Kasar Sin Ta Bayyana Rashin Jin Dadi Kan Matakin Kakaba Karin Haraji Na Kasar Amurka
Published: 2nd, February 2025 GMT
A jiya Asabar kasar Amurka ta sanar da kakaba karin harajin kwastam na kaso 10% kan kayayyakin da kasar Sin take fitarwa zuwa Amurka. Dangane da batun, ma’aikatar kasuwanci ta Sin ta bayyana rashin jin dadi da kin amincewa daga bangaren Sin.
Cikin sanarwar da ma’aikatar ta gabatar, ta ce matakin Amurka ya keta ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, wanda ba zai ba da damar daidaita matsalar da kasar Amurka ke fuskanta ba, maimakon haka, zai lalata huldar hadin gwiwa tsakanin kasashen 2 ta fuskar tattalin arziki da cinikayya.
A sa’i daya kuma, kasar Amurka ta ce za ta sanya karin harajin kwastam da ya kai kaso 25%, kan kayayyakin da take shigowa da su daga kasashen Mexico da Canada. Ban da haka, shugaban kasar Donald Trump ya ce yana duba yiwuwar kakaba karin haraji kan kayayyakin da ake shigar da su kasar Amurka daga kasashen Turai, ganin yadda kungiyar kasashen Turai EU ta hana shigowar motoci da amfanin gona na kasar Amurka cikin kasuwannin kasashen Turai, a lokacin da ya yi hira da ‘yan jaridu a kwanan baya. (Bello Wang)
কীওয়ার্ড: kasar Amurka
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Da Iraki Sun Ce An Kammala Shimfida Layin Dogo Daga Shalamcheh Zuwa Basra
A wani taro wanda ya hada ministan riko na tattalin arziki da kudade na JMI da kuma mai bawa firai ministan kasar Iraki shawara, bangarorin biyu sun tabbatar da cewa an kammala aikin shimfida layin dogo tsakanin garin Shalamcheh na kasar Iran da kuma birnin Basra a kasar Iraki.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jami’an gwamnatocin kasashen biyu na fadar haka, sun kuma jaddada muhimmancin layin dogon da kuma samar da kasuwar babu kudaden fito a kan iyakokin kasashen biyu.
Labarin ya kara da cewa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu ya zuwa yanzu ya kai dalar Amurka biliyon $11a ko wace shekara kuma anan saran nan gaba zai iyakaruwa zuwa dalar Amurka biliyon $25.
Rahmatollah Akrami, ministan riko na tattalin arziki da kudade na JMI, da kuma Hazem Majid Naji Al-Khalidi mai bawa firai ministan kasar Iraki shawara sun jaddada muhimmancin kammala layin dogo tsakanin kasashen biyu, da kuma kasuwar ba kudaden fito tsakanin kasashen biyu. Da kuma fatan zasu yi kokarin amfanar juna gwagwadon abinda zasu iya.