Malasiya Ta Bukaci A Kori Isara’ila (HKI) Daga MDD
Published: 29th, August 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Malasiya Muhammad Hassan ya sake nanata bukatar a kori HKI daga MDD saboda kissan kare dangin da take yi a zirin gaza.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar ya nakalto Muhammad Hassan yana fadar haka a yau Jumma’a ya kuma kara da cewa, kasashen masu rauni a duniya sun damu da yadda manya-,manyan kasashen duniya suka kyale HKI take yin abinda taga dama a kasar Falasdinu da ta mamaye.
Labarin ya kara da cewa HKI a cikin shekaru kimani biyu da suka gabata, sun kashe falasdinawa fiye da dubu 62, amma MDD da kuma sauran kasashen yamma sun hana hatta shigar abinci a cikin zirin gaza. Alhali a gaban idommu yara kanana suna mutuwa saboda yunwa.
Ministan ya kammala da cewa, idan MDD ta kasa yin wani abut oi daddaikun kasashen duniya su dora-mata takunkuman tattalin arziki su kaurace mata, har sai hakan yayi tasiri a cikin mummunan ayyukan da take aikatawa a gaza.
Hassan yace kasar Malasiya zata gabatar da wannan batun a jawabinda zata gabatar a babban taron manya-manyan kasashen duniya a cikin watan satumba mai zuwa.
Banda kasar Malasiya wasu kasashe kamar Afirka ta kudu da kuma sauran kasashe masu tasowa sun bukaci a kauracewa HKI kan wannan kissan kiayashin da ta ke yi a gaza.
Jamia’a mai tattara rahotanni dangane da yaki a gaza, Francesca Albanese ta bayyana kissan kare dangin da HKI take aikatawa a gaza, a matsayin irinsa mafi muni a wannan zamanin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran: Kasar China Ta Zuba Jari A Aikin Samar Da Wutan Lantarki Daga Rana A Bushar August 29, 2025 MDD Ta Yi Tir Da Dirar Mikiyan Da Jamus Takewa Masu Goyon Bayan Falasdinawa August 29, 2025 Majalisar dokokin Iran ta gabatar da kudirin ficewa daga NPT August 29, 2025 Guterres: Dole ne a kawo karshen halin da ake ciki a Gaza August 29, 2025 Pezeshkian: Alakar Iran, China Na Da Amfani Mai Yawa Ga Kasashen Biyu August 29, 2025 Araqchi: Matakin Gungun Kasashen Turai Kan Iran Lamari Ne Da Zai Dagula Al’amura August 29, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Mayar Da Martani Kan Kudurin Tawagar Turai August 29, 2025 Yemen Da Jaddada Yiwuwar Daukan Dogon Lokaci Dakarunta Suna Arangama Da Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya August 29, 2025 Guterres: Shirin Gwamantin Mamayar Isra’ila Kan Gaza Wani Babban Hatsari Ne August 29, 2025 Aragchi: Iran Zata Maida Martani Ga Kasashen Turai Dangane Da “SnapBack” August 28, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar
Shugaban Lebanon Joseph Aoun ya yi Allah wadai da keta hurumin kasarsa da Isra’ila ke yi a kudancin kasar, yana mai kira da a dauki tsauraran matakai kan duk wani kutse da sojojin mamaye za su yi a nan gaba a cikin Lebanon.
A lokacin wata ganawa da Kwamandan Rundunar Soja Rodolphe Heikal, Shugaba Aoun ya bayyana cewa dole ne Lebanon ta “fuskanci duk wani kutse da Isra’ila ta yi wa yankunan kudancin da aka ‘yantar don kare filayenmu da kuma tsaron ‘yan kasa.”
Wannan jawabi ya zo ne bayan harin da Isra’ila ta kai wa gundumar Blida, inda sojojin Isra’ila suka kashe wani ma’aikacin gundumar a lokacin wani hari da suka kai kan ginin ofishin karamar hukuma.
Daga baya, karamar hukumar ta tabbatar da cewa Ibrahim Salameh, wanda ya kwana a cikin ginin, ya yi shahada bayan da sojojin mamaya suka harbe shi. Aoun ya yi Allah wadai da kisan, yana mai cewa wani bangare ne na ayyukan “Isra’ila” kan fararen hula kuma ya zo ne ‘yan sa’o’i bayan taron da kwamitin da ke sa ido kan yarjejeniyar dakatar da fadan ya gudanar.
0Please leave a feedback on thisxShare
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci