Matar da aka haifa ‘babu mahaifa’ ta haihu
Published: 23rd, April 2025 GMT
Rahotanni sun bayyana cewa, an haifi wata ‘yar baiwa a Birtaniya ba tare da mahaifa ba.
Mahaifiyar jaririyar mai suna Grace Davidson, mai shekara 36, tun farko an haife ta ne ba tare da mahaifar da za ta iya renon ciki ba.
Hajjin Bana: Kamfanoni 4 da za su yi jigilar maniyyata — NAHCON An daƙile yunƙurin juyin mulki a Burkina FasoA shekara ta 2023 ’yar’uwarta ta ba ta gudunmawar mahaifa – lamarin da ya zamo karo na farko a Birtaniya da aka yi dashen mahaifa cikin nasara.
Shekara biyu bayan wannan dashe, Grace ta haifi ɗiyarta ta farko a watan Fabarairun da ya gabata.
Ita da mijinta Angus, mai shekara 37 sun sanya wa jaririyar suna Amy, wato sunan yayar Grace, wadda ita ce ta bai wa ’yar’uwar tata mahaifar.
Grace mahaifiyar Amy, mai nauyin kilo biyu ta ce, ba za ta iya bayyana irin farin cikin da take ji sakamakon zama uwa a karon farko.
Grace da mijinta Angus, waɗanda ’yan asalin Scotland ne, amma suna zaune a birnin Landan, na sa ran samun haihuwa ta biyu nan ba da jimawa ba da mahaifar da aka ba su gudunmawa.
A farko, ma’auratan ba su so, su fito fili, su bayyana kansu ba, amma bayan haihuwar Amy, sun yanke shawarar tattaunawa da BBC kan abin da suka kira “ ‘yar baiwa”.
Likitocin da suka yi wa Grace aikin dashen mahaifar sun ce, sun kara yin irin wannan dashe sau uku ta hanyar amfani da mahaifar mutanen da suka mutu, tun bayan aikin da suka yi wa Grace.
Sun ce, suna sa ran yin dashen maihaifa 15 a matakin gwaji.
An haifi Grace ne da wata lalura da ba a cika samu ba, wadda ake kira MayerRokitansky-Küster-Hauser (MRKH) syndrome, inda mace kan zo babu mahaifa kwatakwata ko kuma ko da akwai mahaifar ba cikakkiya ba ce, sai dai sukan zo da kwayayan haihuwa.
A karon farko da BBC ta tattauna da ita a shekarar 2018, Grace na sa ran mahaifiyarta za ta ba ta mahaifarta domin ta samu damar haihuwa – sai dai daga baya an gano cewa, mahaifar mahaifiyar tata ba ta yi daidai da jikin Grace ba.
A shekarar 2019, BBC ta sake tattaunawa da Grace da mijinta Angus, lokacin da ake auna ’yar’uwar Grace, wato Amy Purdie, domin gano ko mahaifarta za ta yi wa Grace.
Amy da mijinta sun riga sun haifi ‘ya’ya biyu, kuma ba su da bukatar kara haihuwa.
An zaunar da ’yan’uwan biyu, inda aka yi masu bayani dalladalla gabanin tiyatar dashen mahaifar.
Grace ta ce, an yi mata tayin amfani da tsarin dakon juna-biyu ko kuma ta karbi rikon yara, amma sai ta ga daukar jinjirin da ta rena a cikinta “abu ne mai matukar muhimmanci”.
“Na kasance ina son zama uwa,” in ji ta, “amma sai na rika dannewa a raina saboda halin da nake ciki.”
Haihuwa ta farko da aka samu bayan yin dashen mahaifa a duniya ta faru ne a kasar Sweden a shekarar 2014.
Tun daga wancan lokacin an yi dashen mahaifa kimanin sau 135 a fiye da kasashe 10, ciki har da Amurka da China da Faransa da Jamus da Indiya da kuma Turkiyya.
Haka kuma an haifi jarirai kimanin 65 bayan dashen. Kimanin likitoci 30 ne suka yi aiki a kan Grace lokacin dashen mahaifar da aka yi mata a watan Fabarairun 2023, inda suka kwashe sa’o’i 17 suna aikin cire mahaifar daga jikin Amy tare da mayar da ita jikin Grace.
An haifi jaririya Amy ne ta hanyar tiyata a asibitin Kueen Charlotte’s da ke yammacin birnin Landan a ranar 27 ga watan Fabarairu.
Grace da Angus sun ce, suna sa ran samun da na biyu – da zarar jami’an lafiya sun ce masu za ta iya sake ɗaukan ciki.
Za a cire mahaifar da zarar Grace ta haihu sau biyu.
Hakan zai bai wa Grace damar daina shan maganin da take yi a kullu-yaumin, wanda ke hana jikinta botsare wa mahaifar da aka dasa mata.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Birtaniya Grace Davidson Haihuwa mahaifar da
এছাড়াও পড়ুন:
An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da Portugal
An dawo da wutar lantarki a safiyar Talatar nan a Sifaniya da Portugal bayan katsewar da aka samu ta sa’o’i wadda ita ce mafi muni da aka gani a Turai.
A jiya Litinin ce dai miliyoyin mutane suka auka cikin duhu bayan ɗaukewar wutar lantarkin a ƙasashen biyu wadda ke ci gaba da ɗiga ayar tambaya kan abin da ya haifar da ita.
Za a rataye wani soja saboda laifin kashe budurwarsa Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a ChibokKafofin watsa labarai sun ruwaito cewa ɗaukewar wutar lantarkin ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama da na ƙasa da katse hanyoyin sadarwa ta wayar hannu da kuma rufe na’urorin cire kuɗi na ATM a duk faɗin ƙasashen biyu.
Wata sanarwa da hukumar samar da wutar lantarki a Spain ta Red Electrica ta fitar, ta ce da misalin ƙarfe 7 na safiya agogon ƙasar, an samu nasarar dawo da sama da kashi 99 na wutar lantarki a ƙasar.
Haka nan ita ma takwararta ta Portugal ta ce tun cikin daren jiya Litinin, aka dawo da wutar lantarkin da dukkanin tashoshin wutar ƙasar guda 89.
Bayan ɗauke wutar da aka samu a Spain, jami’an ba da agajin gaggawa sun sanar da nasarar kuɓutar da mutane dubu 35 da suka maƙale a jiragen ƙasa na ƙarƙashin ƙasa.
Har yanzu dai hukumomi ba su bayyana dalilin da ya sa aka samu ɗaukewar wutar lantarkin ba, wanda shi ne karo na biyu da irin wannan mummunar katsewar wutar lantarki ta faru a Turai cikin watanni