Kotu ta ɗaure wani mutum kan kashe saurayin ’yarsa a Ekiti
Published: 3rd, September 2025 GMT
Wata kotu a Jihar Ekiti, ta tura wani mutum mai suna Ibrahim zuwa gidan yari bisa zargin kashe saurayin ’yarsa.
Rahotanni sun ce saurayin ya ziyarci budurwarsa a gidan mahaifinta da ke kusa da Corpers’ Lodge, a kan titin New Iyin, Ado Ekiti.
Da ina da iko da cikin mako biyu zan magance matsalar tsaron Zamfara – Gwamna ’Yan daba sun tarwatsa taron neman zaman lafiya na dattawan KatsinaMahaifin, wanda ba ya son dangantakaru, ya kira ’yan uwansa suka tare saurayin, inda suka yi masa dukan da ya yi sanadin mutuwarsa saboda zubar jini.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Sunday Abutu, ya tabbatar da gurfanar da mahaifin yarinyar.
Hakazalika, ya ce an gurfanar da wasu mutane biyu, kuma kotu ta tura su gidan yari yayin da ake ci gaba da shari’a.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Saurayi
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Ceto Wani Mutum Da Aka Sace A Taraba
Ana zargin mutumin da hannu wajen sace Alhaji Adamu.
Wanda ake zargin ya samu raunuka bayan jama’a sun yi masa duka kafin isowar sojoji, kuma an garzaya da shi asibiti, yayin da ake ci gaba da bincike.
Brigedi Janar Kingsley Chidiebere Uwa, kwamandan Rundunar 6, ya yaba da yadda sojoji, ‘yan sa-kai da mafarauta suka haɗa kai, yana mai cewa wannan haɗin kai ya taimaka wajen samun nasarar ceto wanda aka sace.
Ya kuma buƙaci jama’ar Taraba su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai da wuri domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA