Kudaden Da Ke Hannun Mutane Sun Ragu Zuwa Naira Tiriliyan 5 – Rahoto
Published: 25th, April 2025 GMT
Raguwar kudin a hannun mutane na iya zama wani bangare na kokarin rage matsin lamba kan hauhawar farashin kayayyaki da samun daidaiton tattalin arziki.
Baya ga raguwar kudade a hannun mutane, ajiyar a bankin CBN ya karu zuwa naira biliyan 28.52 a watan Maris na 2025, daga naira biliyan 27.57 a watan Fabrairun 2025.
A halin yanzu, ajiyar ko-ta kwana ba ta canza ba a naira miliyan 284.36 a cikin watanni uku.
Ajiyar banki yana nufin kudaden da Babban Bankin da bankunan kasuwanci ke rike da shi don tabbatar da hada-hadar kudade a cikin bangaren banki. Ci gaba da karuwar ajiyar bankuna wata alama ce ta kokarin CBN na tsare harkokin kudade da daidaita tattalin arziki.
Ya daidai wannan lokacin a bara, an bayyana cewa darajar kudin Nijeriya da ke yawo a hannun mutane ya karu zuwa naira tiriliyan 3.87 a karshen watan Maris na 2024.
Wannan ya nuna karuwa daga naira tiriliyan 3.69 a watan Fabrairu da naira tiriliyan 3.65 a watan Janairu. Bugu da kari, kudin da ke wajen bankuna kuma ya karuwa a cikin kwata na farko, ya karu daga naira tiriliyan 3.28 a watan Janairu zuwa naira tiriliyan 3.41 a watan Fabrairu, kuma ya kai naira tiriliyan 3.63 a watan Maris.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: naira tiriliyan 3
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka ta sake laftawa wasu kamfaninin mai na Iran takunkumi
Amurka ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu kamfanoni 7 da ta ce suna da hannu wajen siyar da man kasar Iran, a wani mataki na kara matsin lamba duk da tattaunawar da aka yi kan shirin nukiliyar Iran.
Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar ta ce, bangarorion da takunkumin ya shafa sun hada da kamfanonin kasuwanci guda biyar, hudu da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, daya kuma a kasar Turkiyya, wadanda suka sayar da albarkatun man fetur na kasar Iran ga kasashe uku, da kuma wasu kamfanonin jigilar kayayyaki guda biyu.
A cikin sanarwar da sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka Marco Rubio ya fitar, ya ce “Matukar dai Iran na son samar da kudaden shiga na man fetur da sinadarai don samar da kudaden gudanar da ayyukanta na tabarbarewar zaman lafiya, da kungiyoyin da ya bayyana da na ta’addanci to Amurka za ta dauki matakin laftawa Iran da dukkan kawayenta alhakin kaucewa takunkumi.”
Matakin na zuwa ne jim kadan bayan Iran ta sanar da cewa za a sake gudanar da zagaye na hudu na tattaunawa da gwamnatin shugaba Donald Trump a birnin Rome a ranar Asabar 3 ga watan Mayu a karkashin jagorancin kasra Oman.