Araqchi: Har yanzu Iran ba ta mayar da amsa ga wasikar Trump kan tattaunawar nukiliya ba
Published: 26th, March 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya sanar da cewa har yanzu Iran ba ta mayar da martani kan wasikar da shugaban Amurka Donald Trump ya aike kan shirin nukiliyar Iran ba. Sai dai ya ce ana shirin mayar da amsa kuma za a mika ta hanyoyin da suka dace nan ba da jimawa ba.
Da yake magana a wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da ministan harkokin wajen Armeniya Ararat Mirzoyan a Yerevan, Araghchi ya nanata cewa Iran ba za ta shiga tattaunawa kai tsaye da Amurka ba a karkashin yanayin matsin lamba da barazanar soji, da kuma kakaba takunkumi.
Sai dai kuma ya tabbatar da cewa har yanzu ana ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai uku, tare da tabbatar da aniyar Iran ta fuskar diflomasiyya.
Wasikar wadda Trump ya sanar da aikewa da ita a ranar 7 ga Maris, an aike da ita ne zuwa ga jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Ayatullah Sayyed Ali Khamenei, a daidai lokacin da gwamnatin Amurka ke ci gaba da aiwatar da matakai na matsin lamba a kan Iran, a daya bangaren kuma take nuna sha’awar yin shawarwari tare da kasar ta Iran.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran Esmaeil Baqaei ya fayyace cewa Tehran ba ta da wani shiri na bayyana wasikar a bainar jama’a, yana mai cewa ba lallai bane jita-jitar da kafafen yada labarai suka yada a game da wasikar ya zama gaskiya.
Za a yi martanin ne game da wannan wasiku ta hanyoyin diflomasiyya bayan yin cikakken nazari a kai, in ji shi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Da Rasha Sun Jaddada Yin Aiki Tare A Fagen Kiwon Lafiya
Ministan kiwon lafiya na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Ridha Zafarqandi ya tattauna hanyoyin bunkasa aiki tare a fagen kiwon lafiya da mataimakin ministan kiwon lafiya na tarayyar kasar Rasha.
Ministan na Iran dai ya yi wannan trattaunar ne a jiya Lahadi inda su ka tabo fagage da dama da su ka yi tarayya akansu a cikin harkar kiwon lafiya.
Ministan na Iran ya kuma ce, a baya kasashen biyu sun cimma yarjejeniya wacce a wannan lokacin ake son bunkasa ta.
Muhammmad Ridha Ya kuma bayyana yadda kasashen biyu suke da kayan aiki masu yawa a fagagen magance cutuka masu yaduwa da wdanda ba su yaduwa haka nan kuma fagen yin magunguna.
Shi kuwa mataimakin ministan kiwon lafiyar na tarayyar Rasha Olog Silgy ya tabbatar da cewa,kasarsa a shirye take ta bunkasa aiki da jamhuriyar musulunci ta Iran a fagen musayar dalibai da kuma nazarce-nazarce da bincike na ilimin likitanci.
Kasashen biyu sun kafa kwamitin hadin gwiwa na yin fada da cutuka masu yaduwa da zai taka rawa mai girma wajen magance cutuka.