2025-05-02@14:24:22 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3366
«Bwala»:
Wata ƙungiyar matasa mai suna “North-East Coalition Against Terrorism” ta yi maraba da Major General Abdulsalam Abubakar, sabon kwamandan yakin Operation HADIN KAI (OPHK), inda ta bayyana cewa tana fatan zaman lafiya ya dawo yankin. A cikin wata sanarwa da Ismail Mustapha da Sakatare Danlami Bukar suka rattaba hannu, ƙungiyar ta ce Sojojin Nijeriya a...
Wuta ta tashi da safiyar yau Juma’a inda ta ƙone shaguna uku da wasu kayayyaki masu yawa a unguwar Sango da ke cikin babban birnin jihar Oyo, Ibadan. Manaja Janar na hukumar kashe gobara ta Jihar Oyo, Akinyemi Akinyinka, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa wutar ta tashi a bayan wani gidan...
A yau Juma’a 2 ga watan Mayu, 2025 Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ke ziyartar Jihar Katsina a karon farko tun bayan hawansa kujerar mulki. Kamar yadda gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa ta ce, shugaban zai duba wasu muhimman ayyukan da gwamnan ya aiwatar da waɗanda ake cikin yi. Wakilin mu ya...
Masana harkokin tsaro sun ja hankalin hukumomi su ɗauki matakan da suka dace bayan gobarar ma’ajiyar makamai a babban Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Sun bayyana damuwa game da mummunan abin da ke iya biyo baya ta fuskoki daban-daban, tare da bayar da shawarar matakan da ya kamata a...
Sai dai kuma, idan Atiku da sauran ‘yan adawa suka ji tsoro, wanda hakan mai yiwuwa ne, kuma Tinubu ya sake cin zaven 2027, wanda shi ma zai iya yiwuwa, hakan ba zai zama saboda sauya sheka ba ne; domin kuwa tuni Atiku ya share fagen ruguza PDP, don kuwa ya nuna shi ne yake...
Masana harkokin tsaro sun ja hankalin hukumomi su ɗauki matakan da suka dace, lura da abin da ke iya biyo bayan gobarar ma’ajiyar makamai a babban Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Sun bayyana damuwa game da mummunan abin da ke iya biyo baya ta fuskoki daban-daban, tare da bayar...
A sanarwar manema labarai da kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi, Babban Sufuritendan dansanda, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya tabbatar da cewa, cikin gaggawa aka yi tura jami’an ‘yansanda wanda hakan ya kai ga kamo Amusu. Wakil ya ce an kai yarinyar zuwa babban asibitin Bayara domin likita ya dubata kuma wanda ake zargin ya...
Amurka ta kawo ƙarshen cire haraji kan wasu kayayyaki da ba ma su tsada ba da ake shiga da su ƙasar daga China. A baya Amurkawa na iya sayan kayayyakin China da ba su haura dala 800 ba, idan za su yi oda ta intanet ba tare da wani haraji ba, amma yanzu za...
Kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC reshen jihar Kano ta yabawa gwamnatin jihar Kano kan kudirin ta na daidaita bashin da ake bin ‘yan fansho da ya haura naira biliyan 16. Da yake jawabi yayin bikin ranar ma’aikata da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata a Kano,...
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen gina jihar da ma’aikata za su bunkasa, samar da ayyukan yi masu nagarta, da baiwa kowane bangare damar bayar da gudunmawa mai ma’ana ga ci gaban jihar. Gwamna AbdulRazaq a cikin sakonsa na bikin ranar ma’aikata ta duniya na shekarar 2025, a Ilorin,...

Zamfara Ta Biya Sama Da Naira Biliyan 13 A Matsayin Bashin Garatuti Da Aka Gada – Mataimakin Gwamna.
Gwamnatin jihar Zamfara ta kammala biyan sama da naira biliyan 13 na garatuti, wanda ke nuna wani gagarumin mataki na inganta jin dadin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya a jihar. Mataimakin gwamnan jihar, Mani Malam Mummuni, ya bayyana hakan a yayin bikin ranar ma’aikata na shekarar 2025 da aka gudanar a Gusau, babban...
Gwamnatin jihar Kebbi, ta baiwa ma’aikatan jihar tabbacin ci gaba da jajircewa wajen kyautata jin dadin su da kuma kare hakkokinsu. Gwamna Nasir Idris wanda ya ba da wannan tabbacin a lokacin da yake jawabi ga ma’aikata domin bikin ranar watan Mayu a Birnin Kebbi, ya jaddada cewa ma’aikata aminai ne masu kima wajen...
Gwamna Umar Namadi ya bi sahun kungiyoyin kwadago domin tunawa da irin gudunmawar da ma’aikata ke bayarwa wajen ci gaban jihar Jigawa. Da yake gabatar da jawabinsa, Gwamna Namadi ya yaba da jajircewar ma’aikatan Jigawa, inda ya bayyana ma’aikata a matsayin masu kawo ci gaba. Ya bayyana cewa, ma’aikata a dukkan bangarori suna...
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago ya bayyana dangantakarsa da mataimakinsa, Kwamared Yakubu Garba a matsayin cikakkiya da jituwa. Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai kan dangantakarsa da mataimakinsa bayan bikin ranar ma’aikata a Minna. A cewarsa, “mu kungiya ce, ba za su iya karya mu...
Jami’an tsaron sa kai sun kama wasu abokai biyu masu sana’ar acaba, bisa zargin yin fyaɗe ga wata Bafulatana mai tallar fura da nono a Yankin Babban Birnin Tarayya Abuja. Wani jami’in tsaron sa kai, Usman Dantala, ya ce abokan biyu sun yi wa Bafulatanar fyade ne da tsakar rana a yankin Ikwa da ke...
“Murkushe ‘yan adawa tare da musguna musu, musamman jam’iyyar PDP, wata alama ce karara da ke nuna cewa; zangon karshen mulki na karatowa; domin kuwa tarihi ya sha nuna hakan”, in ji Lamido a tattaunawarsa da BBC Hausa. “Ya kamata Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya kasance mai adalci, domin shi ne shugaban dukkanin...
An kama wani matashi ɗan shekaru 33 bisa zargin yin garkuwa da ’yar maƙwabcinsa mai shekaru 21 a ƙauyen Paikon Bassa da ke Ƙaramar Hukumar Abaji a yankin Babban Birnin Tarayya. Wani ɗan banga a yankin, Dangana Bala, ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan samun ƙorafi daga iyayen matashiyar da ta ɓace...

Ranar Maleriya Ta Duniya: ‘Yan Nijeriya Na Kashe Naira Tiriliyan 1.156 Duk Shekara Wajen Sayen Magunguna
Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa, duba mara lafiya guda daya tak da ke dauke da cutar Maleriyar da ba ta yi karfi sosai ba a asibitin gwamnati, na lashe kimanin Naira 17,000, tsakanin ganin likita, yin gwaje-gwaje da kuma magunguna. Wadannan kudade sun kai kimanin Naira tiriliyan 1.156 da ake kashewa a kan wannan...

Sabon Tsarin Ci Gaba Na Sin Ya Kawo Sauyi Daga Samar Da Takalma Miliyan 100 Zuwa Kera Mattarar Bayanai Ta Microchip
Kamar yadda firaministan kasar Malaysia Anwar bin Ibrahim ya fada a kwanan baya cewa, yayin da kasa da kasa ke fuskantar mawuyacin hali, suna bukatar samun tabbaci da wani nagartaccen shiri na samun ci gaba. Don haka, ana ganin yadda kasar Sin ta samu nasarori, an nuna yabo ga kasar ta Sin, kasar Sin ta...
Al’ummar Arewa mazauna yankin Obalande da ke Jihar Legas sun yunƙura domin tunkarar matsalolin da ke ci musu tuwo a ƙwarya, musamman yadda suka ce ’yan ƙasa ke musu cin kashi. Sun ce sun gaji da irin tsangwama da ƙasƙanci da ’yan ƙasa a yankin ke nuna wa ’yan Arewa, musamman Hausawa mazauna. Sun bayar...

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce Kasar Oman Ce Ta Bukaci Dage Zaman Tattaunawan Iran Da Amurka
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: An dage zaman tattaunawan Iran da Amurka ne bisa shawarar kasar Oman Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi nuni da cewa: Ministan harkokin wajen kasar Oman ne ya sanar da sauyin lokacin zaman tattaunawan ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka,...
Ministan Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta zama babbar alamar ta’addanci a duniya Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh, yayin da yake yin Allah wadai da kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suke yi wa al’ummomin Falastinu da na Lebanon a daidai lokacin da kungiyoyin kasa da kasa da tarurrukan...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kimanin Naira biliyan ɗaya ce aka ƙiyasta ta salwanta sakamakon gobarar da ta ƙone wani sashe na babbar kasuwar da ke tsakiyar garin Jos, babbar birnin Jihar Filato. An rawaito cewar gobarar ta laƙume shaguna fiye da ɗari biyar, galibinsu na masu sayar da kayan gwanjo. Mutane da...

Masifar Gobara Tana Kara Bunkasa A Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tare Da Fara Raba Yahudawa Da Muhallinsu
Ana sa alamar tambayar cewa: Shin gobarar da ta tashi a birnin Kudus… shin sako ne na ranar tunawa da kafuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya? Gobarar da ta tashi a tsaunin Kudus da aka mamaye ta bazu zuwa manyan yankuna a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta kewaye wani sansanin soji tare da cinye filayen masu...
Ma’aikatan jihar Ribas sun hallara a sakatariyar kungiyar kwadago ta kasa, NLC da ke Fatakwal domin bikin ranar ma’aikata ta 2025 a ranar Alhamis. Dama kungiyar ta NLC, tuni ta sanar da cewa, ba za ta gudanar da bikin murnar ranar ma’aikata ba kamar yadda aka saba yi a filin shakatawa na Isaac Boro, inda...
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yaba wa takwarorinsa na gwamnonin Jihohin Borno, Bauchi, Adamawa, Gombe da Taraba a bisa ga samun damar da suka yi na halartar taron ƙungiyarsu ta Arewa maso Gabas (NEGF) karo na 11 a garin Damaturu. Ya yi wannan yabo ne a ranar Alhamis a ɗakin taro na gidan gwamnati...
Cibiyar cinikayyar kasashen waje ta kasar Sin, mai shirya bikin, ta ba da sanarwar cewa, baya ga wuraren baje kolin da suka shafi farfado da yankunan karkara da za a ba su rumfuna kyauta, sauran masu baje kolin kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje su ma za a rage musu kudaden rumfunansu da kashi...
Haka kuma, kasar Sin ta yi nuni da cewa, matakan kasar Amurka kan harajin kwastam sun kawo illa ga cinikayyar duniya, da moriyar kasashe masu tasowa, amma kasar Sin a nata bangaren kokari take yi wajen tabbatar da bunkasar cinikayya ta duniya, da kuma tsayawa tare da kasashe masu tasowa. (Zainab Zhang) Daga kanmu,...
Faɗin ginin, wanda ya haura sukwaya mita 13,000, ya ƙunshi babban ginin tashar da ababen da ke tattare da shi, kuma zai kasance tashar da ta fi kowace girma a layin dogon da ake kira Kaka Reluwe. Kaka Reluwe na nufin hanyar dogo daga KAduna zuwa KAno. Kamfanin CCECC ya ce idan an...
A ranar Laraba ne jami’an sojojin ruwa na Najeriya da ke Fatakwal suka ceto fasinjoji 99 daga wani hatsarin kwale-kwale da ya rutsa da su a kogin Bukuma da ke ƙaramar hukumar Degema a Jihar Ribas. Jirgin ruwan, wanda yake na jigilar fasinja yana kan hanyarsa ta daga Fatakwal zuwa Ƙaramar hukumar Akuku-Toru, inda ya...
Jakadan kasar Sin ya bayyana cewa, kasar tana kiran a samar da hanyar kawar da makaman nukiliya wacce a karkashinta ba za a iya raba tsaro na kashin kai da tsaro na bai daya ba, tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Babban darektan sashen kula da makamai na ma’aikatar harkokin...
Gwamnan ya kara da bayyana biyan Biliyan 16 na basussukan fansho, da kuma sauya mafi karancin fansho daga ₦5,000 zuwa ₦20,000, da kuma fitar da Naira miliyan 100 domin tallafawa ayyukan ’yan fansho. A wani mataki makamancin haka, gwamnan ya sanar da kafa sabbin ma’aikatu 4 da hukumomi 2 da za su zaburar da...
Kasashen Iran da Nijar sun gudanar da taron kwamitin hadin gwiwa kan tattalin arziki. An gudanar da taron ne a gefen taron baje koli na Iran 2025, karo na bakwai na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda aka fara a birnin Tehran a ranar Litinin. Mohammad Atabak, ministan masana’antu, ma’adinai, da kasuwanci na Iran; da Mohammad...
Hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta nuna matukar kaduwa game da halin da ake ciki a Gaza. Abin da ke faruwa a Gaza “ba abinda za’a lamunta da shi ne ba,” in ji Mike Ryan, mataimakin darekta-janar na Hukumar Lafiya ta Duniya, yayin wani taron manema labarai. Mista Ryan, ya nuna fushinsa matuka game da...
Iran ta sanar da cewa an dage tattauanwa ta karo na hudu da aka shirya gudanarwa tsakaninta Washington a ranar Asabar mai zuwa. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ne ya sanar da manema labarai da hakan a yammacin yau Alhamis yana mai cewa an sauya ranar da za a gudanar da tattaunawar ta gaba...
Jiragen yakin Amurka sun sake kai hare-hare da dama kan lardunan Saada da Hudaidah na kasar Yemen yau Alhamis. Wata majiyar tsaro a Yemen ta kara da cewa, an kai wasu hare-hare uku a yankin Kataf da ke lardin Saada, yayin da wani kuma ya afkawa gundumar al-Houk da ke lardin Hudaidah a gabar tekun...
