ranar Alhamis ya ƙunshi ’yan majalisa da masu kare hakkin dan’adam da kuma wasu kungiyoyin fararen hula. An shafe lokaci ana lugudan laɓɓa da musayar yawu tsakanin mambobin majalisar da sauran waɗanda suka halarci zaman, wanda aka kuma yada shi kai-tsaye ta intanet. Masu magana a wajen sun haɗa...
Ƴan ta’adda sun kai hari Makarantar St. Mary’s da ke ƙauyen Papiri, a ƙaramar hukumar Agwara da ke Jihar Neja a Najeriya, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da ma’aikatan makaranta da ba a tantance adadinsu ba zuwa yanzu. Rahotanni daga makarantar sun ce harin ya faru ne da tsakar dare, kuma tuni aka fara tattara bayanai domin gano yawan mutanen da aka sace. Wata majiya daga cocin Katolika a jihar ta tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, inda ta ce har yanzu ana tattara bayanai kuma za a fitar da sanarwa nan gaba. Kawo yanzu Jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ƴan Sandan Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce ana ci gaba da tattara bayanai, kuma daga bisani...
Daga Ali Muhammad Rabi’u ‘Yan bindigar da suka sace masu ibada 38 a Cocin Christ Apostolic Church (CAC), Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a Jihar Kwara sun nemi kudin fansa na Naira miliyan 100 kan kowane mutum daya da suka sace. Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa masu garkuwan sun fara kiran iyalan waɗanda aka sace a cocin. Shugaban al’umma kuma Olori Eta na Eruku, Cif Olusegun Olukotun, wanda mutane huɗu daga cikin danginsa suka kasance cikin waɗanda aka sace, ya tabbatar da hakan ga ’yan jarida. Olukotun ya ce yana cikin coci tare da mutane biyar na danginsa lokacin da lamarin ya faru, inda ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin yaran da yake kula da su ya tsere...
Daga Bello Wakili Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan Tsaro, Alhaji Bello Matawalle, da ya koma Jihar Kebbi biyo bayan sace dalibai ’yan mata 24 a jihar. An umurci Matawalle, wanda tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a jihar domin sa ido kan ƙoƙarin da ake yi na kubutar da ɗaliban da aka sace. ’Yan bindiga sun sace ɗalibai mata 24 na Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata da ke garin Maga, Jihar Kebbi, da misalin ƙarfe 4 na asubar ranar Litinin. Matawalle, wanda ake sa ran zai isa Birnin Kebbi a ranar Juma’a, ya samu ƙwarewa wajen fuskantar matsalar ’yan fashi da garkuwa da mutane a lokacin da yake gwamnan Jihar Zamfara daga shekarar 2019 zuwa 2023. Idan...
Daga Usman Muhammad Zaria Daliban makarantu daga jihohin Arewa maso Yamma da suka hada da Kano, Jigawa da Katsina sun yi kira ga masu ruwa da tsaki da su samar musu da tsaro, ingantaccen kiwon lafiya, da taftataccen ruwan sha. Daliban sun yi wannan kiran ne yayin bikin Ranar Yara ta Duniya da aka gudanar a Kano, wanda Hukumar Kula da Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ta shirya. Haka zalika ɗaliban sun nemi a mayar da yaran da ba sa zuwa makaranta domin samun ilimi mai inganci. Haka kuma, sun buƙaci a aiwatar da dokokin kare haƙƙin yara tare da ba da dama ga daidaito tsakanin jinsi, musamman a fannin ilimin ’ya’ya mata. Bugu da ƙari, sun koka...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da fitar da Naira Biliyan 3 a matsayin tallafin hadin gwiwa na kowace shekara domin inganta ilimi a matakin farko, wato UBEC 2025 Matching Grant. A wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na Jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya fitar ya bayyana cewa za a yi amfani da kudaden ne wajen gina sabbin azuzuwa, gyare-gyare, haka rijiyoyin burtsatse da kuma samar da kayan koyo da koyarwa ga dalibai da malamai. Ya ce, majalisar ta kuma amince da sama da Naira Miliyan 289 domin gina sabbin ofisoshin gudanarwa da gyare-gyare a kananan hukumomi 9 na jihar. A cewarsa, za a yi amfani da kudaden ne wajen gina ofisoshin...
Iyalan Waɗanda Aka Kashe Yayin Zanga-zangar Bangladesh Sun Yi Maraba Da hukuncin Kisan Tsohuwar Firaminstar
Iyalai da ‘yan uwan wadanda aka kashe a lokacin zanga-zangar da ta kawo karshen gwamnatin tsohuwar Firaminstar Bangaledash Sheikh Hasina a bara, sun yi maraba da hukuncin kisa da wata kotun birnin Dhaka ta yanke mata. An samu Sheikh Hasina da laifin cin zarafin bil adama tare da ba ‘yan sanda umurnin kashe masu zanga-zanga, inda aka yanke mata hukuncin a bayan idonta. Gwamnatin Bangaledash ta bukaci Indiya da ta tasa keyar Hasina da ke gudun hijira a can domin ta fuskanci hukuncin. Wakiliyar BBC ta ce Hukumomin Indiya na cewa suna ci gaba da bibiyar lamarin tsakanin Sheikh Hasina da mahukuntan Bangaledash kuma hakan na nufin Indiya na neman wata hanyar diflomasiyya akan lamarin. BBC
Shugaban kasar rasha vladmir putin ya bayyana cewa ba zamu ja baya daga ayyukan soji da muke yi a kasar Ukrain ba, bayan rahoton da fadar kremlin ta fitar dake nuna cewa dakarunta sun kutsa cikin kasar ukrain suna kusa da birnin Kupiansk mafi mahumimmanci a kasar A loakcin ziyara da babban kwamanda kasar rasha ya kai a wajen da ke cikin yakin Ukrain putin yace yanzu haka dakarun rasha sun kewaye rundunoni 15 na kasar Ukrain a garin Kupiansk, za su bada dama ga sojojin kasar su mika makamansu kuma su yi saranda Kakakin fadar kremlin Dmitry peskov ya fadi cewa putin ya karbi rahoto game da karbe kula da ikon garin Kuoansk . Wannan bayani yazo ne bayan...
Rahotanni sun bayyana cewa a zaman da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya yayi a baya bayan nan yayi kira a dauki matakin gaggawa don kawo kareshen yaduwa ayyukan ta’addanci a kasashen yammacin Afrika da kuma yankin sahel, yana gargadin cewa yankin na so ya zama cibiyar tsattsauran raayi da rikice- rikice Anasa bangaren babban sakatare janar din majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bayyan cewa yanayin da yankin sahel da sauran kasahen dake makwabtaka da shi kullum yana kara yin tsananin sosai, kamar kai hare-haren ta’addanci da kuma matsalar da ta shafi mai a kasar mali suna mummunan tasiri a yankin. Haka zalika yayi gargadin cewa kungiyoyin masu iykirarin jihadi masu yankurin kafa daular musulunci a yankin sahara ISGS...
Kafofin yada labarai na duniya sun mayar da hankali kan taron majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar Shanghai SCO na 24 da aka gudanar kwanan nan a birnin Moscow na kasar Rasha. Fira ministan kasar Sin Li Qiang ya yi kira ga kungiyar SCO da ta aiwatar da shawarar inganta tsarin shugabanci na duniya da kasar Sin ta gabatar, da karfafa kungiyar SCO a bangaren hadin kai da harkoki da kuma tasirinta. Shekaru 24 da suka wuce bayan kafuwar kungiyar SCO, a karkashin jagorancin ruhin Shanghai, an samu habakar abotan kungiyar, da kara ingancinta, shi ya sa ma ta zama kungiyar yanki mafi girma a duniya, wadda ta kare muradun kasashe mambobin kungiyar, ta kuma inganta zaman lafiya da ci gaban...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esmail Baghaei yayi tir da shigar isara’ila kasar Siriya ba bisa kaida ba, yayi gargadin cewa ci gaba da kai hare-hare da fadada siyasarta ta mamaya babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaron yanki. Haka zalika tahren ta yi gargadin cewa matakin baya bayan nan da isra’ila ta dauka wani bangare ne na nuna tsangwama da kai hare hare da aka dade ana yi ta sama da kasa da kuma mamaye kudancin Syria da zai iya jefa yankin cikin mawuyacin hali. Fira ministan isra’ila banjamin na tanyaho da wasu manyan jami’an gwamnati da suka hada da ministan harkokin wajen da na yaki sun shiga cikin kasar siriya kuma sun zarta iyakar aka yi...
Shugaban Cocin Katolika na Duniya, Fafaroma Leo XIV, ya musanta zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya. Babban limamin, ya bayyana cewa duk da cewa akwai damuwa dangane da matsalar tsaron Nijeriya, amma babu wani mabiyi na kowanne addini da matsalar ta ƙyale. Sai da Kwankwaso APC za ta iya samun nasara a 2027 — NNPP Za a aurar da marayu 200 a Zamfara “Matsalar tsaron da ake fuskanta a Nijeriya ba Kiristoci kaɗai ta shafa ba, domin ta shafi Musulmi da sauran al’ummomi baki ɗaya,” in ji shi. Fafaroman ya yi wannan furucin ne yayin da yake zantawa da ’yan jarida a lokacin da yake barin gidansa na Castel Gandolfo a Vatican, inda aka tambaye shi...
Shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya ce jam’iyyar APC ba ta da ƙarfin da zai kai ta ga samun nasara a 2027, sai dai idan ta jingina da tasirin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar NNPP ta jihar, Dungurawa ya ce APC a Kano har ma da matakin ƙasa “ta rasa shugabanci da tsari”, wanda hakan, a cewarsa, ya sa suke yawan neman kusanci da Kwankwaso. Muna roƙon Tinubu ya ƙawo ƙarshen taƙaddamar gwamnati da ASUU — Ɗalibai IAEA ta buƙaci Iran ta bayyana yawan makamashin nukiliyar da ta mallaka A cewarsa, “Wannan mutanen APC ba su da ƙarfi, kuma a halin yanzu sun shiga ruɗani. Sun san...
Ƙungiyar ɗalibai ’yan Jihar Kano ta roƙi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, gwamnoni da ’yan Majalisar Tarayya da su kawo ƙarshen taƙaddamar Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU. Ƙungiyar ɗaliban ta ƙasa reshen Jihar Kano (NAKS) ta roƙi shugabannin da su gaggauta aiwatar da duk mai yiwuwa domin warware taƙaddamar da ke tsakanin gwamnati da ASUU. IAEA ta buƙaci Iran ta bayyana yawan makamashin nukiliyar da ta mallaka An yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai Aminiyar ta ruwaito cewa, ɗaliban sun yi wannan kiran ne yayin wani taron manema labarai da shugabannin ƙungiyar a jami’o’in Bayero da kuma North West —Mudassir Adamu Musa da Asahabulkhair Labaran Usman —suka jagoranta. Ɗaliban sun bayyana cewa yajin aikin da ƙungiyar ASUU...
Kwamitin hukumar hana yaɗuwar makamin nukiliya IAEA a Majalisar Dinkin Duniya, ya buƙaci ƙasar Iran da ta bayyana yawan makamashin nukiliyar da ta mallaka. Wannan dai na zuwa ne bayan kwamitin ya amince da wani ƙuduri da zai tilasta wa Iran bayyana musu yawan makamashin nukiliyarta. An yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai Kotu ta sami Nnamdi Kanu da laifukan ta’addanci A cewar sabon ƙudurin da ƙasashe 19 suka yi na’am da shi, dole Tehran ta bayar da kai bori ya hau ta hanyar sallama duk wasu bayanai gamsassu, da kuma ba wa ƙwararrun jami’an IAEA damar shiga wuraren da take gudanar da shirinta na bunƙasa makamashi. Ƙudurin ya kuma ce dole ne Iran ta bayar da...
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, babban birnin Nijeriya, ta yanke wa fitaccen jagoran masu fafutukar kafa ƙasar Biafra Nnamdi Kanu, hukuncin ɗaurin rai-da-rai, bayan samunsa da aikata laifukan ta’addanci. Masu gabatar da ƙara sun buƙaci a yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin kisa, to amma Mai Shari’a James Omotosho, ya bayyana cewa a yanzu ba a amfani da hukuncin kisa, a maimakon haka ya yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sami jagoran haramtacciyar ƙungiyar neman kafa kasar Biyafara ta IPOB, Nnamdi Kanu, da laifukan ta’addanci da aka zarge shi da aikatawa. Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis, Mai Shari’a James Omotosho, ya amince da batutuwa uku da aka gabatar a shari’ar, inda ya yanke hukunci a kan su daga bangaren masu gabatar da ƙara. Gwamnatin Kwara ta rufe makarantu a kananan hukumomi 4 saboda matsalar tsaro Wayar wutar lantarki ta kashe mutum 4 a wajen cashiya a Legas Alkalin ya ce barazanar tashin hankali da Kanu ya yi a cikin jawabansa ta haifar da tsoro da damuwa a zukatan jama’a a yankin Kudu maso Gabas. Justice Omotosho ya ƙara da cewa bisa...
Mutum uku da wani yaron babbar motar kaya sun rasa ransu bayan wayar wutar lantarki kashe su a lokacin wani bikin nadin sarauta a unguwar Idimu da ke Ƙaramar Hukumar Alimosho ta jihar Legas, bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne ranar Talata, 11 ga watan Nuwamba, kuma an gano cewa yaron motar, wanda ba a tantance sunansa ba tukuna, ya mutu nan take a wurin. Najeriya ta ɗora alhakin taɓarɓarewar harkokin tsaronta kan Amurka Babu addinin da ake yi wa kisan ƙare dangi a Binuwai — Gwamna Alia Rahotanni sun ce wani mazaunin unguwar da aka karrama da sarauta ne ya shirya taron cashiyar a titin Anjorin domin murnar nadin. Sai dai yayin da ake tsaka da bikin,...
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya jagoranci manyan jami’an Gwamnatin Nijeriya zuwa Amurka don tattaunawa game da zargin kisan ƙare dangi da ake yi wa Kiristoci. Lamarin ya samo asali ne bayan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya goyi bayan kafa ƙasashe biyu na Isra’ila da Gaza. A farkon watan nan, Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi barazanar daukar matakin soji a kan Nijeriya, kuma ya bukaci ‘yan majalisar dokokin kasar, ciki har da dan majalisa Riley Moore, su binciki lamarin. Ko da yake Nijeriya ta karyata ikirarin, amma Amurka ta ci gaba da jadadda zargin kisan Kiristoci. A ranar Talata, mawakiyar Amurka, Nicki Minaj a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ta...
Gwamnatin Tarayya ta ɗora alhakin dawowar hare-haren ta’addanci, ciki har da sace dalibai mata a jihar Kebbi da kai hari a coci a jihar Kwara, kan kalaman da Amurka ta yi kwanan nan a kan Najeriya. Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya ce sakonnin da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa, inda ya zargi Najeriya da “kisan kiyasin Kiristoci” tare da barazanar tura sojojin kasarsa, sun kara wa wasu ƙungiyoyin ’yan ta’adda kaimin kai hare-hare. Babu addinin da ake yi wa kisan ƙare dangi a Binuwai — Gwamna Alia Yadda maganin sauro ya yi ajalin magidanci da iyalinsa a Kano “Kalaman da Amurka ta yi kwanan nan sun kara wa wasu ƙungiyoyin masu tayar da kayar baya da ke son...
Bayan kwashe watanni da dama ana ta cece-kuce tsakanin hukumar kula da sufurin jiragen sama ta najeriya da kuma kamfanin jiragen sama na kasar Qatar, daga karshe dai hukumar kula da zirga zirgar jiragen sama ta najeriya ta ci tarar kamfanin naira miliyan 5 saboda kate dokokin da suka shafin fasinjojinta. An fitar da wannan sanarwa ce a shafin x na micheal achimugu daraktan kula da hulda da jama’a da kula da fasinjoji, ya kara da cewa wannan hukumci ya sanya adadin kamfanonin jiragen sama da aka ci tara sun kai guda 7 a wannan shekarar ta 2025 Hukumar NCAA ta zargi kamfanin jiragen sama na Qatar airways a watan satumban shekarar da muke ciki da take dokokin kula da...
Rahotanni sun bayyana cewa kasashen Iran da malesiya sun cimma yaejejeniyar kara fadada dangantar yin aiki tare a bangaren Addinin da Ala’adu musamman a bangaren kimiyar alkur’ani bayan tarurruka da manyan jami’an gwamnati suka yi a birnin kuala Lumpur babban birnin kasar, Wannan yarjejeniyar za ta kara karfafa hadin guiwa tsakanin manyan kasashen musulmi adaidai lokacin da kasashen musulmi suke fuskantar matsalolin aladu da tasirin kasashen yamma a tsarin zaman takewarsu da tashe tashen hankula na siyasa musamman ma kan yankin falasdinu. Kasashen biyu suna da matsaya daya na dogon lokaci a bangaren abincin Halal, aladun musulunci da kuma ilimin Addinin, don haka wannan tattaunawar da aka yi an sake sabunta alakar ne bisa ababen girmama wa na musulunci da...
Gwamnan Jihar Binuwai, Hyacinth Alia, ya ce babu wani addini ko mabiyansa da ake yi wa kisan ƙare dangi a jiharsa ko a Najeriya baki ɗaya. Ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba a wani taron da Hukumar Kare Haƙƙin Dan Adam ta Ƙasa (NHRC) ta shirya a Abuja kan kare haƙƙoƙin mutanen da aka tilasta musu barin gidajensu. Yadda maganin sauro ya yi ajalin magidanci da iyalinsa a Kano NAJERIYA A YAU: Halin Kunci Da Matan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ke Tsintar Kansu A Ciki Gwamna Alia, wanda tsohon Faston Katolika ne, ya ce: “A Binuwai, babu wani kisan kare addini, ƙabilanci, launin fata, ƙasa ko jiha. “Muna da wasu matsalolin tsaro, amma ba kisan addini...
Wani magidanci tare da ɗaukacin iyalinsa huɗu sun rasu sakamakon wata gobara da ta tashi a sanadin kunna maganin sauro a layin Baba Impossible da ke Unguwar Kundila, da ke Ƙaramar Hukumar Tarauni a Jihar Kano. Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da tashin wutar da misalin ƙarfe 4:13 na Asubar ranar Laraba. NAJERIYA A YAU: Halin Kunci Da Matan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ke Tsintar Kansu A Ciki Kotu ta sanya ranar fara shari’ar shugabannin ƙungiyar Ansaru Mai magana da yawun hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya ce sun samu kiran wani ma’aikacinsu, HFS Abba Datti, game da gobarar. A cewarsa ba tare da ɓata lokaci ba suka tura jami’ansu daga hedikwatar hukumar zuwa wajen...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mata da dama da aka yi garkuwa da su na shiga wani irin mawuyacin hali yayin da suke hannun wadanda suka sace su, suna fuskantar rayuwar kaskanci, da cin zarafi, da muzgunawa da wasu irin yanayi wanda sai ka tausaya musu. Irin wadannan mata a wasu lokutan basa tsira da rayukansu, a wasu lokutan kuma ko sun tsira, sukan shiga halin ciwon damuwa wanda ke daidaita musu rayuwa, a wasu lokutan ma har sai sun ji kamar su dauki rayuwar su. NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Shirin Najeriya A Yau na...
Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 15 ga watan Janairun 2026, don fara shari’ar shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru; Mahmud Usman da Abubakar Abba. Ana zargin su da jagorantar ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, kuma Hukumar DSS ce ta kama su tare da gurfanar da su a kotu. Ribadu ya jagoranci tawaga zuwa Amurka don ƙaryata zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana An tsara faea sauraren shari’ar a ranar Laraba, amma aka ɗage bayan lauyoyin waɗanda ake tuhuma sun nemi a ƙara musu lokaci. Lauyansu, B.I. Bakum, ya bayyana cewa har yanzu suna jiran takardun zargi da wajen DSS. Haka kuma, ya nemi a mayar da...
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa daftarin kudirin da kasar Canada ta gabatar yana cike da siyasa ne kawai hasali ma nuna kin jinin Iran ne. Mataimakin Wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya, game da daftarin kudurin da Canada ta gabatar, ya ce: “Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta nuna adawarta ta musamman ga wannan daftarin, wanda aka yi shi bisa dalilai na siyasa, son rai, da kuma na neman haddasa barna.” Gholamhossein Darzi, Jakadan Iran kuma Mataimakin Wakilin Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana a ranar Laraba, a lokacin zaman Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya na Uku kan kudurin kare hakkin dan adam na Canada kan Iran: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada cewa: “Mun yi...
Kamfanonin labarai na Reuters da AFP sun rawaito cewa Amurka ta shawarci Ukraine ta amince da Crimea da sauran yankunan da Rasha ta mamaye mata da kuma rage girman sojojinta zuwa rabi kamar yadda yake kunshe a sabuwar shawarar da Amurka ta gabatar na samar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu. Ukraine ta sami sabuwar, wacce ke bukatar Kiev ta mika yankunan dake karkashin ikon Rasha da kuma rage yawan sojojinta zuwa 400,000 kamar yadda jami’an Amurka da aka sakaya sunansu suka shaida wa Reuters da kamfanin dillancin labarai na AFP. Shirin ya kuma tanadi Ukraine ta mika dukkan makamai masu kaiwa nesa. Bayanai sun ce da alama shirin ya maimaita sharuddan Rasha wadanda da Ukraine ta sha watsi da...
Sudan ta yaba da kokarin zaman lafiya da Amurka da Saudiyya suka yi na dakatar da zubar da jini a kasar. A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin X, Majalisar Mulkin Sojan Sudan ta yi maraba da “kokarin Saudiyya da Amurka na kawo zaman lafiya mai ga Sudan.” Ta gode wa Washington da Riyadh saboda “sha’awarsu da kuma ci gaba da kokarinsu na dakatar da zubar da jinni a Sudan” kuma ta tabbatar da shirin Sudan na yin tattaunawa da kasashen biyu “don cimma zaman lafiyar da al’ummar Sudan suka dade suna jira.” Wannan sanarwar ta zo ne jim kadan bayan da Shugaba Donald Trump ya ce Amurka “za ta fara dubi lamarin Sudan” bisa bukatar Yarima Mohammed...
Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya jagoranci wata tawagar gwamnati zuwa Amurka domin mayar da martani kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya. Wannan zargi ya samo asali ne bayan mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya nuna goyon bayansa wajen kafa ƙasashe biyu tsakanin Isra’ila da Gaza. Wardley ya zama zakaran damben boksin na duniya Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana A farkon wannan watan ne Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ayyana Najeriya cikin jerin ƙasashen matsala ta musamman. Sannan Trump ya umarci wasu ’yan majalisar Amurka, ciki har da Ɗan Majalisa Riley Moore da su binciki lamarin. Duk da ƙoƙarin da Najeriya ta yi na bayyana...
Ana sa ran za a karrama shahararren ɗan damben boksin na Birtaniya, Fabio Wardley, da kambun zakarun ajin masu nauyi na WBO, bayan Oleksandr Usyk ya janye daga kare kambunsa a fafatawar da zai yi da Wardley. Janyewar ta faru ne bayan Usyk, ɗan kasar Ukraine, ya shaida wa Hukumar Damben Boksin ta Duniya (WBO) cewa ba zai kare kambunsa a kan Wardley ba. Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana Na sha alwashin kafa tarihi a Camp Nou — Lamine Yamal WBO ta tabbatar da cewa Usyk “ya zaɓi ya ajiye kambun ne saboda wasu dalilai da suka gamsar da hukumar.” A halin yanzu, Usyk na ci gaba da riƙe kambuna uku: WBA, WBC da IBF,...
Tauraron ƙwallon ƙafar ƙungiyar PSG da ƙasar Morocco, Achraf Hakimi, ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana.
Fitaccen ɗan wasan gaba na Najeriya da ke taka leda a ƙungiyar Galatasaray ta Turkiyya, Victor Osimhen, ba zai halarci bikin karrama gwarazan ‘yan wasan Afirka na 2025 ba. Osimhen, wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Afirka a 2023, ya bayyana cewa ya koma Turkiyya ne domin duba lafiyarsa, bayan raunin da ya samu a wasan da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta doke Najeriya. Tankin ruwa ya kashe mutum 4, wasu sun jikkata a Jigawa An yanke wa shugaban ISWAP hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari A yau Laraba ne Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) za ta sanar da sunayen gwarazan ‘yan wasan nahiyar na shekarar 2025, a yayin babban bikin da za a gudanar a Morocco. Za...
An shiga jimami a garin Zugai da ke Ƙaramar Hukumar Roni ta Jihar Jigawa, bayan da wani tankin ruwa ya faɗo tare yin sanadin rasuwar mutum da jikkata wasu. Daga cikin waɗanda suka rasu har da wata mace mai juna biyu. An yanke wa shugaban ISWAP hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari Gwamna Abba ya gabatar da N1.36trn a matsayin kasafin 2026 Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya auku ne kwana uku bayan shugaban Ƙaramar Hukumar, ya raba ruwa ga masu sana’r sayar da ruwa, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin wasu mutane. Tankin ruwa, wanda ke amfani da hasken rana wajen samar da ruwa, ya fashe yayin da mutane da yawa suka taru a ƙasa domin...
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa wani shugaban ISWAP Hussaini Ismaila, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bayan samun sa da aikata laifukan ta’addanci. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya yanke hukuncin ne bayan Ismaila, wanda ake kira Mai Tangaran, ya amsa tuhume-tuhume guda huɗu da Hukumar DSS ta gabatar a kansa. Gwamna Abba ya gabatar da N1.36trn a matsayin kasafin 2026 Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya DSS ta ce Ismaila ne, ya jagoranci kai wasu hare-haren ta’addanci a Kano a shekarar 2012. Hare-haren sun haɗa da harin Hedikwatar ’Yan Sanda ta Bompai, Barikin ’Yan Sandan Mopol a titin Kabuga, ofishin ’yan sanda na Farm Centre, ofishin ’yan...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin 2026 na kuɗi Naira tiriliyan 1.36 a Majalisar Dokokin jihar. Kasafin wanda aka yi laƙabi da “Kasafin Gine-gine, Ci Gaban Kowa da Ɗorewar Ci Gaba.” Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya Yayin jawabi da ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba, gwamnan ya ce an tsara kasafin ne don samar da sauye-sauye, kammala manyan ayyuka, inganta ilimi da harkar kiwon lafiya. Ya bayyana cewa za a kashe Naira biliyan 934.6 (kashi 68) a manyan ayyuka kamar hanyoyi, gine-gine da sauran muhimman ayyuka. Sauran Naira biliyan 433.4 (kashi 32), za su tafi...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin 2026 na kuɗi Naira tiriliyan 1.36 tiriliyan a Majalisar Dokokin jihar. Kasafin wanda aka yi laƙabi da “Kasafin Gine-gine, Ci Gaban Kowa da Ɗorewar Ci Gaba.” Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya Yayin jawabi da ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba, gwamnan ya ce an tsara kasafin ne don samar da sauye-sauye, kammala manyan ayyuka, inganta ilimi da harkar kiwon lafiya. Ya bayyana cewa za a kashe Naira biliyan 934.6 (kashi 68) a manyan ayyuka kamar hanyoyi, gine-gine da sauran muhimman ayyuka. Sauran Naira biliyan 433.4 (kashi 32), za su...
Cibiyar Blue Sapphire ta kaddamar da wani shiri na musamman da aka kirkiro domin ƙarfafa gwiwar mata ’yan kasuwa a fannin dinkin kayan sawa da kuma harkokin kirkira a arewa maso yammacin Najeriya. Cibiyar na aiwatar da wannan shiri ne tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar ’Yan Kasuwa Mata ta Arewa (ANWE) da Jami’ar Northwest Kano, tare da tallafin Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU). Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’ Da take jawabi a wajen kaddamarwar a Kano ranar Talata, shugabar cibiyar, Maryam Lawan Gwadabe, ta ce an kirkiro shirin ne domin samar wa mata amintaccen muhallin da za su yi amfani da shi wajen...
Shugaban ƙungiyar masu sayar da tsofaffin ƙarafa a jihar Gombe, A.A. Laja, ya ce gobarar da ta tashi a kasuwar tsofaffin ƙarafa da ke kasuwar katakon jihar ta jawo masa asara da ta kai sama da Naira miliyan 500. Lamarin ya faru ne a daren Laraba, inda wutar ta ƙone shaguna fiye da 30 da ke ɗauke da kayan kasuwancinsa. Sanatan Enugu ya mutu a Birtaniya ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’ A.A Laja, wanda ya yi magana da wakilinmu jim kaɗan bayan aukuwar lamarin, ya ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 10 na dare, ta kuma ci gaba da ci har zuwa karfe 4:00 na Asuba, saboda rashin isowar jami’an kashe gobara cikin...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da tafiyarsa zuwa Birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu, da Luanda na Angola, sakamakon sace ɗalibai a Jihar Kebbi da kuma harin da aka kai wa masu ibada a wata coci da ke yankin Eruku a Jihar Kwara. Tinubu, shirya barin Abuja a ranar Laraba domin halartar taron G20 karo na 20 da kuma Taron AU-EU karo na bakwai. Sanatan Enugu ya mutu a Birtaniya ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’ Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba. “Shugaban ƙasa ya umarci sojoji da ’yan sanda da su aike ƙarin jami’ai zuwa waɗannan yankuna domin a tabbatar...
Majalisar Dattawa ta shiga cikin jimami a ranar Laraba bayan mutuwar Sanata Okey Ezea, mai wakiltar mazabar Enugu ta Arewa. Bayanai sun nuna marigayin ya rasu ne a kasar Burtaniya inda yake jinya. ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’ Mai taɓin hankali ya kashe soja a Legas Ezea, wanda aka zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar LP, shi ne kaɗai Sanatan da ya ci zabe daga Enugu karkashin jam’iyyar a Majalisar Dattawa ta 10. Rasuwarsa ta sa ya zama sanata na biyu daga yankin Kudu maso Gabas da ya rasu cikin shekaru biyu, bayan mutuwar Sanata Ifeanyi Ubah daga Jihar Anambra, wanda shi ma ya rasu a Landan a watan Yuli 2024 yana da shekara 52. Da labarin...
Shugabar kasar maziko Claudia shinbaum ta fadi a cewa kasarta ta yi watsi da duk wani kokarin tsoma bakin kasashen wajen da kuma kalaman da shugaban Amurka Donald Trump yayi na kai harin soji kan iyakar kasar. A farkon makon nan ne trump yace yana so ya umarci sojoji su kaddamar da wani samame a kasar meziko domin yakar masu fataucin miyagun kwayoyi, yace wata dama ce gareshi ya aiwatar da wannan aiki don haka zai yi duk abin da ya dace wajen ganin an kawo karshen masu fataucin miyagun kwayoyi a yankin. Da aka tambayeshi ko zai nemi izinin kasar Maziko, sai yace ya riga yayi Magana da jami’an gwamnatin meziko sai dai basu gamsu da kokarinsa ba, amma...
Amina Hassan, matar Yakubu Makuku, mai gadin makarantar ’yan mata ta GCGSS Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu a Jihar Kebbi, wadda aka kai wa hari da safiyar Litinin, ta bayyana yadda aka kashe mijinta. Da take magana da ’yan jarida a wurin da lamarin ya faru, ta ce bayan da maharan suka kutsa cikin makarantar, sai suka shigo cikin gidansu. Mai taɓin hankali ya kashe soja a Legas HOTUNA: Gobara ta laƙume kasuwar Katako a Gombe Matar ta ce ba ta san cewa mutane ne a bakin ƙofar ba sai da suka shigo cikin ɗakinsu. “Da misalin ƙarfe 4:00 na Asuba a ranar Litinin muna kwance ni da mijina sai muka ji ana ƙoƙarin karya ƙofar dakinm. Na...
Majalisar Wakilai ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya sake kawo sabuwar dabarar da za ta kawo karshen kashe-kashe, da sace-sace da sauran ayyukan ‘yan bindiga a Jihar Zamfara da ma kasa baki daya. Wannan ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa na kula da muradun jama’a da dan majalisa mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe ta jihar Zamfara, Hon. Kabiru Amadu, ya gabatar a zaman majalisar . A yayin gabatar da kudirin, Amadu ya bayyana cewa, idan aka yi la’akari da kalubalen tsaron da “yaki ci yaki cinyewa” a Jihar Zamfara da ma fadin kasar, za a iya cewa, “gwamnati ba ta yi abin da ya dace ba don kare rayuka da kadarorin ‘yan Nijeriya don ba su damar...
Wani mutum da ake zargin yana fama da matsalar tabin hankali ya kai hari tare da kashe wani soja a yankin Imota da ke Ikorodu a jihar Legas. Lamarin, wanda ya faru a fili da rana tsaka a ranar Lahadi, ya sa makwabtan wurin da dama guduwa don neman tsira. Gobara ta laƙume kasuwar Katako a Gombe Amurka za ta binciki zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya ranar Alhamis Shaidu sun bayyana cewa wanda ya kai harin, wanda ba shi da makami sai sanda ta itace, ya kusanci sojan ya dinga dukan shi da sandar. Sojan da ya rasu, wanda aka ce yana aiki a karkashin Operation AWASE, rundunar haɗin gwiwa ta musamman da ke yaki da laifuka...
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa dole ne kudirin Amurka da MDD ta amince da shi ya tabbatar da kare hakki da yancin Falasdinawa a sahun gaba samar da kasar Falasdinu. Jakadan Iran kuma wakilin dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeed Iraqini, ne ya bayyana haka, a matsayin martanin ga amincewar da kwamitin Tsaro ya yi da daftarin kudirin Shugaba Donald Trump na Amurka game da Gaza. Iran ta yi gargadi akan amfani da wannan kuduri a hanyar da za ta keta ko ta wargaza hakkokin al’ummar Falasdinawa ba, musamman ‘yancin cin gashin kai da kuma kafa kasar Falasdinawa mai cin gashin kanta. A Kudurin da aka amince dashi jiya Litinin, Iran ta jaddada damuwar da wasu membobin...
Kasar Saudiyya ta sanar cewa za ta kara hannun jarinta a Amurka zuwa dala tiriliyan daya, daga dala biliyan 600 da kasar ta zuba a baya. Yariman Saudiyyar ne Mohammed Ben Salman ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai tare da Shugaban Amurka Donald Trump a ziyarar da ya kai fadar gwamnatin Amurka, bayan ganawar sirri da suka yi. A baya ne Trump ya bukaci Saudiyya da ta kara hannun jarinta a Amurka, sannan ya bukaci yariman ya tabbatar, inda shi kuma ya amsa da cewa, “tabbas.” Shugaban na Amurka ya ce Saudiyya za ta zama “babbar kawar kawance wacce ba daga NATO ba,” Ya kuma sanar da karfafa hadin gwiwar soja zuwa wani matsayi mafi...
Wani harin Isra’ila ya kashe akalla mutane 15 a sansanin ‘yan gudun hijira na Falasdinawa mafi girma a Lebanon. An kuma kwantar da adadi mai yawa na mutane a asibitoci a birnin Sidon bayan harin na Ain al-Hilweh da ke can ranar Talata, in ji kamfanin dillancin labarai na kasar Lebanon (NNA). Sojojin Isra’ila sun yi ikirarin kai harin, kan abin suka kira, membobin kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas a sansanin. Saidai kungiyar ta yi watsi da zargin, tana mai cewa yawancin wadanda abin ya shafa yara ne. https://hausatv.com/wp-login.php?adminpanel&redirect=false https://hausatv.com/wp-login.php?adminpanel&redirect=false Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name*...
A ranar Alhamis, 20 ga watan Nuwamban 2025, ake sa ran Majalisar Wakilan Amurka za ta gudanar da zama na musamman domin bincikar zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya. Kwamitin Majalisar Wakilan kan Afirka ya sanya ranar domin bitar fasalin da Shugaba Donald Trump ya yi kwanan nan na sanya Nijeriya a matsayin kasar da ake sa wa ido na musamman, CPC, kan zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi. Gwamnan Taraba ya dakatar da ficewa daga PDP saboda sace ɗalibai a Kebbi Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a Kebbi Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa, an gayyaci mambobin Kwamitin Harkokin Waje na majalisar, wanda aka shirya za a yi tattaunawar da...
Gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya sanar da dakatar da sauya sheƙa daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC a dalilin sace ɗalibai mata ’yan sakandire da aka yi a Jihar Kebbi. Gwamnan ya ce zai ci gaba da tattaunawa da kuma nazari kan lokacin da ya fi dacewa ya sauya sheƙar tare da magoya bayansa. Mutane 7 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a Kebbi Aminiya ta ruwaito cewa, da sanyin safiyar Litinin, 17 ga watan Nuwambar 2025, mahara suka shiga a makarantar sakandare ta ’yan mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi, inda bayanai ke nuni da cewa sun yi awon gaba da ɗalibai 25 tare da halaka mataimakin...
Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suna ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon, da a yau Talata su ka kai wani hari a garin Bint-Jubail da ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya da kuma jikkatar wani. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya ambato ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon tana cewa; Birnin na Bint Jubail ya fuskanci hare-hare ta hanar amfani da jirgin sama maras matuki, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya. Tashar talabijin din ‘almanar’ ta Lebanon ta ambaci cewa, wani jirgin “sra’ila” maras matuki ta jefa bom a kan wata motar haka rami da hakan ya yi sanadiyyar konewarta, wanda shi ma sabon keta yarjejeniya ne. Mahukunta a yankin na “Bint-Jubail” sun fitar da bayanin...
A wani labari da kungiyar “ISWAP” mai alaka da “Isis” ta watsa, ta sanar da kashe wani babban jami’in sojan Najeriya a wani kwanton bauna da ta yi wa sojoji a kusa da kauyen Wajiroko dake Jahar Borno a ranar Juma’ar da ta gabata. Sanarwar kungiyar ta “Isis” ya kuma kunshi cewa, baya ga Birgediya janar Uba da su ka kashe, sun kuma kashe wasu sojojin 4. Kamfanin dillancin labarun “Reuters” da ya tuntubi rundunar sojan kasar ta Najeriya domin samun Karin bayani akan abinda ya faru bai sami jawabi ba. Sai dai rundunar sojan ta Najeriya ta ce labarin da ake watsawa na kama babban jami’i mai mukamin janar, ba gaskiya ba ne, kuma bai kamata ‘yan kasa su...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta doke Enugu Rangers da ci 2-0 a wasan mako na 13 na Firimiyar Najeriya da suka buga a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a Jihar Kano. Umar Bala Mohammed ne ya fara zura ƙwallo ta farko a minti na 25, kafin Joseph Kemin ya ƙara ta biyu a minti na 72 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci. HOTUNA: Fada ya barke a Hedikwatar Jam’iyyar PDP ’Yan bindiga sun sako mutane 45 bayan sulhu a Katsina Wannan nasarar ce ta uku da Barau FC ta yi cikin wasanni 12 da ta buga a kakar bana, inda ta yi kunnen doki a wasanni huɗu, aka kuma doke ta a biyar. Yanzu...
Ministan harkokin wajen Najeriya ya ce kasar ta soma tattaunawa da Amurka, bayan barazanar da Shugaba Trump ya yi na kai wa Najeriya harin soji kan kisan kiristoci da ya ce ana yi a kasar. A wata hira da kamfanin dillancin labarai na AFP, yayi da Yusuf Maitama Tuggar ya ce abin da suke tattaunawa a kai shi ne yadda za su hada kai wajen magance matsalolin tsaro don amfanin duniya. A farkon watan Nuwamban nan Trump ya ce ya bai wa ma’aikatar tsaron Amurka umurnin ta soma tsara yadda za ta kai hari Najeriyar. Sai dai ministan ya ce ba ya tunanin Amurka za ta yi hakan, ” muna ci gaba da tattaunawa, kuma ana samun ci gaba a...
An ba wa hamata iska a Hedikwatar Jam’iyyar PDP da ke Abuja a tsakanin bangarorin da ke hamayya da juna. Fadan ya barke ne bayan bangarorin sun halarci ofishin domin gudanar da tarukansu daban-daban a safiyar Talata. Idan ba a manta ba, bangaren Ministan Abuja, Nyesom Wike, wadanda uwar jam’iyyar ta dakatar a yayin babban taronta na kasa da ya gudana a karshen mako ya kira taron gaggawa a yau Talata a hedikwatar Jam’iyyar da ke Wadata Plaza a Abuja.
Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar-Janar Waidu Shuaibu, ya umarni dakarun soji cewa ya zama tilas su nemo sannan su ceto daliban da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Makarantar ’Yan Mata ta Gwamnati (GGCSS) da ke yankin Maga a Jihar Kebbi. Janar Waidi Shuaibu ya bayar da umarnin ne a yayin ziyarar aiki da ya kai, Jihar Kebbi, washegarin harin ’yan bindiga suka kai makarantar da ke Karamar Hukumar Danko Wasagu.
“Lokacin da Wike, Makinde, Ugwuanyi, Ikpeazu da Ortom suka kafa G5, bana are da su. Amma duk da haka, Wike abokina ne sosai. Lokacin da PDP ta samu matsala Wike ne ya yi ƙoƙarin tallafa mata,” in ji Anyanwu. Ya ƙara da cewa Wike bai fice daga PDP ba. Anyanwu ya kira taron gangamin PDP da aka yi a Ibadan a matsayin ɓata lokaci, yana mai cewa ba a yi sa bisa ƙa’ida ba. Ya ce dakatar da shi daga matsayin Sakataren jam’iyyar na Ƙasa ba a kan ka’ida yake ba saboda jam’iyyar ba ta bi umarnin kotu ba. Ya kuma ce taron bai haɗa jihohi da dama ba, don haka bai samu cikakken goyon baya ba. A yayin babban...
Iyayen ɗalibai ’yan mata 25 ’yan bindiga sace ɗakunan kwanansu a Jihar Kebbi sun bayyana irin tashin hankali da suka shiga bayan abin da ya faru. “Ita kaɗai gare ni,” in ji Malam Muhammad Maga, mahaifin Nafisa, wadda ita kadai ya haifa, kuma take cikin ɗaliban da ’yan bindiga suka sace a makarantar. Malam Muhammad wanda idanunsa ke cike da ƙwalla ya ce, “Roƙona Allah Ya sa a dawo min da ita lafiya, ita kaɗai gare ni. Ina roƙon Gwamna Idris ya taimaka a dawo mana da su. Mun san ƙoƙarin da yake yi a fannin tsaro a tsawon shekara biyu da ya yi a kan mulki.” Shi ma Malam Aliyu Yakubu, ɗaya daga cikin iyayen ɗaliban da aka sace,...
“Cikin hukuncin Allah, sojojin Daularmu sun kama ‘Kwamandan Runduna’… bayan ya gudu daga harin kwantan-ɓauna… Bayan mun yi masa tambayoyi, Mujahidai suka kashe shi.” An kuma wallafa wani hoto a kafafen sada zumunta da ya nuna Janar Uba a ɗaure. Har yanzu rundunar sojin Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa game da wannan lamari ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ’Yansanda Sun Tura Tawaga Don Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Kebbi November 18, 2025 Manyan Labarai Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai November 17, 2025 Manyan Labarai Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC November 17, 2025
Ministan tsaron Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya kai ziyarar aiki a Hadaddiyar Daular Larabawa don inganta dangantakar soja da kuma huldar tsaro a yankin. Nasirzadeh ya jagoranci wata babbar tawaga, wadda ta isa Dubai a ranar Litinin bisa gayyatar takwaransa na Hadaddiyar Daular Larabawa. Ministan tsaron Iran yana shirin yin tattaunawa da jami’an Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma halartar taron Dubai Airshow na 2025, wanda aka shirya gudanarwa a tsakanin 17-21 ga Nuwamba. Ziyarar ta zo ne a karkashin tsarin diflomasiyyar tsaron Iran kuma tana da nufin inganta huldar yanki da kuma gano damar yin hadin gwiwa a fannoni daban-daban. A lokacin rangadin baje kolin, an shirya cewa ministan tsaron na Iran zai yi tarurruka da jami’an tsaro daga...
Gwamna Ahmed Idris na Jihar Kebbi ya ba da tabbacin cewa jami’an tsaro za su ƙwato ’yan matan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kwalejin ’Yan Mata ta GGCSS Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasu ta jihar cikin ƙoshin lafiya. Gwamnan ya bayar da tabbacin ne a yayin ganawarsa da iyayen ɗaliban kaɗan bayan harin ’yan bindigar a ranar Litinin. Aminiya ta ruwaito cewar da asubahin ranar ’yan bindiga suka kusta cikin harabar makarantar kwana ta ’yan mata ta GGCSS Maga, suka kwashe ɗalibai 25 daga ɗakin kwanansu zuwa cikin jeji. Maharan da suka riƙa harbi a iska kafin su shiga harabar makarantar sun bindige Matakin Shugaban Makarantar, Malam Hassan Yakubu Makuku, wanda ya yi ƙoƙarin...
Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi kakkausar suka kan sabon harin da ’yan bindiga suka kai makarantar sakandare ta ’yan mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi, wanda ya kai ga sace ɗalibai mata sama da 25 tare da halaka mai gadi da mataimakin shugaban makarantar. A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, Amnesty ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici da kuma nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa ballantana kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga. CAF ta fitar da ’yan wasa uku da suka rage a takarar gwarzon Afirka na bana Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas Ƙungiyar ta ce bincikenta ya gano...
Hukumar ƙwallon ƙafar Afirka CAF, ta bayyana cewa bayan tankade da rairaya da ta yi, a yanzu ’yan wasa uku kacal ne suka rage a takarar gwarzon nahiyyar na bana. A wata sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana Achraf Hakimi da Mohamed Salah da Victor Osimhen, a matsayin sauran ukun da suka rage a takarar gwarzon dan ƙwallon ƙafar Afirka na bana. Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno Hakimi, kyaftin din Morocco, ya lashe kofuna daga ciki har da Champions League a PSG — na farko a tarihin ƙungiyar — da Ligue 1, da European Super Cup, da kuma kai wa zagayen ƙarshe...
Gobara ta laƙume rayukan wasu yara biyu ’yan gida ɗaya a unguwar Rumuola da ke ƙaramar hukumar Obio/Akpor a Jihar Ribas. Bayanai sun ce ibtila’in ya auku ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Lahadi, lokacin da gobarar ta tashi a ɗaya daga cikin wasu ɗakunan haya da mahaifiyar yaran ta kulle ’ya’yanta huɗu ta tafi sayen kayan girki. Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno ’Yan sanda sun kama ƙunshi 66 na Tabar Wiwi a Gombe A cewar mazauna yankin, cikin yaran huɗun, biyun da suka riga suka kwanta barci sun ƙone su kurmus, yayin da sauran biyun da ke farke suka samu damar tserewa. Aminiya ta ruwaito cewa, mazauna yankin da sun ankara da gobarar...
An samu wannan raguwar ne sakamakon sauye-sauyen da aka samu a shekarar da muke ciki. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga November 17, 2025 Labarai Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi November 17, 2025 Labarai MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda Ta Ƙaƙabawa Takunkumi November 17, 2025
Ya bayyana cewa, zaman bitar ya yi daidai da umarnin Sufeto Janar na ‘Yansanda, IGP Kayode Egbetokun, musamman kan karfafawa jami’an rundunar. Don haka, CP Bakori ya umurci Kwamandojin da su zurfafa wayar da kan jama’a a yankunan karkara da birane domin sanar da su irin rawar da suke takawa wajen wanzar da zaman lafiya da daƙile ayyukan ‘yan ta’adda. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi November 17, 2025 Labarai MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda Ta Ƙaƙabawa Takunkumi November 17, 2025 Manyan Labarai Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai November 17, 2025
Mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya bayyana cewa: Iran tana da kyakkyawar alaƙa ta musamman da kuma al’adu da membobin ƙungiyar haɗin gwiwa ta Shanghai Mataimakin Shugaban Kasa na Farko na Iran ya ce, “Iran tana da alaƙar haɗin gwiwa na musamman da al’adu da dukkan ƙasashe membobin Ƙungiyar Haɗin Kan Shanghai (SCO), kuma abin farin ciki, ƙasar Iran ta shiga ƙungiyar SCO a hukumance cikin shekaru biyu da suka gabata.” Da yake jawabi a Filin Jirgin Sama na Mehr-abad kafin ya tashi zuwa Rasha don halartar taron kolin kungiyar Shaanghai ta SCO, Mataimakin Shugaban Kasa na Farko Mohammad Reza Aref ya ce, “Ƙungiyar SCO ƙungiya ce mai tasowa amma mai ƙarfi da cikakken iko. Jimillar yawan al’ummar ƙasashe...
Na’ini: Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Da Kansa Ya Jagoranci Yaki Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran
Jagoram juyin juya halin Musulunci da kan sa ya jagoranci yaki da harkokin al’umma a lokacin yakin wuce gona da iri na karshe kan Iran Kakakin Rundunar Tsaron kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC), Brigadier Janar Ali Mohammad Na’ini, ya tabbatar da cewa: Maƙiya ‘yan sahayoniyya ba su da yanayin sabon yaƙi, kuma abin da ake gabatarwa a yau shine yaƙin tunani da yaƙin da aka saba gani. A wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr, Brigadier Janar Na’ini ya ba da labarin lokutan shaƙatawa da ba zato ba tsammani na barkewar yaƙin da kuma shahadar wasu manyan kwamandojin soja na ƙasar. Ya kuma lura da yadda aka sake gina sansanin umarni a cikin ɗan gajeren lokaci da kuma...
Ya kuma yi Allah wadai da kisan wani jigo na Jam’iyyar APC, Umar Moriki, da kuma sace-sacen jama’a da aka yi a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, inda aka sace iyalai baki daya, ciki har da mata da yara. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda Ta Ƙaƙabawa Takunkumi November 17, 2025 Manyan Labarai Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai November 17, 2025 Manyan Labarai Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC November 17, 2025
An sanya hannu kan yarjejeniyoyin cinikayya na biliyoyin kudi, a yayin baje kolin hajojin fasahohin zamani na kasar Sin ko CHTF, wanda aka kammala a jiya Lahadi a birnin Shenzhen dake kudancin kasar Sin. Wannan ne karo na 27 da aka gudanar da baje kolin na CHTF, inda aka kai ga daddale huldodin cinikayya da ayyukan zuba jari 1,023, wadanda darajarsu ta haura kudin Sin yuan biliyan 170, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 24. Baje kolin na wannan karo ya gudana ne bisa taken “Fasahohi masu jagorantar ci gaba da dunkulewar masana’antu”. Kazalika, taron na yini uku ya hallara kamfanoni da hukumomi sama da 5,000 daga kasashe da yankuna sama da 100, ya kuma samu halartar baki sama da 450,000. Yayin...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai November 17, 2025 Manyan Labarai Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC November 17, 2025 Kasashen Ketare An Yanke Wa Tsohuwar Shugabar Bangladesh Hukuncin Kisa November 17, 2025
Shugaba Bola Tinubu a ranar Litinin ya gargadi jami’an shari’a a fadin kasar cewa dole ne a tabbatar da adalci ga kowa – Talaka da mai kudi, ba tare da nuna wata wariya ba, ko karɓar cin hanci, “bai dace adalci ya zama na sayarwa ba.” Da yake jawabi a yayin bude taron alkalan Nijeriya na kotunan koli na shekarar 2025 a Abuja, Tinubu ya jaddada cewa jami’an shari’a su ne ainihin masu kula da adalci, don haka, shugaban ya tabbatar da goyon bayansa kan samar da walwala, horo, da inganta Cibiyar Shari’a ta Kasa. ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC November 17, 2025 Manyan...
Hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce hauhawar farashin kayyayaki a ƙasar ya ragu zuwa kashi 16.05 cikin 100 a watan Oktoban 2025. Cikin rahoton wata wata da hukumar ke fitarwa, ta ce hauhawar farashin ya ragu ne da kashi 1.97 idan aka kwatanta da kashi 18.02 da aka samu a watan Satumba. ’Yan Majalisar Dokokin Taraba 16 sun sauya sheka daga PDP zuwa APC An ɗaura auren Sanata Kawu Sumaila da wata jami’ar soji a Kano A watanin baya-bayan an riƙa samun raguwar hauhawar farashin kayyaki a ƙasar. Aminiya ta ruwaito cewa, tun dai daga watan Yunin bana, hauhawar farashin kayayyaki ke ci gaba da sauka a ƙasar har kawo yanzu. Ana iya tuna cewa, tun watanni kadan da...
Bonzena ya ƙara da cewa duk da cewa kafin yanzu APC ce ke da rashin rinjaye a majalisar, an ci gaba da aiki cikin zaman lafiya, amma yanzu yana farin cikin ganin cewa dukkan mambobin majalisar sun haɗe ƙarƙashin tsari daya da ya yi daidai da hangen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi November 17, 2025 Manyan Labarai Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka November 17, 2025 Manyan Labarai Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda November 17, 2025