HausaTv:
2025-05-01@01:10:54 GMT

Iran da Amurka na shirin tattaunawa ta biyu a birnin Rome

Published: 19th, April 2025 GMT

Yau Asabar Washington da Tehran, ke tattauanwa a birnin Rome na kasar Italiya, wace ita ce ta biyu a shiga tsakanin kasar Oman kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya.

Tattaunwar wacce ba ta gaba-da-gaba ba an gudanar da irin ta a ranar Asabar data gabata a birnin Muscat na kasar Oman, inda bangarorin biyu suka bayyana tattaunawar da mai armashi.

Gabanin tattaunawar ta yau, Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce akwai yuwuwar kulla yarjejeniya da Amurka idan har Washington ba ta gabatar da wasu bukatu na da suka wuce da tunani ba”.

Araghchi ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwaransa na Rasha, Sergei Lavrov, a ranar Juma’a a birnin Moscow, gabanin tattaunawar ta biyu tsakanin Tehran da Washington, da ake shirin gudanarwa yau a birnin Rome na kasar Italiya.

“Za mu tattauna kan batun nukiliya ne kawai, kuma ba za a saka wasu batutuwa a cikin wannan tattaunawar ba,” in ji shi.

Ya kara da cewa “Ina ganin mai yiyuwa ne a cimma matsaya idan [Amurkawa] suka nuna da gaske su ke kuma ba su gabatar da bukatu da ba su dace ba.

Sai dai ya jaddada cewa: “Hanyar diflomasiya a bude take, amma ya nuna matukar shakku game da aniyar Amurka idan aka yi la’akari da matsayin Washington da ke cin karo da juna.

“Muna da matukar shakku game da aniya da manufar bangaren Amurka, amma za mu shiga shawarwarin tare da azama.”Ya kuma jaddada aniyar Tehran ta ci gaba da samar da hanyoyin warware shirinta na nukiliya cikin lumana.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Amurka ta sake laftawa wasu kamfaninin mai na Iran takunkumi

Amurka ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu kamfanoni 7 da ta ce suna da hannu wajen siyar da man kasar Iran, a wani mataki na kara matsin lamba duk da tattaunawar da aka yi kan shirin nukiliyar Iran.

Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar ta ce, bangarorion da takunkumin ya shafa sun hada da kamfanonin kasuwanci guda biyar, hudu da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, daya kuma a kasar Turkiyya, wadanda suka sayar da albarkatun man fetur na kasar Iran ga kasashe uku, da kuma wasu kamfanonin jigilar kayayyaki guda biyu.

A cikin sanarwar da sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka Marco Rubio ya fitar, ya ce “Matukar dai Iran na son samar da kudaden shiga na man fetur da sinadarai don samar da kudaden gudanar da ayyukanta na tabarbarewar zaman lafiya, da kungiyoyin da ya bayyana da na ta’addanci to Amurka za ta dauki matakin laftawa Iran da dukkan kawayenta alhakin kaucewa takunkumi.”

Matakin na zuwa ne jim kadan bayan Iran ta sanar da cewa za a sake gudanar da zagaye na hudu na tattaunawa da gwamnatin shugaba Donald Trump a birnin Rome a ranar Asabar 3 ga watan Mayu a karkashin jagorancin kasra Oman.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Araghchi : Za’ayi Tattaunawar Iran da Amurka ta gaba a Rome bayan taron E3
  • Amurka ta sake laftawa wasu kamfaninin mai na Iran takunkumi
  • Xi Ya Jaddada Muhimmancin Tsara Nagartaccen Shirin Raya Tattalin Arziki Da Zamantakewar Al’umma Tsakanin 2026-2030
  • Iran Da Iraki Sun Ce An Kammala Shimfida Layin Dogo Daga Shalamcheh Zuwa Basra
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kutsa Cikin Quneitra Na Kasar Siriya Tare Da Kafa Shingen Bincike
  • Shugaban Putin Na Rasha Ya Bada Sanarwan Tsagaita Wuta Da Ukraine Na Sa’o’ii 72
  • Babu Wata Tattaunawa Tsakanin Sin Da Amurka Game Da Batun Haraji
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Ci Gaba Da Killace Gaza Da Kashe Mutane, Laifi Ne Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA
  • Takht Ravanji: Iran Ba Za Ta Taba Yin Tattaunawa Akan Dakatar Da Tace Sanadarin Uranium Ba