Gwamnan Zulum ya yi tsokaci dangane da yadda tabarbarewar harkokin tsaro ke ci gaba da zafafa a yankin, yayin da kuma ya yaba wa kokarin sojojin Nijeriya, inda ya ce, “Ina kira gareku, ku ci gaba da yaki da yan ta’adda har sai mun kawo karshen wannan matsalar.” “Dawowar hare-haren yan ta’adda a cikin...
Iran ta yi tir da Allah-wadai da sabbin takunkuman da Amurka ta lafta mata. Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce matakin wata babbar alama ce da ke nuna cewa Washington ba ta da kyakyawar niyya, hasali ba abar yarda ce ba. Sanarwar ta bayyana karara cewa Iran ba...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ranar Alhamis ɗin nan ne rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa, an samu fashewar wani abu a wurin ajiyar makamai da ke barikin Giwa a Maiduguri wanda ya faru sakamakon tsananin zafi da aka samu a yankin. A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis mai ɗauke da sa hannun muƙaddashin daraktan...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi ne sun kai hari kan wani jirgin ruwa da ke jigilar mata ’yan kasuwa zuwa Ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudancin Jihar Bayelsa, a kan hanyar ruwan Lobia/Foropa. Rahotanni sun ce maharan sun yi garkuwa da wasu mata huɗu a lokacin da lamarin ya faru a ranar Talata....
Zargin sabani tsakanin Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, da mataimakinsa, Kwamred Yakubu Garba, ya karu a yau Alhamis bayan da mataimakin gwamnan ya kaurace wa bikin Ranar Ma’aikata a birnin Minna, babban birnin jihar. LEADERSHIP ta ruwaito cewa Kwamred Garba, wanda shi ne tsohon shugaban reshen jihar na ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), bai...
An tashi 3-3 tsakanin Barcelona da Inter Milan a wasan farko zagayen daf da karshe a Champions League da suka kara a Sifaniya ranar Laraba. Inter Milan ce ta fara cin ƙwallo a daƙiƙa 30 da take leda ta hannun Marcus Thuram, ya zama na farko da ya ci ƙwallo a ƙanƙanin lokaci a daf...
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wayar da kan al’umma kan kare lafiyar ruwa tare da raba riguna a wasu zababbun Jihohin Najeriya. Ministan Tattalin Arzikin Ruwa, Adegboyega Oyetola wanda ya kaddamar da taron a gidan gwamnati, Minna ya ce wannan ra’ayin ya yi daidai da jajircewar Gwamnatin Tarayya na kare rayuka da dukiyoyin al’umma...
An ce shafin neman aikin zai kasance a buɗe har tsawon makonni biyu. Bayan haka, za a zaɓi waɗanda suka cancanta domin ganawa da su da kuma tantance su Hukumar ta shawarci duk masu sha’awar aikin da su gaggauta cike fom ɗin domin guje wa cunkoson mutane a ranar ƙarshe. Gwamna Fintiri ne, ya bayar.da...
Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da kashe Naira biliyan 51.5 wanda ba a taba ganin irinsa ba, domin muhimman ababen more rayuwa da ayyukan yi wa al’umma hidima a fadin jihar, a wani bangare na tsare-tsare na gwamnatin na bunkasa zamantakewa da tattalin arziki. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai...
Gwamnatin jihar Kwara ta sake jaddada kudirinta na kara bude kofa ga al’umma domin ci gaba da kuma sanya jihar ta yadda za ta yi tasiri a duniya ta hanyar sanya hannun jari mai inganci. Kwamishinan Ayyuka na Jiha Injiniya. Abdulquawiy Olododo, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da ayukkan ma’aikatar...
Gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa samar da kasar Falasdinu mai cikekken yenci , kuma da dukkan birnin Qudus a matsayin babban birnin kasar, hakkin Falasdinawa ne wannan babu tattaunawa a kansa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jakadan kasar Iran na din din din a MDD Amir Said Iravani yana fadar...
Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu tare da hadin guiwar Kyakyawar Gate Handicapped Centre Jos, sun bayar da tallafin keken guragu guda dari da talatin ga masu bukata ta musamman a Birnin Kebbi na jihar Kebbi. Kakakin Ministan, Sadiq Nura Maiyaka, ya ce Ministan ya kuduri aniyar taimakawa masu bukata...

An Bukaci Masu Yiwa Kasa Hidima Su Yi Amfani Da Kafofin Sadarwa Na Zamani Don Inganta Hadin Kan Kasa.
Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC), Birgediya-Janar Olakunle Oluseye Nafiu, ya yi kira ga mambobin kungiyar a fadin kasar nan da su yi amfani da kafafen sada zumunta na zamani cikin gaskiya da kuma bayar da gudunmawa mai ma’ana ga ci gaban kasa. Ya bayyana hakan ne a lokacin da...