UNICEF Ya Jinjinawa Jihar Jigawa
Published: 21st, February 2025 GMT
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce zai ci gaba da tallafa wa jihar Jigawa wajen gina tsarin kiwon lafiya na al’umma.
Shugaban hukumar UNICEF a Najeriya, Dr. Shyam Sharan-Pathak ya bayyana haka a wajen bikin mika aikin ga gwamnatin jihar Jigawa na tsawon shekaru 3 na GAVI, a hukumance a Dutse babban birnin jihar.
A cewarsa, UNICEF za ta ci gaba da tallafa wa jihar don bunkasa muhimman ayyuka daga cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko na PHC, gami da ayyukan rigakafi na yau da kullun.
Dokta Shyam ya ci gaba da bayyana cewa, gagarumin ci gaban da aka samu ta hanyar shirin, shaida ce ta hadin gwiwa da jajircewa ga kowane yaro, matasa da uwa a jihar da ma fadin kasar nan.
Shugaban ma’aikatan ya yaba da gudunmawar sama da naira miliyan 879 a matsayin tallafin hadin gwiwa na shirin fahimtar juna da gwamnatin jihar Jigawa ta yi, wanda hakan ya sa gwamnatin jihar ta ware kashi 15.6% na kasafin jihar ga sashen kiwon lafiya.
Ya ce, UNICEF ta yaba da GAVI, kawancen rigakafin, saboda tallafin da suke bayarwa don haɓaka ayyukan PHC, don inganta ɗaukar rigakafin yau da kullun da kuma isar da ingantaccen shirin kula da lafiya.
A nasa jawabin, gwamna Umar Namadi ya yabawa hukumar UNICEF da abokan hulda, bisa goyon bayan da suka baiwa fannin kiwon lafiya a jihar a tsawon shekarun da suka gabata na aikin.
Namadi, ya yi nuni da cewa, gwamnatin ta fara aikin farfado da fannin lafiya a matakin farko a jihar.
USMAN MZ
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jugawa Lafiya jihar Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata Za Ta Fara Daukar Bayanai Ta Yanar Gizo
Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta sanar da cewa, a halin yanzu ana iya bayyana kadarorin ma’aikatan ta hanyar yanar gizo, wani mataki da aka tsara domin saukaka aikin da kuma kara yin lissafi.
Daraktan ofishin na jihar Jigawa Abubakar Bello ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Muhammad K. Dagaceri a ofishin sa.
Abubakar Bello ya jaddada cewa sabon shirin na da nufin rage dinbin aikin dake gaban ma’aiakata da kuma saukaka tantance kadarorin domin yaki da cin hanci da rashawa a cikin tsarin.
“Mun sauya dabara zuwa rajista ta yanar gizo don bayyana kadarorin, muna ba wa mutane damar kammala aikin daga gidajensu. Duk da haka, muna neman goyon bayan ku don tabbatar da cewa an sanar da jami’an gwamnati tare da karfafa gwiwar su bi wannan sabon tsari,” in ji shi.
Da yake mayar da jawabi, shugaban ma’aikata na jiha Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya yi alkawarin wayar da kan jami’an gwamnati cikin tsanaki game da muhimmancin bayyana kadarorin su, kamar yadda hukumar da’ar ma’aikata ta ba su umarni.
Ya tunatar da cewa rashin yin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasa ne.
Dagaceri ya bada tabbacin bada goyon baya da hadin kai domin cimma burin da ake so na wannan shiri.
USMAN MZ