Sin Za Ta Kara Ingiza Samar Da Kudaden Gudanar Da Kamfanoni Masu Zaman Kansu
Published: 6th, March 2025 GMT
Shugaban hukuma mai lura da hada hadar samar da kudade ta kasar Sin Li Yunze, ya ce kasar za ta kara azamar samar da kudaden gudanar da kamfanoni masu zaman kan su, da kanana da mafiya kankantar sana’o’i.
Li, wanda ya yi tsokacin a Larabar nan, a gefen taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin dake gudana yanzu haka, ya ce Sin za ta kara yawan lamuni da ake baiwa sassa masu zaman kan su, da rage tsadar samar da kudaden sana’o’i, ta yadda hakan zai haifar da karin alfanu ga kamfanoni.
Jami’in ya kara da cewa, kamfanoni masu zaman kan su ne ke da kaso 92 bisa dari na jimillar kamfanonin dake kasar Sin, kuma akwai tarin hanayen jari a mafiya kankantar sana’o’i, da kananan kamfanonin dake kasar. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5
Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya taron manema labarai a yau 17 ga wata, inda aka bayyana cewa, tun daga fara aiwatar da shiri na 14 na shekaru 5 na raya kasa, wato daga shekarar 2021 zuwa ta 2025, karfin kamfanoni mallakar gwamnati ya kara karuwa, kuma jimillar kadarorinsu ta wuce yuan tiriliyan 90, kwatankwacin sama da dalar Amurka tiriliyan 12.6.
Darektan kwamitin sa ido kan kadarori mallakar gwamnati na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, Zhang Yuzhuo ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2021 har zuwa yanzu, jimillar kadarorin kamfanoni mallakar gwamnati ta karu daga kasa da yuan tiriliyan 70, kwatankwacin dalar Amurka kimanin tiriliyan 10, zuwa sama da yuan tiriliyan 90, kwatankwacin sama da dalar Amurka tiriliyan 12.6, yayin da jimillar ribar da suka samu ta karu daga yuan tiriliyan 1.9, kwatankwacin sama da dalar Amurka biliyan 267, zuwa yuan tiriliyan 2.6, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 365. Matsakaicin karuwar jimlolin biyu a kowace shekara kuwa ya kai kashi 7.3 cikin dari da kashi 8.3 cikin dari bi da bi.
Bugu da kari, tun daga aka fara aiwatar da shirin, kamfanoni mallakar gwamnati sun biya kudin harajin da yawansu ya zarce yuan tiriliyan 10, kwatankwacin fiye da dalar Amurka triliyan 1.4, kuma darajar yawan hannun jarin da suka mikawa asusun inshorar zaman al’umma ta kai yuan tiriliyan 1.2, kwatankwacin fiye da dalar Amurka biliyan 168.(Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp