Gwamna Namadi Ya Bukaci Wadanda Suka Amfana Da Tallafin Mazabu Su Zama Masu Dogaro Da Kai
Published: 25th, February 2025 GMT
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin bayar da tallafi a mazabun jihar da su yi amfani da damar da suka samu domin dogaro da kai.
Ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da shirin da majalisar da ke wakiltar mazabar Kaugama ya yi.
Malam Umar Namadi wanda ya samu wakilcin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin, ya ce shirin samar da tallafin a mazabu zai kara inganta manufofi 12 na gwamnatin jihar wadanda suka hada da karfafawa al’umma don bunkasa zamantakewa da tattalin arziki a kowane mataki.
Ya yi fatan wannan karimcin zai yi kyakkyawan tasiri ga mutane 1,200 da suka ci gajiyar tallafin.
A jawabinsa, dan majalisa mai wakiltar mazabar Kaugama a majalisar dokokin jihar Jigawa, Alhaji Sani Sale Zaburan, ya yabawa gwamna Umar Namadi bisa dimbin ayyuka da shirye-shiryen da aka aiwatar a karamar hukumar Kaugama.
A cewarsa, an ware sama da naira miliyan 30 domin gudanar da shirin kuma wadanda suka ci gajiyar shirin sun hada da kananan ‘yan kasuwa, masu karamin karfi da dai sauransu.
A jawabin maraba shugaban karamar hukumar Kaugama Alhaji Usman Masaki Dansule ya yabawa bangaren zartaswa da na majalisa bisa yadda suka fara shirin ,wanda zai ci gaba da bunkasa tattalin arzikin al’umma da ke karkara.
Don haka Dansule ya bukaci wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da kudaden don inganta rayuwarsu.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa da suka ci gajiyar wadanda suka
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kammala Ziyarar Yini 3 A Ma’aikatar Kananan Hukumomin Jihar
Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya bukaci ma’aikatar kananan hukumomi da ta karfafa matakan yiwa kananan hukumomin jihar 27 jagoranci akan sha’anin mulki da harkokin kudi domin inganta ayyukan su.
Shugaban Kwamatin, Alhaji Aminu Zakari ya yi wannan kiran a karshen ziyarar kwanaki 3 da kwamatin ya yi a ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar a Dutse.
Alhaji Aminu Zakari wanda shi ne wakilin mazabar Gwiwa a majalisar dokokin jihar Jigawa, ya ce ziyarar kwamatin na da nufin tantance yadda ma’aikatar ta ke gudanar da ayyukan ta, ta fuskar harkokin mulki da na kudi da kuma dangantakar aiki tsakanin ta da kananan hukumomin jihar 27 kamar yadda tsarin mulki ya dorawa majalisa nauyi.
A nasa jawabin, mataimakin shugaban Kwamatin kuma wakilin mazabar Kaugama, Alhaji Sani Sale Zaburan ya bayyana bukatar ganin jami’an ma’aikatar da ke kula da kananan hukumomi a shiyya shiyya suna gudanar da ayyukan su ba tare da jingina da shugabannin kananan hukumomi ba a ko da yaushe amma Kuma su na yiwa kananan hukumomin jagoranci wajen gudanar da sha’anin mulki da harkokin Kudi kamar yadda ya kamata.
Daya daga cikin ‘yan kwamatin Malam Ibrahim Sabo Ahmad Roni ya duba kundin bayanan sha’anin mulki yayin da Oditoci su ka duba kundin bayanan harkokin Kudi tare da yabawa da kuma bada shawarwari da za su inganta ayyukan ma’aikatar.
Da ya ke mayar da jawabi, kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi Alhaji Ibrahim Garba Hannun Giwa wanda Babban Sakatare na maikatar ya wakilce shi, Alhaji Muhammad Yusha’u ya ce ma’aikatar ce ke uwa da makarbiya wajen yiwa kananan hukumomi jagoranci a sha’anin mulki da harkokin Kudi da zamantakewa domin kawo cigaba a yankunan karkara.
Kazalika, a daya bangaren kuma, karamin Kwamatin da Babban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar Dokokin jihar Jigawa ya kafa bisa jagorancin wakilin mazabar Kiyawa Alhaji Yahaya Muhammad Andaza domin duba aikin gyaran gidajen kananan hukumomin jihar 27 da ke kan titin Bypass a Dutse ya mika rahoton sa ga babban kwamatin.
Alhaji Yahaya Muhammad Andaza Wanda sakataren Kwamatin Alhaji Yusha’u Muhammad ya wakilta, ya ce karamin Kwamatin ya duba gidajen Inda ya dauki samfur din yanayin da su ke ciki.
Ya ce daga cikin gidajen akwai wadda ke funskatar matsaloli kamar na tsagewar bango da sanya darduma da kujeru da kayan amfani a dakin girki marasa inganci yayin da ba a mayar da na’urar sanyaya daki a wasu gidajen ba.
Yusha’u wanda shi ne mataimakin Akawun majalisar, ya lura cewa akwai rashin kyawun flasta a wasu gidajen yayin da kan dakin wasu ke yayyo sai Kuma rashin fankar sama da karayyayun kujeru da rashin hada wasu gidajen da wutar lantarki mai amfani da hasken rana da rashin kyawun kofofi da magudanin ruwa da ke kawo barazanar ambaliyar ruwa ga wasu gidajen.
A nasa jawabin, shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar Dokokin jihar Jigawa Alhaji Aminu Zakari ya ja hankalin shugabannin kananan hukumomin jihar da su dauki nauyin cikakkiyar kulawa ga gidajen bisa la’akari da dinbin kudaden da aka kashe wajen gyara gidajen.
Usman Mohammed Zaria