A kokarinta na karfafa hadin gwiwa da tabbatar da gaskiya da rikon amana, hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Jigawa (JG-PCACC) ta kai ziyarar ban girma ga takwararta da ke Abuja.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulda da jama’a na JG-PCACC Alhaji Yusuf Suleiman ya bai wa gidan rediyon Najeriya a birnin Dutse na jihar Jigawa.

A cewarsa, sun kai  ziyarar ce karkashin jagorancin shugaban PCACC, Barista Salisu Abdu,  da zummar tantancewa da kuma cudanya da masu ruwa da tsaki a hukumar, tare da lalubo hanyoyin hadin gwiwa  tsakanin bangarorin biyu.

Barista Salisu Abdu ya jaddada mahimmancin hadin gwiwar t domin hana cin zarafi da rashin adalci a hukumomi da cibiyoyin gwamnati.

“Mun yi imanin cewa ta hanyar yin aiki tare, za mu iya samun ci gaba da samar da ingantacciyar al’umma.

“Ziyarar da muka kawo a yau wata shaida ce da ke nuna aniyarmu ta hada kai da kuma kawar da jihar Jigawa daga kowane irin zalunci.

Barista Abdu ya kuma shaida wa babban kwamishinan cewa hukumarsa na son yin amfani da kwarewar hukumar korafe-korafen jama’a ta fannin horar da ma’aikata.

“Muna da tabbacin hukumarku za ta iya taimaka mana da shawarwari,  da horarwa da goyon baya kan mafi kyawun ayyuka wajen tafiyar da koke-koken jama’a duba da nasarorin da kuka samu tsawon shekaru.” In ji Barr. Abdu.

Shugaban ya kuma bayyana cewa JG-PCACC na da ayyuka guda biyu da suka hada da sauraran korafe-korafen jama’a da kuma yaki da cin hanci da rashawa, inda ya ce tun farko hukumar ta karbi korafe-korafe sama da 150 tare da warware su cikin ruwan sanyi.

“Muna da tasiri sosai a fannin korafe-korafen jama’a, tun daga farko mun samu kararraki sama da 150 da suka hada da batutuwan aure, daGado, da karbo basussuka, da  takaddamar ciniki, da dai sauransu, kuma da dama daga cikinsu an warwaresu.” In ji shugaban na JGPCACC.

A nasa jawabin, shugaban hukumar kula da korafe-korafen jama’a da ke Abuja (PCC), Bashir Abubakar ya bayyanawa jami’an hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Jigawa irin tasirin da hukumarsa  ta ke bi wajen magance rikice-rikice.

“Jihar Jigawa na daya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya amma za ku iya taimakawa jihar wajen samun nasara idan kun yi amfani da fasahar sadarwa ta zamani wajen kawo korafe-korafe cikin sauki,” inji shi.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa korafe korafen jama a korafe korafe jihar Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Shirya Fara Tantance ‘Yan Fansho

Hukumar Fensho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomin jihar ta shirya fara aikin tantance ‘yan fansho da ke cikin tsarin.

Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Gidan Fansho, inda shugabannin kungiyar ‘Yan Fansho ta Najeriya reshen Jigawa suka halarta.

A cewarsa, an shirya fara aikin tantancewar ne daga ranar Litinin, 5 ga Mayu, 2025.

Alhaji Dagaceri ya bayyana cewa, an shirya hakan ne da nufin sabunta tsarin biyan fansho tare da tabbatar da ingancin bayanai.

Ya ce, aikin tantancewar zai gyara wasu ‘yan kura-kurai da suka kunno kai a cikin shekaru uku da suka gabata, da kuma tabbatar da ingantattun bayanai a jadawalin biyan fansho.

Ya kara da cewa, wannan yunkuri ya yi daidai da kudirin jihar gwamnati na tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin mulki, tare da bai wa ‘yan fansho dama su gyara duk wani bayanin da bai cika ba a takardunsu.

Shi ma da ya ke jawabi, Akanta Janar na Jihar, Alhaji Abdullahi S.G. Shehu, ya jaddada cewa aikin tantancewar zai bai wa ‘yan fansho damar sabunta bayanansu da suka bace ko suka canza a takardunsu.

Saboda haka, ya bukaci dukkan ‘yan fansho daga ma’aikatun gwamnati, sassan hukumomi, kananan hukumomi da kuma hukumomin ilimi na kananan hukumomi da su halarci tantancewar a ranar da aka tsara kamar yadda yake cikin jadawalin aikin.

A jawabinsa, Shugaban kungiyar kananan hukumomi ALGON ta Jihar Jigawa, Farfesa Salim Abdurrahman, ya tabbatar da cikakken goyon baya daga shugabannin kananan hukumomi 27 domin cimma burin aikin.

Shugaban na ALGON wanda shugaban karamar hukumar Malam Madori,  Alhaji Salisu Sani ya wakilta,  ya bukaci ‘yan fanshon da su ba da cikakken haɗin kai don samun nasarar shirin.

Shi ma Shugaban hukumar, Dr. Bilyaminu Shitu Aminu, ya bukaci ‘yan fansho daga sassa daban-daban da su ba da hadin kai domin cimma burin da aka sanya, tare da jaddada cewa su ziyarci sakatariyar kananan hukumominsu domin a tantance su.

Shugaban Kungiyar ‘Yan Fansho ta Najeriya reshen Jihar Jigawa, Alhaji Umar Sani Babura, ya yi alkawarin cewa kungiyar za ta bada cikakken goyon baya domin nasarar wannan shiri.

Dukkan ‘yan fansho daga Ma’aikatun Gwamnati, Kananan Hukumomi, da Hukumomin Ilimi na Kananan Hukumomi da ke cikin tsarin  fanshon, ya zama wajibi su halarci wannan tantancewa a ranakun da aka tsara a jadawalin aikin.

 

Usman Muhammad Zaria

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsoffin ma’aikatan NECO na neman a biya su bashin haƙƙoƙinsu
  • Yadda ’yan Tifa da baƙin direbobi ke haddasa haɗari a Abuja
  • NEMA Ta Karɓi ‘Yan Nijeriya 203 Da Suka Maƙale A Libya
  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Shirya Fara Tantance ‘Yan Fansho
  • Gwamna Namadi Ya Nada Aisha Mujaddadi Sabuwar Shugabar Hukumar InvestJigawa
  • Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok
  • Hajjin 2025: An Fara Yi Wa Maniyyata Allurar Rigakafi A Jigawa
  • Hajjin 2025: Jihar Kwara Ta Fara Allurar Rigakafi Ga Maniyyata
  • Hajjin 2025: Gwamna Namadi Ya Nada Sarkin Kazaure Amirul Hajj
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA