Iran Ta Sami Lambobin Yabo 8 A Wasan Taekwondo Na Duniya
Published: 23rd, April 2025 GMT
Kungiyar da take wakiltar Iran a wasannin Taekwondo na duniya a kasar Sin, ta sami lambobin yabo 8 a ranar farko da bude gasar ta kasa da kasa.
An fara wasannin na Tikondu a garin Tayan dake kasar China wanda shi ne karo na 7 da kuma ‘yan wasa 491 daga duniya suke gasa.
Daga cikin lambobin yabon din da tawagar ta Iran ta lashe da akwai gwala-gwalai 4, azurfa 3 da kuma tagulla.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Za Ta Aiwatar Da Matakan Daidaita Samar Da Guraben Ayyukan Yi Da Raya Tattalin Arziki
Kazalika, domin daidaita ci gaban cinikayyar waje, manufofin da za a aiwatar sun hada da na tallafawa kamfanonin dake fitar da hajoji, ta yadda za su rage hadurra daka iya aukuwa, da fadada fitar da hidimomin da ake samarwa ga karin sassan duniya, da karfafa gwiwar kamfanonin waje, ta yadda za su kara zuba jarinsu a kasar ta Sin.
Daga nan sai jami’in ya bayyana cewa, Sin na da isassun manufofi da tsare-tsare, da za su wanzar da burinta na raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma a shekarar nan ta bana. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp