Aminiya:
2025-08-01@01:53:24 GMT

’Yan bindiga sun mamaye garuruwa 64 a Filato — Gwamna Mutfwang

Published: 9th, April 2025 GMT

Gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana damuwa kan yadda matsalar tsaro ta ƙara ƙamari, yana mai cewa a halin yanzu ’yan bindiga sun mamaye aƙalla garuruwa 64 na Jihar Filato.

A wata hirarsa da gidan talabijin na Channels a yau Laraba, Gwamna Mutfwang ya ɗora alhakin matsalar tsaron da ake fuskanta a jiharsa kacokam a kan ta’addancin ’yan bindiga da ke ƙara ta’azzara.

Ibas ya naɗa kantomomin ƙananan hukumomin Ribas ’Yan bindiga sun kashe masunta 3 a Sakkwato

Gwamnan ya yi zargin cewa akwai masu ɗaukar nauyin hare-haren da ke aukuwa a jiharsa.

“A haƙiƙanin gaskiya babu wani bayani da zan yi face cewa akwai masu ɗaukar nauyin ta’addancin nan,” a cewar gwamnan.

“Abin tambayar shi ne, su wa ke ɗaukar nauyin ta’addancin? Wannan shi ne abin da hukumomin tsaro za su yi ƙoƙari su gano.

“Mun zo gaɓar da za a gano masu hannu a wannan lamari domin dole akwai masu ɗaukar nauyin waɗannan hare-haren.

“Waɗannan garuruwa da a bayan nan aka kai wa hari suna cikin yankunan da suka fuskanci hare-hare a 2023 amma suka sake gina alaƙaryar da kansu.

“Misali, a shekarar 2023 an kai wa ƙauyen Ruwi hari har aka kashe mutane 17, amma suka sake farfaɗowa suka gina matsugunninsu.

“Idan an ɗauki kusan shekaru 10 ana wannan hare-hare, shi yake nuna cewa akwai wasu da ke shirya wannan ta’addanci da gayya domin kawar da mutane daga doron ƙasa.

“A halin yanzu akwai aƙalla garuruwa 64 da ’yan bindiga suka mamaye a tsakanin ƙananan hukumomin Bokkos, Barkin Ladi, da Riyom na Jihar Filato.

“’Yan bindiga sun ƙwace iko waɗannan wurare sun sauya musu suna kuma mutane sun ci gaba da rayuwa a cikinsu.

“Sai dai ina fatan cewa nan da wani lokaci kaɗan hukumomin tsaro za su haɗa gwiwa domin kawo ƙarshen wannan matsalar.

Aminiya ta ruwaito cewa a makon jiya ne Gwamna Mutfwang ya yi iƙirarin cewa matsalar tsaron da ke addabar jihar ta wuce iya rikicin makiyaya da manoma.

“Dole ne na nanata cewa manufar waɗannan maƙiya ita ce tayar da hargitsi da hana zaman lafiya a jihar nan.

“Sai dai ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba har sai mun tabbatar da cewa burinsu bai cika ba.

“Masu tunanin cewa rikicin makiyaya da manoma ne ka haddasa matsalar tsaro su daina wannan tunani domin kuwa wasu ne ke sojan gona da zummar hana zaman lafiya a jihar.

“Ina mai tabbatar wa mutanen Filato cewa da izinin Allah za mu yi nasara a kansu kuma mun kusa ganin ƙarshen waɗannan maƙiya,” a cewar gwamnan.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Caleb Muftwang hare hare Jihar Filato ɗaukar nauyin matsalar tsaro

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina

’Yan bindiga sun tarwatsa kauyaku sama da 10 da ke zagaye da ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina.

Maharan dai sun rika kashe mazauna kauyukan sannan su sace wasu su yi garkuwa da su domin karɓan kuɗin fansa.

Bayanai na cewa a ’yan kwanakin nan, ’yan bindigar na cin karensu babu babbaka a inda suka tarwatsa kauyuka kamar su Guga da Kandarawa da Kakumi da kuma Monono.

Gwamnatin Tinubu ta mayar da Arewa saniyar ware – ACF DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure

Har ila yau lamarin ya shafi ƙauyukan anguwar ’Yar Dabaru da anguwar Ɗan Marka, da Sabon Gida da ƙauyan Doma da dai sauran su.

Hakan dai ya haifar da kauracewa ƙauyukan ga mazaunansu da suke da sauran numfashi inda a yanzu haka ake da ’yan gudun hijira sama da 3,500 da ke neman mafaka a cikin garin Bakori.

Kazalika, rahotanni sun kuma ce akwai wasu sama da 2,500 da ke garin Guga don neman mafaka.

’Yan gudun hijirar wadanda akasarinsu mata ne da ƙananan yara sun watsu a wurare daban daban.

Aminiya ta zagaya unguwan Kafaɗi da unguwar Ma’aru da ke Sabuwar Abuja a cikin garin na Bakori, inda wakilinmu ya tarar da cincirindon mata da ƙananan yara a rakuɓe, a gidajen ’yan uwa, wasu kuma a makarantun firamaren gwamnati da ke karamar hukumar ta Bakori.

A tattaunawar Wakilinmu da wasu daga cikin ’yan gudun hijira wadanda suka fito daga kauyaku daban-daban na jihar, sun nuna alhininsu game da yadda ’yan bindigar ke cin karensu ba babbaka a yankin.

Imrana Shafi’u wanda ’yan bindigar suka harbe shi a ƙafa har wuri biyu, wanda shi ya yi hijira ne daga kauyan Ɗan Marka, ya ce lamarin na da ban tsoro matuƙa.

A cewarsa, “Ni ma Allah ne ya sa zan rayu domin ’yan bindigan sun zaci na mutu ne.

“Domin da suka zo kanmu harbin kan mai uwa da wabi, suka yi ta yi, inda suka kashe mutane da dama.

“Ni ma dai Allah ne ya tsirar dani, domin duk wadanda nake tare da su duk an kashe su, ni kadai na tsira cikin ikon Allah,” in ji shi.

Ita kuwa Malama Marawiya wacce ta yi gudun hijira daga kauyan ’Yar Dabaru ta ce da rana tsaka ’yan bindiga suka keto cikin kauyan nasu, suka tarwatsasu sa’ilin da suka tasa ƙeyar mata sama da 10 kuma duk yawancinsu suna ɗauke da goyo suka yi cikin daji da su.

Marawiya ta kara da cewa kusan kwanakin matan 10 ke nan a hannun su kuma sun ce sai an biya kudin fansa har Naira miliyan daya da rabi kan kowanne mutum daya kafin a sake su.

Ta Kara da cewa “A da in suka dauki mutum bai wuce su ce a ba su Naira dubu ɗari biyar ba amma a wannan karon sai suka ce sai an biya har sama da naira miliyan daya da rabi ga kowanne mutum,” in ji ta.

Yusuf Usman, wanda suka yi sansani a wata makarantar Firamare ta Nadabo da ke cikin garin Bakori, ya ce kusan su ɗari uku ne suka yi gudun hijira daga kauyan Doma, cikinsu har da tsofaffi.

Ya kuma ce, “A haka muka tako da ƙafa muka yini muna tafiya tare da mata da yaran kanana har Allah ya kawo mu garin Bakori,” in ji shi.

Ya kara da cewa kusan shekara biyar kenan suna fama da wannan matsalar ta tsaro, kuma ba dare ba rana bare damina ko rani, haka ake shigowa kauyakun su ana kashe su sannan kuma a tasa ƙeyar su a tafi da su daji domin karɓan kuɗin fansa.

Shugaban kwamitin da ƙaramar hukumar Bakori ta kafa domin kula da ’yan gudun hijirar, Mallam Mamman Yaro Bakori, ya ce adadin ’yan gudun hijirar sun kai 3,500 a garin Bakori.

Ya Kara da cewa a garin Guga Kuma akwai akalla kimanin mutane 2,500 da suke gudun hijira a can.

Shugaban ya ce kuma kusan a kullum yawan su ƙaruwa yake yi, sannan suna warwatse ne a wurare daban daban a inda wasu suke zaune a gidajen ‘yan uwansu wasu kuma suna zaune ne a makarantar firamare ta Nadabo a cikin garin Bakori.

Sai dai ya ce tuni Shugaban ƙaramar hukumar Bakori, Abubakar Barde ya bayar da umurnin kai masu tallafin kayan abinci sau uku a rana tare da kudin cefane don saukaka masu rayuwar da suke ciki.

Wasu na bayyana cewa a ‘yan kwanakinnan ’yan bindigar na cin karensu babu babbaka a inda suka kafa sansaninsu a dajin Guga da Kandarawa da Kakumi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ZAMFARA: APC Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Kawo Dauki Don Matsalar Tsaro Na Kara Tsananta
  • Hare-hare: ’Yan bindiga sun raba mutum 5,000 da muhallansu a Katsina
  • Sojojin Yemen Sun Kai Zafafan Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Guda Uku  
  • ’Yansanda Sun Ceto Mutane 28 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Katsina
  • Yadda ’yan bindiga suka tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina
  • ’Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina
  • Babu Wata Karamar Hukumar Da Ke Ƙarƙashin Ikon Ƴan Ta’adda A Filato -Gwamna Mutfwang
  • Babu Wata Karamar Hukumar Dake Ƙarƙashin Ikon Ƴan Ta’adda A Filato -Gwamna Mutfwang
  • Jami’an Tsaron Katsina Sama Da 100 Sun Rasu A Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda – Gwamnati
  • ’Yan sa-kai aƙalla 100 da jami’an tsaro 30 sun mutu a bakin aiki a Katsina —Gwamnati