2025-07-31@23:07:18 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4327

«Majalisar Ɗinkin Duniya»:

    Har ila yau, Ribadu ya ce yanzu mutane suna iya zuwa gonakinsu a wuraren da a baya ba a iya shiga saboda barazanar ‘yan bindiga. Sai dai duk da wannan ikirari, har yanzu wasu yankunan kamar Zamfara, Benuwe da Filato na fama da hare-haren ‘an bindiga da rikicin ƙabilanci. A ƙarshen makon da ya gabata,...
    An shawarci gwamnatocin jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara da su kirkiro hanyoyi na wayar da kan al’umma dangane da shirye-shiryen tallafi da ayyukan ci gaba da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa domin bunkasa tattalin arziki da tabbatar da tsaro a yankunansu. Shugaban sashen kimiyyar zamantakewa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Chika Umar Aliyu,...
    Kwamitin neman sabuwar Karamar Hukumar Kanya Babba daga Karamar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa, ya gabatar da takardar bukatarsa ga kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da kirkiro jihohi da kananan hukumomi a zaman da aka yi a jihar Kano. A yayin mika takardar, Shugaban kwamitin kuma Hakimin Kanya Babba,  Makaman Ringim, Malam Mohammed Ibrahim...
    Shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara wanda ke jagorantar ƙasar tun daga shekarar 2011, na fuskantar suka na neman mayar da shugabancin ƙasar mutu ka raba. Wannan dai na zuwa ne bayan Ouattara mai shekaru 83 ya tabbatar da aniyar sake takara wa’adi na hudu a zaben da za a yi ranar 25 ga watan Oktoba....
    Birtaniya ta sanar da cewa muddin Isra’ila ba ta biyayya wa wasu sharuɗa ba, to kuwa a watan Satumba mai zuwa za ta amince da Falasɗinu a matsayin halastacciyar ƙasa a yayin taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA). Firaiministan Birtaniya Keir Starmer ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya gudanar a yau...
    Birtaniya ta sanar da cewa muddin Isra’ila ba ta biyayya wa wasu sharuɗa ba, to kuwa a watan Satumba mai zuwa za ta amince da Falasɗinu a matsayin halastacciyar ƙasa a yayin taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA). Firaiministan Birtaniya Keir Starmer ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya gudanar a yau...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Uwargidan Shugaban Nijeriya, Sanata Remi Tinubu ta bayar da tallafin naira biliyan daya ga wadanda harin nan ya rutsa da su a yankin Yelwata na Ƙaramar Hukumar Guma a Jihar Benuwe. Sanata Tinubu wadda ta miƙa cakin kuɗin ga Gwamna Hyacinth Alia ta sanar da bayar da tallafin ne a jawabinta na jaje wanda ta...
    Jamhuriyar Nijar da ƙasar Rasha a ranar Litinin, 28 ga watan Yulin 2025 sun ƙulla yarjejeniya game da makamashin nukiliya da kuma haƙar yuraniyom. Kamfanin dillancin labaran Nijar (ANP) ya ruwaito cewa ƙasashen biyu sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar ce bayan ganawar shugaban Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, da wata babbar tawagar Rasha ƙarƙashin jagorancin...
    Yau Talata, kwamitin kwaskwarima da raya kasar Sin, ya fitar da kudin Sin RMB yuan miliyan 200, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 28, domin tallafawa wajen farfado da sassan birnin Beijing da bala’in ambaliyar ruwa ya shafa, musamman ma fannin sake gina ababen more rayuwar jama’a na sufuri, da samar da ruwan sha, da kiwon lafiya,...
    Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminai, ya bayyana cewa a cikin yakin kwanaki 12 da ya gabata JMI ta bayyanawa duniya karfinta da jajircewar a ga duniya. Da kuma tabbatan JM tayi a kasar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto jagoran yana fadar haka a lokacinda...
    Ma’aikatar leken asiri na JMI ta bada sanarwan cewa ta gano shirin makiya na kashe manya-manyan Jami’an gwamnati har 35 a kasar kafin yakin da suka dorawa kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar ma’aikatar na fadar haka, ta kuma kara da cewa a cikin yakin kwanaki 12 sun yi kokarin...
    Likitoci a jihar Lagos na tarayyar Najeriya sun fara yajin aiki na gargadi na kuma kwanaki 3 saboda nuna rashin amincewasu da rage hakkokinsu da kuma hanasu kudadensu wanda gwamnatin jihar take yi. Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa duk tare da kokarin da ma’aikatar kiwon lafiya ta yi don kada likitocin su...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Uwargidan Shugaban Nijeriya, Sanata Remi Tinubu ta bayar da tallafin naira biliyan daya ga wadanda harin nan ya rutsa da su a yankin Yelwata na Ƙaramar Hukumar Guma a Jihar Benuwe. Sanata Tinubu wadda ta miƙa cakin kuɗin ga Gwamna Hyacinth Alia ta sanar da bayar da tallafin ne a jawabinta na jaje wanda ta...
    Akalla mutane 7 ne aka ceto, bayan kifewar kwale-kwale a wani kogi da ke Zangon Maje, ƙaramar hukumar Taura, ta jihar Jigawa ranar Litinin. Shugaban ƙaramar hukumar Taura, Dr Shuaibu Hambali ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, lokacin...
    2. Asibitin Turai Yar’Adua 3. Asibitin Amadi Rimi 4. Asibitin Jibia 5. Asibitin Funtua Zango, ya ce gwamnati na ƙoƙarin tabbatar da cewa duk wanda ke fama da cutar ya samu magani cikin sauƙi ba tare da biyan kuɗi ba. Zazzabin taifod yana yaɗuwa ne musamman a lokacin damina, kuma yana da nasaba da amfani...
    Mahara sun kashe akalla mutane biyar a Dajin Madam da ke yankin Karamar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi. Wannan na zuwa ne bayan a makon jiya ’yan bindiga sun kutsa kauyukan da ke kusa da garin Mansur a karamar hukumar, inda suka kashe mutane hudu, suka kwashe kayayyaki a shagunansu. Daga bisani ’yan sanda sun...
    Dan majalisa mai suna muhammad Mirzai ya ce; Kasashen turai sun zaku, akan su sami bayanai akan girman asarar da aka yi wa cibiyoyin Nukiliyar Iran don haka ya zama wajibi Iran din ta yi amfani da siyasar barinsu a cikin duhu. A yayin zaman da majalisar shawarar musulunci ta Iran ta yi a yau...
    Wani mutum ya rasu yayin da yake ƙoƙarin raba wani mutum da matarsa da fada a yankin Babban Birnin Tarayya. Da farko mutumin ya faɗi ne a sume kafin daga bisani rai ya yi halinsa a yankin Dogon-Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Abaji. Wani ganau, Barnabas Yakubu, ya ce lamarin ya faru ne a ranar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mata a Arewacin Najeriya na fuskantar kalubale da dama a fannin karantar kimiyya. Akwai darussan da a mafi yawan lokuta ba mata kadai ba, har da mazan na kaurace musu. NAJERIYA A YAU: Matakan Da Muke Dauka Don Karfafawa ’Yan Najeriya Kwarin Gwiwar Kada Kuri’a —INEC DAGA LARABA:...
    Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Idan aka maimaita ta’asar kai hari kan Iran, za ta mayar da martani ta hanyar da ba za a iya boyewa ba Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya mayar da martani kan barazanar da jami’an Amurka suka yi a baya-bayan nan, inda ya ce idan aka sake...
    Martanin da Rasha ta mayar dangane da sabon wa’adin Trump na kawo karshen yakin Ukraine Mataimakin shugaban kwamitin tsaron Rasha Dmitry Medvedev ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump game da takaita wa’adin tsagaita bude wuta tsakanin Rasha da Ukraine, yana mai cewa matakin kunna yaki ne. Medvedev ya rubuta a kan dandalinsa...
    Mummunar yunwa a Gaza.. Wakilin gidan talabijin na Al-Alam ya bayyana cewa: Shi da iyalansa kwana biyu ba su ci abinci ba Wakilin gidan talabijin na Al-Alam na kasar Iran ya ruwaito cewa: An samu barkewar yunwa mai tsanani a Gaza, inda ya tabbatar da cewa ya kwashe kwanaki biyu bai ci komai ba. Basil...
    Amma yanzu, babu matsalar gaba ɗaya a ƙananan hukumomi 11, yayin da aka samu sauƙi a wasu tara. Ya ce har yanzu ana fama da hare-hare a ƙananan hukumomi huɗu: Faskari, Ƙankara, Safana da Matazu. Kwamishinan ya jaddada cewa jami’an tsaro suna iyakar ƙoƙarinsu, kuma gwamna yana ci gaba da tattaunawa da manyan jami’an tsaro...
    Sama da mutum 100 daga cikin jami’an tsaron al’umma da  Gwamnatin Katsina ta samar ne suka suka mutu a yayin aikin karaɗe ’yan bindiga da suka addabi al’ummomin jihar. Wannan ƙari ne a kan sojoji da kuma aƙalla jami’an ’yan sanda 30 da suka rasu a yayin aikin tabbatar da tsaron rayuwa da duniyoyin al’umma,...
    Ya bayyana halin da aka shiga mara daɗi, inda ya jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu da waɗanda suka yi asarar dukiyoyi, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta tallafa musu wajen sake gina musu gidajen su da sauya muhallinsu. Fintiri ya kuma soki waɗanda ke yaɗa rahotannin ƙaryar game da lamarin, ba tare...
    Umarnin NYSC ta amince da sanya siket ga mata masu hujjar sanya wa saboda addininsu. Umarnin NYSC ta dawo da su ta ‘yan matan da suka shigar da ƙarar tare da ba su takardar shaidar kammala NYSC. Kotun kuma ta bayar da umarnin bai wa kowacce daga cikinsu kuɗaɗe har ₦500,000 a matsayin diyya saboda...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa Iran a shirye take ta fadada hulda da kasashen turai, amma kuma wannan ba zai sa ta saryar da hakkinta na sarrafa makamashin nukliya karshen dokokin kasa da kasa wadanda suka amince mata ta yi haka ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban...
    Alkalin alkalan JMI Gholamhussain Muhsen Ejei, ya bayyana cewa, babu shakka gwamnatin kasar Amurka tana da hannu a hare-haren da ake dangantawa da kungiyar yan ta’adda ta Jaishul Zulm da ya faru a cikin wani kotu a garin Zahidan na lardin sistan Baluchistan a cikin yan kwanakin da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a...
    Shugaban kasar Masar Abdulfattah Assisi ya bukaci shuggaban kasar Amurka Donal  Trump ya taiama ya kawo karshen yaki a Gaza, ya kuma kawo karshen walar da Falasdinawa suke ciki. Jaridar The Nation ta kasar Amurka ta nakalto shugaba Sisi yana fadar haka a wani jawabinda ya gabatar a yau Litinin, inda yayi alkawaliwa mutanen kasar...
    A yankin sweida na kudancin kasar Siriya mazauna wurin sun bayyana cewa abinci da ruwa da kuma kayakin bukatu nay au da kullum sun fara karanci sosai a yankin saboda yakin makonni uku da suke fafatawa da sojojin sabuwar gwamnati a Damascus. Jaridar The National ta Amurka ta bayyana cewa yankin sweida na kudancin kasar...
    Shugaba Bola Tinubu ya karrama ’yan wasan tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya da lambar yabo ta OON. Shugaban ya bai kowacce ’yar wasa  a tawagar ta Super Falcons kyautar gida mai ɗakuna 3 a rukunin gidaje na Renewed Hope da kuɗi dala dubu 100. Haka kuma, shugaban ya kuma bai wa masu horas...
    Kasar Sin ta bullo da wani shirin bayar da tallafin kula da yara a fadin kasar wanda zai fara aiki daga shekarar 2025, a wani bangare na kokarin tallafa wa iyalai da kuma karfafa yawan haihuwa. Shirin zai bai wa iyalai tallafin yuan 3,600, kimanin dalar Amurka 503, a kowace shekara a kan kowane yaro...
    Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana alhinin sa kan rahotannin ambaliya mai tsanani da ta faru a Yola, Jihar Adamawa, wacce ta yi sanadiyar  mutuwar mutane, da asarar dukiyoyi da kuma raba dimbin jama’a da muhallansu. A cikin wata sanarwa, Gwamna AbdulRazaq ya ce kungiyar NGF na jajantawa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya DSS da takwarorinsu na rundunar sojin ƙasa sun kashe aƙalla ’yan ta’adda 45 da ke addabar wasu sassan Jihar Neja. Bayanai sun ce an kashe ’yan ta’addan ne a ƙauyen Iburu da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro a ranar Juma’ar da ta gabata bayan jami’an DSS sun tattaro bayanan sirri kan...
