Babban Taron Lauyoyi Na Kasa: Sarkin Musulmi Ya Gargadi Alkalai Kan Tabbatar Da Adalci
Published: 30th, August 2025 GMT
‘Kun kuduri aniyar kiyaye manyan ka’idojin bin doka domin tabbatar da cewa kowa, har da masu mulki, suna karkashin doka kuma ana iya daukar mataki a kansu. Idan muka yi haka, to mun magance tushen matsalar mulki a wannan kasa,’ in ji shi.
Sarkin Musulmi ya jaddada cewa adalci shi ne tubalin zaman lafiyar al’umma, kuma dole doka kullum ta kasance mai nufin cimma adalci a matsayin babbar manufarta.
Ya shawarci mahalarta taron da su yi amfani da wannan taro wajen tattauna muhimman batutuwan da suke tsara makomar Nijeriya.”
“Ya ce, ‘Ina fatan wannan taro zai ba ku damar tattauna batutuwan da suka shafi makomar al’ummarmu.
Abubuwa uku ne manya: Ci gaba da kokari wajen gyaran dokoki domin a hankali a kawar da tasirin mulkin mallaka a cikin dokokinmu tare da kusantar da su da kimominmu, al’adu da tarihimmu; magance batun adalcin zamantakewa domin rage gibin rashin daidaito tare da karfafa hadin kai; da kuma inganta samun damar zuwa kotu, musamman la’akari da tsadar shari’a da kuma yadda marasa karfi da masu rauni ake barinsu a baya.’
Ya yi tir da matsalar da Nijeriya ke fama da ita ta rashin aiwatar da manufofi yadda ya kamata duk da kasancewar manufofin “masu kyau kwarai.”
Doka da ilimi ba za a iya raba su ba.
A fannin sanin doka akwai sanin kima, kuma adalci na daya daga cikin manyan kimomin da doka ya kamata ta cimma,’ in ji Sarkin Musulmi wanda ya bayyana haka ga mahalarta taron, ciki kuwa har da shugaban jam’iyyar hamayya na Afirka ta Kudu, Julius Malema.”
Ra’ayin Lauya, da Kungiyoyin Fararen Hula Sun Bambanta Kan Maganar Sarkin Musulmi Game Da Alkalancin Nijeriya
Yayin da Nijeriya ke ci gaba da fama da tsarin shari’a mara inganci wanda ke bayyana gazawar kotuna wajen tabbatar da adalci, boye shaida, halayyar rashin da’a ta masu shari’a, cin hanci da rashawa, da tsoma bakin siyasa cikin tsarin shari’ar kasa, jama’a da dama sun nuna rashin yabonsu ga tsarin.
Wannan ra’ayi ne Sarkin Musulmi na Sakkwato, Muhammadu Sa’ad Abubakar, wanda ya jaddada a Taron Koli na Kungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) da aka gudanar a Enugu ranar Lahadi, inda ya yi gargadin cewa adalci a Nijeriya na kara zama ‘kayan ciniki,’ inda talakawa ke zama wadanda ake zalunta, kuma masu kudi ke fin karfin doka.”
Yayin da yake mayar da martani ga maganar wannan girmamaccen sarki, wani malamin lauya, Dr. Wahab Shittu (SAN), ya bayyana furucin Sultan a matsayin abin takaici kwarai kuma rashin adalci ga alkalan da ke jajircewa da aiki tukuru da kuma gaba daya bangaren shari’a.
Dr. Shittu ya ce, “Ikirarin cewa a Nijeriya ana iya sayen adalci wata fahimta ce kawai, ba gaskiya ba. Wannan kuwa rashin adalcin fahimta ne da kuma maganganun da ake ta yi a teburin shan shayi.”
“Ina ganin masu ruwa da tsaki a harkar gudanar da shari’a suna da babban alhaki na canza wannan labari. Ya kamata a samu adalci bisa cancantar shari’ar da aka gabatar, ba bisa wanda ya fi bayar da kud ba.”
Haka kuma, yayin da yake mayar da martani kan maganar Sultan Sa’ad Abubakar cewa adalci yana zama abin saye a Nijeriya, Kwamared Bankole Solomon (esk), shugaban Kungiyoyin Farar Hula (CSOs) da Kungiyoyin Goyon Bayan Dimokuradiyya a Jihar Ogun, ya yaba wa wannan fitaccen sarki bisa karfin gwiwar da ya nuna na fadin gaskiya kan wannan batu.
Bankole ya ce, “Abin takaici ne kwarai cewa mun kai ga shiga wannan mummunan hali a kasarmu.
“Ina tare da Sultan wajen cewa adalci yanzu na mai bayar da kudi ne, ko kuma in ce adalci a Nijeriya ya zama kayan sayarwa, domin idan ka ga abubuwan da ke faruwa, sai ka tausaya wa wannan kasa.
“Ina fada wa mutane cewa bisa ga abubuwan da muka gani da CSOs, ma ya fi sauki, arha da adalci akan bayar da cin hanci a matakin ‘yansanda; ko a ofishin ‘yansanda, ko a Area Command, ko kuma a hedikwatar jiha, fiye da a kotu, domin makudan kudi ake nema a kan saukakan matakai a kotu.”
“Wasu mutane za su saurare ka, su ji maganarka, kuma watakila su yi maka shaguben cewa ai wani ya bayar da kudin beli. Amma da za ka san irin abin da ake karba domin kammala wannan belin a kotu, za ka yi wa kasar nan kuka.”
Jeka Kotu, Maza Ka Garzaya Kotu
“Akwai wasu shari’o’in da idan aka fara su, wani lokaci za ka gaskata cewa lallai ba su da kyau, amma daga karshe idan ka ga sakamakon, za ka gane cewa tabbas wannan ba abin da ake tsammani daga bangaren shari’a ba ne. Shi ya sa yau a kasar nan ya zama magana ta kowa idan ka ji ana cewa:” “Jeka kotu”! Idan an sace maka dukiyarka, “jeka kotu”! Duk wanda ya kai maka hari, “je kotu”! Idan ka yi zargi ko ka yi hasashen dan siyasa ya sace dukiyar kasa, “jeka kotu”! Du kana fadar haka ne saboda sun san za su iya yin yadda suka ga dama idan shari’ar ta kai kotu.
Babu attajiri a gidan yari, talakawa kadai ake samu
“Don haka, ina son in yarda da Sultan cewa adalci yana zama kayan sayarwa; ta hanyar wanda ka sani da kuma yawan kudin da kake da shi! Kuma wannan shi ne abin da ake tattaunawa a yau, domin idan ka ziyarci Gidajen Gyaran Hali a fadin kasar nan, da wuya ka ga attajiri; da wuya ka ga babban dan siyasa; abin da za ka gani kawai talakawa ne wadanda saboda wani dalili ko wani ba su samu hanyar tsira ba, ko kuma ba su da hanya, ko rashin yin abu, ko dabaru da za su ba su damar sayen hanyar da za su fita.”
“A takaice, ba damuwar Sultan da sarakunan gargajiya kadai ba ce; har ma da bangaren CSOs ba su gamsu da abin da ke faruwa ba. Muna ziyartar kotuna muna sauraron labarai, kuma muna ganin wasu mutane da muka sani wadanda shari’unsu a fili suke cewa take hakkin su aka tauye, amma idan ka shiga kotu, yawanci hukuncin da za ka gani abin shakku ne.”
“Don haka, ba tare da boye magana ba, na yarda kuma na amince gaba daya da furucin Sultan Sa’ad Abubakar cewa adalci a wannan duniya kayan sayarwa ne tsantsa.”
Lauyoyi Sun Yi Kira da A Yi Hattara
Wasu lauyoyi sun nemi a dauki matakin gaskiya daga bangaren shari’a, inda suka yi gargadin cewa idanun kowa na kan bangaren shari’a domin ganin an yi adalci ba tare da tsoro ko son zuciya ba.
A cewarsu, ya zama dole harkar lauya ta sake samun girmamawar ‘yan Nijeriya ta hanyar yin abin da ya dace koyaushe.
Haka kuma sun yi kira da a yi hattara game da maganganun da ba su da tushe wadanda nufin su shi ne bata sunan bangaren shari’a.
Bangaren Shari’a Bai Yi Muni Kamar Yadda Ake Ambatawa Ba
Lauyan kundin tsarin mulki, Farfesa Isah Awo, ya ce Sultan na iya kuskure. Ya ce bangaren shari’a ba ya da muni kamar yadda jama’a ke ambatawa.
“Duk da cewa zan yarda cewa wasu shari’o’i da ke fitowa daga kotunmu na iya samun rashin daidaito, wannan kananan abu ne sosai don a iya cewa ana iya sayan adalci.
“Ban yarda cewa ana iya sayen adalci ba, kuma bangaren shari’a na Nijeriya bai kai kasa haka ba.
“Akwai lokuta da bangaren shari’a zai iya gazawa; zai iya gazawa kan yadda mutane ke tsammani, amma har yanzu bai lalace kamar yadda ake bayyana shi ba.”
Kada mu tsoratar da masu zuba jari na kasashen waje
A nasa bangare, wani lauya dake Abuja, Barrister Innocent Amokade, ya yi gargadi kan lalata bangaren shari’a.
Ya ce irin wadannan maganganun na iya rage amincewar masu zuba jari na kasashen waje a kasar.
Ya ce idan ‘yan Nijeriya ba su yarda da tsarin kasarsu ba, me kuke so ‘yan kasashen waje su yi?
“Muna bukatar mu yarda da tsarinmu domin hadari ne a sa ‘yan kasashen waje, musamman masu zuba jari, su yi imani cewa bangaren shari’armu ba mai zaman kansa ba ne. Wannan zai rage musu amincewa da ikonmu na yin adalci.”
Sarkin Sokoto, Mai Girma, Dr. Sa’ad Abubakar III, ne ya jagoranci bikin bude taron. Julius Malema, jagora mai jan hankali na kungiyar Economic Freedom Fighters ta Afirka ta Kudu kuma mamba na majalisar dokokin kasa, shi ne ya gabatar da jawabin babban mai jawabi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: bangaren shari a Sa ad Abubakar Sarkin Musulmi kasashen waje cewa adalci
এছাড়াও পড়ুন:
Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 75 na shekarar 2025, ga gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi 27.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa, wannan ƙarin kasafin kuɗi ya samo asali ne daga ƙarin kuɗaɗen shiga domin biyan buƙatun kuɗaɗen da suka taso, da kuma ƙarfafa manyan fannoni da za su kawo ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, majalisar ta amince da Naira Biliyan 58 ga gwamnatin jiha da kuma Naira Biliyan 17 ga Kananan Hukumomi 27, wanda ya shafi kashe-kashen kudade na yau da kullum da kuma manyan ayyuka.
Ya ce, wannan ƙarin kasafin kuɗin zai inganta ayyuka da tsare-tsare da ake gudanarwa a muhimman fannoni irin su ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa, noma da sauran muhimman ayyukan ci gaba.
Sagir ya ƙara da cewa, za a mika ƙarin kasafin kuɗin ga Majalisar Dokokin Jihar domin tattaunawa da amincewa da shi, kamar yadda kundin tsarin mulki da ka’idojin kasafi suka tanada.
Kwamishinan ya ƙara jaddada cewa, wannan mataki ya nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen gudanar da mulki bisa gaskiya da adalci, da kula da kuɗaɗen jama’a yadda ya dace, da kuma tabbatar da samar da ingantattun ayyuka ga al’ummar jihar baki ɗaya.
Usman Muhammad Zaria