Hizbullah Ta Yi Alhinin Sahadar Muhammad Dhaif Kwamandan Rundunar Kassam Ta Hamas
Published: 1st, February 2025 GMT
A wani bayani da kungiyar ta Hizbullah ta fitar ta bayyana alhininta na shahadar babban hafsan mayakan rundunar “Kassam” ta kungiyar Hamas Muhammad Dhaif tare da wasu abokan aikinsa, tare da bayyana rawar da suka taka a fagen gwagwarmaya.
Kungiyar ta Hizbullaha ta mika sakon ta’aziyya da kuma barka akan shhadar Muhammad Dhaif ga kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas da sauran kungiyoyin Falasdinawa da kuma al’ummar Falasdinu.
Kungiyar gwgawarmayar musuluncin ta Lebanon ta kuma ambaci cewa, Muhammad Dhaif ya tafiyar da dukkanin rayuwarsa ne wajen fada da ‘yan sahayoniya da kwankwasar kansu, musamman ma dai a yayin farmakin Aksa, da ya kasance daya daga cikin fitattun wadanda su ka shriya shi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar
Shugaba Xi ya kara da cewa, a halin da ake ciki yanzu, duniya na fuskantar sauye-sauye irin wadanda ba a taba gani ba kuma cikin sauri. Don haka, kamata ya yi kasashen biyu masu dadaddun wayewar kai su zurfafa koyi da juna, da shigar da sabon kuzari cikin gina cikakken salon hadin kai, bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu, kana su tattaro karfin wayewar kai don gina al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil’adama.
A wani ci gaban kuma, wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping wato ministan raya al’adu da yawon bude ido na kasar Sun Yeli, ya halarci bikin bude babban gidan adana kayan tarihin na GEM bisa gayyatar gwamnatin Masar. Kafin bikin, shugaba al-Sisi ya gana tare da gudanar da gajeriyar tattaunawa da Sun Yeli. (Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA