Bankin AfDB zai zuba jarin $650m a Nijeriya a duk shekara
Published: 3rd, May 2025 GMT
Bankin Raya kasashen Afirka (AfDB) ya ware dala miliyan 650 a duk shekara tun daga 2025 zuwa 2030 domin wani shiri na musamman na habaka ci gaban tattalin arziki a Nijeriya.
Bankin ya sanar da hakan ne a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce za a samar da dala biliyan 2.95 tsawon shekara hudu a wannan shirin, inda zai samu ƙarin kimanin dala biliyan 3.
Sanarwar ta ce shirin zai mayar da hankali kan abubuwa biyu muhimmai wadanda suka hada da kawo ci gaba ma dorewa da samar da ababen more rayuwa wadanda suka zo daidai da tsarin da ake da shi na sauyin yanayi da samar da gasa da ci gaban masana’antu; da kuma samar da daidaito a tsakanin matasa da jinsi ta bangaren ci gaban masana’antu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Adadin Wuraren Cajin Ababen Hawa Masu Aiki Da Lantarki Na Sin Ya Karu Da 47.6% A Shekara
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp