Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-Rufai
Published: 30th, January 2025 GMT
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi zargin cewar akwai wasu shafaffu da mai da ake biya maƙudan kuɗaɗe domin kare Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Ya bayyana haka ne, yayin mayar wa Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa kan Harkokin Siyasar, Daniel Bwala, martani kan sukar da ya masa game da APC.
An kashe mutumin da ya ƙone Al-Ƙur’ani a Sweden Mahaifi ya harbe ’yarsa har lahira saboda wallafa bidiyo a TiktokEl-Rufai ya yi wannan magana ne a wani taro da aka shirya kan ƙarfafa dimokuraɗiyya a Najeriya.
Tsohon gwamnan ya soki jam’iyyar APC saboda rashin kwatanta dimokuraɗiyya, inda ya ce bai gane inda jam’iyyar ta dosa a yanzu ba.
A yayin martaninsa ga El-Rufai, Bwala ya tambayi ko El-Rufai zai ci gaba da yin irin waɗannan kalamai idan yana cikin gwamnati.
Bwala ya ce: “Ɗan uwana, idan kana cikinagwamnati da majalisar zartarwa, shin za ka riƙa irin waɗannan kalamai? Tarihi yana cike da misalai.
“Gwamnatin da ka taka rawa aka kafa, yanzu ita kake son saukewa. Haba Mallam, a ji tsoron Allah mana.”
El-Rufai ya mayar da martani, inda ya ce: “Na yi minista shekaru 22 da suka wuce kuma Asiwaju ya fahimci cewa bana sha’awar kowane muƙami a cikin gwamnatinsa.”
Ya ƙara da cewa, “Idan na zauna a cikin gwamnatin Tinubu, zan ci gaba yin abin da nake ganin ba daidai ba ne.”
El-Rufai ya kuma soki wasu daga cikin mutanen da ya ke ganin ’yan siyasa ne da ake biya don kare gwamnatin Tinubu.
Ya ce, “Wannan wasa ne na siyasa da ake biyan wasu kuɗaɗe masu yawa don suke shiga shafukan sada zumunta don kare duk abin da gwamnatin Asiwaju.”
Ya kammala da cewa, “Ka more muƙamin mai bayar da shawara na musamman, ɗan uwana, amma ka tuna cewa biyayya ga Allah da ƙasa yana da muhimmanci sama da kowane mutum ko hukuma.”
Majalisar Dattawa ga ƙi amincewa El-Rufai ya zama minista a 2023, saboda ƙarar da wasu abokan hamayyarsa suka shigar a kansa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Bwala gwamnatin tinubu Siyasa tsohon gwamna El Rufai ya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa ta horas da malamai 20,000 fasahar sadarwar zamani
Gwamnatin Jihar Jigawa ta horas da Malaman makarantun sakandare kimanin dubu 20 ilimin fasahar sadarwar zamani (digital).
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawaga daga Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta ƙasa (NITDA) da Cibiyar Zaman Lafiya ƙarƙashin jagorancin Farfesa Hauwa Ibrahim da take Amurka, a ziyarar ban girma da suka kai a gidan gwamnati da ke Dutse.
Peter Obi zai lashe jihohin Arewa idan ya koma PDP – Jerry Gana Mun yi asarar shanu 340 a hannun ɓarayi a Yuli — Miyetti AllahYa ce: “Mun gabatar da cibiya ta dijital don malamai, don sadarwa da kuma kula da ilmantarwa a matakin farko, mun sanya hannu kan haɗin gwiwa na shekaru biyar tare da NewGlobe don ƙarfafa ƙa’idojin rubutu da ƙididdiga ta amfani da kayan aikin dijital.
“Don haka shirin ku ya yi daidai da gyare-gyaren da muke da su kuma yana ƙara ƙimar ilimi matuƙa.” In ji Namadi.
Gwamna Namadi ya kuma nanata ƙudirin gwamnatin Jigawa na ɗorewar shirin, yana mai cewa, “Ina tabbatar muku: Za mu mallaki wannan shiri, za mu ci gaba da faɗaɗa shi, Kwamishinoninmu na ilimi a matakin farko da kuma na manyan makarantu za su sa ido a kansa.”
Darakta mai riƙon ƙwarya na dijital a Hukumar NITDA, Dokta Ahmed Tambuwal ya bayyana hangen nesa na ƙasa da ke jagorantar shirin.
“Muna nan a matsayin wani ɓangare na Hukumarmu ta NITDA na ci gaba da sadaukar da kai don aiwatar da ajandar Sabuwar Najeriya na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.”
“Babban ginshiƙi na wannan ajandar ita ce rarraba tattalin arzikin Najeriya ta hanyar fasahar dijital.”
Tambuwal ya bayyana cewa, NITDA tana ci gaba wajen cimma buri na kashi 70% na ilimin zamani a shekarar 2027, yana mai jaddada buƙatar haɗin gwiwa don cimma burin.