’Yan sanda sun ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi a Gombe
Published: 5th, March 2025 GMT
’Yan sanda sun ceto wani mutum mai shekaru 48, Alhaji Samaila Muhammed, da aka yi garkuwa da shi a ƙauyen Lano da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba ta Jihar Gombe.
An gudanar da aikin ceton bisa tsari tare da haɗin gwiwar ‘yan banga na yankin, lamarin da ya tabbatar da cewa mutumin ya shaƙi iskar ’yanci salin-alin.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, mahukunta sun tabbatar da ƙoshin lafiyarsa sannan daga bisani aka sada shi da ’yan uwansa.
Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya fitar, ya tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
DSP Buhari ya tabbatar wa jama’a cewa za a ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ayyukan laifi a jihar.
Sanarwar ta kuma gode wa jama’a bisa haɗin kansu tare da yin kira da su kasance masu sa ido, su kuma riƙa sanar da hukuma game da duk wani abu da suka ga ya dace ko ya saɓa da al’ada a cikin al’umma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda garkuwa da mutane jihar Gombe
এছাড়াও পড়ুন:
An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe
Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Najeriya (NUT) reshen Jihar Gombe, ta ziyarci shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi na jihar, Barista Sani Ahmad Haruna, a ofishinsa da ke Gombe.
Shugaban ƙungiyar, wanda shi ne shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, ya bayyana cewa gwamnati da shugabannin ƙananan hukumomi za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen inganta walwalar malamai.
Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyiYa ce: “Ba za mu taɓa barin malamai su shiga cikin matsanancin hali ba. Za mu duba matsalolinsu domin tabbatar da walwalarsu da ci gaban ilimi a jihar.”
Sani, ya kuma yaba da yadda NUT ke tattaunawa cikin lumana da kawo shawarwari maimakon ɗaukar matakan da za su iya kawo tsaiko ga harkar ilimi.
A nasa jawabin, shugaban NUT na jihar ya ce sun kai ziyarar ne domin tattauna matsalolin da malamai ke fuskanta, musamman na makarantun firamare da ƙananun sakandare da ke ƙarƙashin kulawar ƙananan hukumomi.
Ya ƙara da cewa manufar NUT ita ce samar da fahimtar juna da haɗin kai tsakaninsu da shugabannin ƙananan hukumomi domin gano hanyoyin magance matsaloli cikin lumana.