Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu
Published: 26th, March 2025 GMT
Tsohon Mataimaki na Musamman kan Harkokin Rediyo ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu.
Ya rasu ne a ranar Laraba 26 ga watan Maris, 2025, bayan gajeriyar rashin lafiya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.
Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4 Ministan tsaro ya yi alƙawarin kawo sauyi a cibiyar horar da sojojiKakakin Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da rasuwar cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin ƙwararren ɗan jarida da ya taka rawar gani wajen inganta harkokin sadarwa a jihar.
Za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin yau Laraba a Filin Masallacin Galadanchi da ke kusa da gidan Galadiman Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya nuna alhininsa kan rasuwar Galadanci, tare da bayyana irin rawar da ya taka a gwamnatinsa.
“Rasuwar Abdullahi Tanka Galadanci babban rashi ne ga gwamnatina da Jihar Kano baki ɗaya.
“Za a yi rashinsa saboda jajircewarsa da ƙwazon da ya nuna wajen inganta harkokin sadarwarmu,” in ji gwamnan.
Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalansa, ’yan uwa da abokan arziƙi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamnan Kano rasuwa ta aziyya
এছাড়াও পড়ুন:
An Kwashe Duk Dabbobin Tsohon Akanta-Janar
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp