Limamin Tehran:Trump Ba Zai Taba Cimma Manufofin Da Ya Bayyana Ba
Published: 7th, February 2025 GMT
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a yau anan birnin Tehran, Hajjatul-Islam Kazim Saddiki, ya bayyana cewa: Trump yana yin baraza da tsoratarwa da cewa zai rage karfin da Iran take da shi a fagen fasahar Nukiliya da kuma matsayin da take da shi a cikin wannan yankin na yammacin Asiya, sai dai kuma ya kamata ya fahimci cewa kamar yadda shugaban da ya gabace shi ya yi kuskuren lissafi, to shi ma haka yake yi.
Limamin na Tehran ya kuma ce,Kamar yadda shugaban Amurka da ya gabaci Trump bai sami nasara akan Iran ba, shi ma haka ba zai cimma manufarsa ba.
Hajjtul-Islam Siddiki ya kuma kara da cewa; Bai kamata ace muna kallon cewa ta hanyar abubuwa na zahiri ne kadai za a iya warware matsaloli ba,domin wannan shi ne koyawar tauhidi a cikin alkur’ani mai girma. Haka nan kuma ya yi kira da kar a biye da mika kai ga sha’awace-sha’awace na duniya ba, maimakon haka mu mika kai da yin biyayya ga dokokin Allah domin mu sami haskakawa akan hanyar da muke tafiya a kanta.
Da yake magana akan kwanaki 10 na cin nasarar juyin juya halin musulunci a Iran, Limamin na Tehran ta ce, abinda ya faru yana cike da darussa da al’umma za ta dauki darussa daga ciki har adaba. Kuma gagarumin sauyin da ya faru a cikin al’ummar Iran yana daga cikin manufar da juyi ya cimmawa a karkashin jagorancin Imam Khumaini (r.a).
Haka nan kuma ya bayyana cewa;siffa mafi girma da take tattare da juyin shi ne kasantuwarsa ta musulunci, kuma a lokaci daya akan tsarin jamhuriya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jagora: Iran Ta Bayyana Karfinta Da Jajircewarta A Yakin Kwanaki 12 Ga Duniya
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminai, ya bayyana cewa a cikin yakin kwanaki 12 da ya gabata JMI ta bayyanawa duniya karfinta da jajircewar a ga duniya. Da kuma tabbatan JM tayi a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto jagoran yana fadar haka a lokacinda yake jawabi a taron cika kwanaki 40 da shahadar wadanda suka yi shahada a yankin. Labarin ya kara da cewa mafi yawan wadanda suka halarci tarun iyalan shahidan yakin kwanaki 12 ne da jami’an gwamnati da kuma manya-manyan sojojin kasar da sauran Jama’a.
Jagoran ya kara da cewa, HKI da Amurka basu fadawa JMI da yaki don shirin ta makamashin Nukliya ko don take hakkin bil’adama ba, sai dai dukkan wadan nan wasila ne na yakar Imani da kuma addininku da kuma ci gaban da mutanen Iran suke samu. Har’ila yaum da kuma hadin kan da kuke da shi. Sun kasa raba kan iraniyawa don gwara kansu su su lalata kasarsu da kansu. Ya ce yakin kwanaki 12 da makiya suka dora mana baa bin mamaki bane, bai zo mana ba zata ba, mun san watarana zasu farmana da yaki, kuma yaki ba sabo ne a wajemmu ba, mun yi yakin shekaru 8 mun gamu da tashe-tashen hankula da dama a cikin gida. Ya ce amfanin wannan yakin a wajemmi shi ne duniya da ga ciki har da su makiya sun ga irin karfin da muke da shi. Da kuma irin shirin yaki da muka bayyana.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Mutum daya Yayi Shahada 4 Sun Ji Rauna Sanadiyar Hare-Haren HKI A Lebanon July 29, 2025 EU Tace Zata Dakatar Da HKI Daga Cibiyar Bincikenta Saboda Gaza July 29, 2025 Ma’aikatar Leken Asirin JMI Ta Ce Ta Gano Shirin Kashe Manyan Mutane 35 a kasar July 29, 2025 Najeriya: Likitoci a Lagas Sun Shiga Yajin Aiki July 29, 2025 Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai July 29, 2025 Sojojin HKI Sun Ci Gaba Da Kashe Kawunansu July 29, 2025 Kasar Holland Ta Hana MInistocin HKI Biyu Shiga Cikin Kasarta July 29, 2025 Manjo Janar Musawi: Ko Kadan Ba Mu Yarda Da Amurka Ba July 29, 2025 Araqchi: Iran Zata Mayar Da Martanin Da Ba Zai Yiwu A Boye Ba Kan Duk Wani Harin Wuce Gona Da Iri Kanta July 29, 2025 Kasar Iran Ta Musanta Yin Katsalandan A Tattaunawar Neman Tsagaita Bude Wuta A Gaza July 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci