Hatsarin kwale-kwale ya yi ajalin mutum 29 a Neja
Published: 3rd, September 2025 GMT
Aƙalla mutum 29 sun rasu a wani hatsarin kwale-kwale da ya auku a gabar kogin Malale da ke cikin Karamar Hukumar Borgu a Jihar Neja.
Aminiya ta ruwaito cewa, kwale-kwalen wanda ke ɗauke da fasinjoji 90, ya tashi ne daga Tugan Sule da ke yankin Shagunu, inda ya nufi Dugga domin zuwa wata ta’aziyya.
Dalilin da Najeriya ba ta jin tsoron matakan Trump — Tinubu Boko Haram ba kiristoci kaɗai suke kashewa a Arewa Maso Gabas ba — NdumeMajiyoyi sun bayyana cewa cikin waɗanda suka mutu har da mata da ƙananan yara, kuma zuwa yanzu an gano gawarwaki 29, yayin da aka ceto mutum 50 da ransu, sai kuma wasu mutum biyu da har yanzu ake ta ƙoƙarin lalubo su.
Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, wanda Aminiya ta tuntuba ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Haka kuma, wani babban jami’in Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa na Ƙasa (NIWA) a yankin, Akapo Adeboye, ya tabbatar da hakan ta wayar tarho.
A cewar Daraktan NSEMA: “Mun samu rahoton hatsarin kwale-kwale a wani gari mai suna Gausawa da ke yankin Malale a Borgu.
“Bisa bayanan da muka samu, kwale-kwalen ya tashi daga Tugan Sule da ke cikin gundumar Shagunu wanda yake ɗauke da mutum 90 ciki har da mata da yara, da nufin zuwa gaisuwar rasuwa a Dugga.
“Wannan lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar ranar Talata, 2 ga Satumba, 2025, a sanadiyar lodin fasinjoji fiye da ƙima sannan kuma kwale-kwalen ya ci karo wani da kututturen itace.”
Ya ƙara da cewa jami’ai na ci gaba da aikin ceto domin gano waɗanda suka bace.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Neja Kwale kwale kwale kwale
এছাড়াও পড়ুন:
Al’ummar Kauru Sun Koka Game Da Karuwar Hare-hare Da Ke Barazana Ga Gonaki Da Rayuka
Daga Yusuf Zubairu Kauru
Al’ummar Karamar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna sun shiga halin kaka-ni-ka-yi duba da yadda rayukansu ke kasancewa cikin hadari yayin da suke gonakinsu.
A wata tattaunawa ta wayar tarho, wani jagoran matasa, Junaidu Ishaq, ya bayyana cewa kusan shekaru biyar ke nan da hare-haren ’yan bindiga ke ta faruwa akai-akai, wanda ya bar al’umma cikin fargaba da ƙuncin rayuwa.
Ya ce manoma suna shiga gonakinsu ne cike da fargaba domin komi na iya faruwa yayin da suke aiki a gonakin.
Mazauna yankin sun bayyana cewa Kauru, wadda aka fi sani da yawan gonaki da ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci a jihar Kaduna, yanzu manoma ba sa iya shiga gonakinsu cikin kwanciyar hankali saboda yadda ‘yan bindiga ke yawan kai musu hare-hare.
A koda yaushe iyayen yara suna fargaba kada ‘ya’yansu su yi nesa da su, yayin da iyalai da dama da ke fama da ƙangin talauci ke kara shiga cikin matsanancin hali.
Sun yi kira gwamnati da hukumomin tsaro su yi gaggawar kai ɗauki wanda zai bai wa manoman karkara kwarin gwiwa, waɗanda su ne ginshiƙin samar da abinci a yankin.
Mazaunan sun yi gargadin cewa idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, hare-haren na iya haifar da ƙaruwar matsalar rashin abinci da yawaitar ƙaura daga yankin.
“Idan zuwa gona zai sa mutumya rasa ransa, to lalle akwai babban matsala,” in ji wani manomi a yankin.
Sun yi fatan cewa za a dawo da zaman lafiya a yankin, yadda ƙasar da Allah Ya albarkace su da ita za ta ci gaba da ciyar da al’ummar Kauru ba wurin binne su ba.