Dakarun Yemen Sun kai hari kan jirgin ruwan yaki na Amurka USS Harry Truman da makamai masu linzami
Published: 3rd, April 2025 GMT
Dakarun Yaman sun sanar da mayar da martani kan harin baya-bayan nan da Amurka ta kai kan kasarsu, wanda ya hada da hare-hare ta sama har sau 36 a yankuna da dama a cikin gundumomin Sanaa, Sa’ada, da wasu jahohin kasar, wanda ya yi sanadin mutuwa da jikkatar mutane da dama.
Kakakin Rundunar sojin Yaman Birgediya Janar Yahya Saree ya tabbatar da cewa, sojojin Yaman sun gudanar da wani shiri na soji na hadin gwiwa, inda suka yi arangama da jirgin ruwan Amurka Harry Truman da jiragen yakin da yake dauke da su a arewacin tekun Bahar Maliya.
Saree ya ci gaba da cewa, a harin an yi amfani da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuka, kuma harin ya cimma nasara kamar yadda aka tsara, inda ya ce an dauki tsawon sa’o’i da dama ana gudanar da farmakin, kamar yadda kuma a lokaci guda sojojin Yeman sun dakile wani bangare na harin Amurka.
Ya kuma kara tabbatar da cewa dakarun na Yemen za su ci gaba da kai hare-hare kan dukkanin jiragen ruwan yakin Amurka da kuma jiragen da suka keta dokar hana shiga yankunan da aka ayyana, yana mai bayyana cewa wadannan hare-haren wuce gona da iri na Amurka ba za su hana su cika alkawarin da suka dauka na tallafawa al’ummar Palasdinu ba.
Saree ya tabbatar da cewa sojojin Yeman na ci gaba da gudanar da ayyukansu a cikin Haramtacciyar Kasar Isra’ila, kuma ba za su gushe ba har sai an dakatar da kai farmaki a kan Gaza tare da kawo karshen killacewar da ake yi wa al’ummar yankin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikatar Sharia A Nan Iran Zata Bayyana Abinda ya farsu A Tashar Jiragen Ruwa Na Shahid Rajae
Kakakin ma’aikatar sharia a nan JMI ya bada sanarwan cewa,ma’aikatar za ta bayyanawa mutanen sakamakon bincken da suka gudanar kuma suke ci gaba da yi, dangane da fashewa da kuma gobatar da ta tashi a tashar jiragen ruwa ta Shahid Rajaee a cikin yan kwanakin da suka gabata. .
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran, ya bayyana cewa, Asgar Jahangir kakakin ma’aikatar sharia da kuma Zabihullah Khudayiyan shugaban hukumar bincike ta kasa, sun gudanar da taron hadin guiwa da yan jaridu da kafafen yada labarai na cikin gida da waje a safiyar, dangane da fashewa da kuma gobarar da ta biyo baya a tashar jiragen ruwa na Shahid Rajaee.
Banda haka jami’an sun amsa tambayoyin yan jarida bayan jawabansu dangane da hatsarin wanda ya lakume rayukan mutane, fiye da 70 da kuma jikata wasu kimani dubu guda.
Kafin haka dai jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminaee ya bada umurni ga ma’aikatun biyu su gudanar da cikekken bincike don gani musabbabin wannan hatsarin sannan idan akwai wadanda suka da hannu, ko sakaci a cikinsa, a bi tsarin da ake da shi don hukunta wadanda suke da laifi.