    Da safiyar yau Litinin ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai, bisa taken “Cimma burikan da aka tsara domin neman bunkasa tattalin arziki da zaman takewar al’umma a tsakanin shekarar 2021 zuwa shekarar 2025”. A yayin taron, jami’in babbar hukumar buga haraji ta kasar Sin ya bayyana cewa,...
    Hukumar Tsarin Fansho na Hadin Gwiwa tsakanin Jiha da Kananan Hukumomi a Jihar Jigawa ta bayyana cewa ta raba sama da Naira Biliyan 1 da dubu 500 ga tsofaffin ma’aikata 569. Yayin da yake jawabi ga wadanda suka ci gajiyar shirin a gaban Gidan Fansho kafin fara rabon kudin, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad...
    Kasar Sin ta fitar da manyan manhajojin AI har 1,509, matakin da ya sanya ta kaiwa matsayi na daya cikin jerin sassan duniya da suka fitar da jimillar irin wadannan manhajoji 3,755. Masana na ganin bunkasar sashen masana’antun fasahohin AI na kasar Sin zai ingiza sabbin nasarori a fannin. A jiya Lahadi, yayin taron karawa...
    Jam’iyyar ta bayyana cewa bayan bincike daga reshen jam’iyyar na jihar Kaduna, ya tabbatar da cewa El-Rufai ba halataccen ɗan SDP bane. Saboda haka, Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na Ƙasa ya kafa masa takunkumin shekaru 30, har zuwa shekarar 2055, ya hana shi sake neman zama mamba ko hulɗa da jam’iyyar ta kowace fuska. Daga...
    Gwamnatin Kano ta sanar da cewa akwai aƙalla fiye da mutum miliyan 1.2 da ke fama da ciwon hanta da ake kira Hepatitis B a faɗin jihar. Kwamishinan Lafiya, Dokta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan yau Litinin yayin wani taron manema labarai a Cibiyar Tiyata ta Gaggawa da ke Asibitin Nasarawa a birnin...
    A kokarinsa na gano hakikanin dalilan da suka sa aka bayar da beli ga wani sanannen mai safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Dan Wawu, da aka ce an sako shi bisa umarnin Kwamishinan Sufuri na Kano, Ibrahim Ali Namadi, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da wani kwamiti na mutum takwas domin...
    Ministan Harkokin Tsaron Ƙasa, Dakta Bello Mohammed Matawalle, ya baiwa iyalan marigayi Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello, gudummawar naira miliyan biyar da kuma kayan abinci, bayan rasuwarsa a ranar Alhamis da ta gabata a birnin Abuja sakamakon gajeruwar rashin lafiya.   Dakta Matawalle, ya bayyana alhininsa bisa wannan rashi na Mai Martaba.   Baya...
    Gwamnatin Najeriya ta ba wa ƙasar Habasha kyautar itatuwan cashew guda 2,000 da kuma irin cashew guda 100,000. Najeriya ta bayar da kyautar irin ne a wani bangare na yunƙurin taimaka wa ƙasashen biyu wajen samar da abinci mai yawa da kuma ƙarfafa dangantakarsu. Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya bayar da wannan kyauta,...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kasar Amurka ta sanar da dakatar da bai wa mutanen Nijar bisa ta shiga cikin kasarta har illa masha Allahu. Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka ne ya tabbatar da cewa an dakatar da bayar da bisa din ga ‘yan kasar Nijar da suke son shiga cikin kasar, saboda abinda ya kira matsala...
    A yau Litinin ne za a yi jana’izar sanannen mawakin kasar Lebanon wanda ya yi fice da wakokin gwgawarmaya da kishin kasa wanda zai sami halartar wakilan gwamnatin kasar da kuma al’umma. Jana’izar za ta kasance ne a majami’ar  Raqad Sayyida dake garin Bakfaya. Asibitin Khuri da Rahbani ya rasu ya cika da mutane tun...
    Wani jami’in kasar Ukiraniya ya bayyana cewa, a kalla mutane 8 ne su ka jikkata sanadiyyar munanan hare-haren da Rasha ta kai wa birnin Kiev ta hanyar amfani da makamai masu linzami. Shugaban sha’anin tafiyar da Mulki na soja a birnin Kiev Taimur Tikatishinko ya wallafa sanarwa a shafinsa na “Telegram’ cewa; A tsakanin wadanda...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp