Gwamnatin jihar Jigawa ta yi alkawarin ci gaba da gudanar da ayyukan kiwon lafiya da aka gudanar karkashin hadin gwiwarta da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), da shirin samar da rigakafin cututtuka a kasashe masu tasowa(GAVI) a cikin shekaru uku da suka gabata.

Haɗin gwiwar wanda aka fara shi da yarjejeniyar fahimtar juna da aka rattaba hannu a shekarar 2022, an yi shi ne don haɓaka tsarin bada lafiya na jihar, da inganta tsarin rigakafi ta hanyar samar da kayan aiki da wadatattun ma’aikatan lafiya.

A wajen mika kayan aikin da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, Gwamna Umar Namadi ya ce shirin ya bayar da gudunmawa musamman wajen samar da inshorar lafiya na musamman ga  mutane sama da dubu 143 a kananan hukumomi 27 na jihar.

Namadi wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Injiniya Aminu Usman, ya ce manufofin yarjejeniyar sun yi daidai da ajandar  gwamnatin jihar 12, wanda ya bai wa fannin lafiya fifiko ta hanyar sauya cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko tun daga tushe.

Mataimakin gwamnan wanda ya karbi tawagar UNICEF/GAVI karkashin jagorancin shugaban hukumar ta UNICEF a Najeriya, Dr Shyam Sharan-Pathak, ya ce gwamnatin za ta ci gaba da bullo da tsare-tsare don bunkasa harkar kiwon lafiya a fadin jihar.

Shi ma da yake jawabi, Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dr Muhammed Abdullahi Kainuwa, ya ce aikin ya samu gagarumar nasara a tsawon wannan lokaci.

Ya ce an samu ingantacciyar hanyar adana alluran rigakafin, ta hanyar sayen kayayyakin adana  sanyi na tafi da gidanka,  da na’urorin sarrafa hasken rana kai tsaye.

Hakazalika Dakta Kainuwa ya ce, an samar da  motoci 3 da suka rarraba kayayyakin aiki, sannan an dauki  mutane 330 aiki.

Ya yabawa shugabannin addini da na gargajiya a jihar, bisa goyon bayan da suka bayar wajen wayar da kan jama’a a tsawon shekaru 3 da aka yi aikin.

A nasa jawabin babban sakataren ma’aikatar lafiya ta jihar Dr Kabiru Ibrahim,  ya yabawa gwamna Namadi bisa jajircewarsa.

Dr Kabiru, ya lura cewa, kudurin gwamnatin na bin ka’idoji da manufofin ma’aikatar lafiya ta tarayya abin yabawa ne matuka.

Shi ma da yake nasa jawabin, babban sakataren hukumar kula da lafiya matakin farko na jihar, Dokta Shehu Sambo, ya ce yarjejeniyar ta jawo sabbin dokoki da suka shafi kiwon lafiya a jihar.

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, shirin karfafa tsarin kula da lafiya a matakin farko shiri ne na hadin gwiwa na tsawon shekaru 3 (wato daga shekarar2022 zuwa  watan Maris  na 2025) tsakanin GAVI da jihohi 8 na Najeriya wanda jihar  Jigawa na daga cikinsu.

 

Usman Muhammad Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa kiwon lafiya

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar 

Gwamnatin jihar ta ce, matakin na daya daga cikin kokarin gwamnati mai ci na inganta ayyukanta domin samar da romon dimokuraɗiyya ga al’ummar jihar Sokoto.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar 
  • Yadda ’yan Tifa da baƙin direbobi ke haddasa haɗari a Abuja
  • Hajj 2025: Kaduna Ta Gaddamar Da Ayarin Likitoci Da Za Su Kula Da Alhazan Jihar
  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Shirya Fara Tantance ‘Yan Fansho
  • Gwamna Namadi Ya Nada Aisha Mujaddadi Sabuwar Shugabar Hukumar InvestJigawa
  • Jihar Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Aikin Hajjin 2025
  • Hajjin 2025: An Fara Yi Wa Maniyyata Allurar Rigakafi A Jigawa
  • Hajjin 2025: Jihar Kwara Ta Fara Allurar Rigakafi Ga Maniyyata
  • Hajjin 2025: Gwamna Namadi Ya Nada Sarkin Kazaure Amirul Hajj
  • Iran Da Rasha Sun Jaddada Yin Aiki Tare A Fagen Kiwon Lafiya