Kaduna: Gwamna Uba Sani Ya Tsabtace Harkokin Hajji – NUJ
Published: 8th, February 2025 GMT
An yabawa Gwamna Uba Sani saboda tsabtace harkokin hajji da kuma naɗa kwararru don jagorantar Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna.
Shugaban Kungiyar Yan Jaridu ta Kasa reshen Jihar Kaduna, Alhaji AbdulGafaar Alabelewe, ne yayi yabo yayin da jami’an kungiyar suka kai ziyarar ban girma ga hukumar.
NUJ ta kuma bayyana naɗin Malam Salihu S. Abubakar a matsayin Shugaban Hukumar a matsayin wanda ya dace da mukami, inda suka jaddada cewa gaskiyarsa da bin doka da na da matukar muhimmanci wajen ci gaban hukumar.
Alhaji AbdulGafaar ya ce hukumar ta samu nasarori masu yawa a lokacin hajjin da ya gabata, ciki har da maidawa kowane mahajjaci dala 50 daga kudin hadaya da suka biya a Najeriya.
Ya kuma ce mahajjatan jihar Kaduna sun sami matsuguni kusa da Masallacin Harami a Makka, kuma farashinsa ya kasance kasa da wanda Hukumar Kula da Hajji ta Kasa (NAHCON) ta tsara.
A cewarsa, maidawa mahajjatan shekarar 2023 naira 61,080 cikin gaggawa ya nuna cewa Malam Salihu da kwamitinsa suna da kwazo da himma wajen gyara harkokin hajji.
Alabelewe ya kuma yaba da gyaran da hukumar ta yi wa sansanin mahajjata na Mando, yana mai danganta nasarorin da gaskiya da rikon amana na shugabancin hukumar.
Shugaban NUJ ya sha alwashin ci gaba da hada hannu da hukumar wajen wayar da kan maniyyata, tare da kira ga ‘yan jaridu da su bai wa hukumar cikakken hadin kai.
Da yake mayar da martani, Malam Salihu ya gode wa ‘yan jaridu bisa kyakkyawar dangantaka da hukumar, tare da alkawarin ƙarfafa hulda da su. Ya bukaci su dinga tantance labarai masu shakku kafin wallafawa, yana mai cewa, “kofarmu a bude take don karin bayani.”
Shugaban hukumar ya gode wa Gwamna Uba Sani bisa goyon bayansa, yana mai cewa duk nasarorin da aka samu saboda tallafinsa ne.
Rel/Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Harkokin Kaduna Gwamna Uba
এছাড়াও পড়ুন:
Kwale-kwale Ya Kife Da Fasinjoji 16 A Karamar Hukumar Taura
Akalla mutane 7 ne aka ceto, bayan kifewar kwale-kwale a wani kogi da ke Zangon Maje, ƙaramar hukumar Taura, ta jihar Jigawa ranar Litinin.
Shugaban ƙaramar hukumar Taura, Dr Shuaibu Hambali ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar.
A cewarsa, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, lokacin da wasu manoma ke dawowa daga gonakinsu a ƙauyen Zangon Maje, inda suka hau kwale-kwalen.
Ya ce, jami’an bada agajin gaggawa na yankin sun samu nasarar ceto mutane 7 a kokarin da suka yi na ceto wadanda lamarin ya shafa.
Ya ƙara da cewa, masu ceton sun gano gawar mutum guda a yankin Yalleman da ke ƙaramar hukumar Kaugama.
Dr Shuaibu ya bayyana cewa, sauran mutane 9 da ke cikin jirgin har yanzu ba a same su ba a lokacin da ake bayar da wannan rahoto.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, ba a fitar da sunayen waɗanda abin ya shafa ba, amma lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin jimami da baƙin ciki.
Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana cewa, za a raba rigunan kariya (life jacket) ga fasinjoji a nan gaba kadan domin kiyaye sake afkuwar lamarin nan gaba.
Ya kuma gargadi matuka kwale-kwale da su kiyaye ƙa’idojin tsaro da kaucewa cunkoson fasinjoji, musamman da yamma a lokacin damina, inda ruwa ke ƙaruwa a kowane lokaci.
Dr Hambali, wanda ya isa wurin da abin ya faru, ya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Wasu daga cikin mazauna yankin da Rediyon Najeriya ta tattauna da su, sun nemi gwamnatin ta gaggauta ɗaukar matakan da suka dace, tare da inganta hanyoyin sufuri ta ruwa.
Usman Muhammad Zaria