Yadda Tinubu ya taimaka wa ’yata ta samu aiki NUPRC — Buba Galadima
Published: 10th, April 2025 GMT
Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana yadda Shugaba Bola Tinubu, ya taimaki ’yarsa ta samu aiki a Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa (NUPRC).
Galadima, ya bayyana haka ne yayin wani shiri a gidan talabijin na AIT.
Matatar Ɗangote ta rage farashin fetur zuwa N865 Yadda masu safarar ɗan Adam ke yaudarar mutane ta intanetYa ce duk da yana yawan sukar gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki, har yanzu shi da Shugaba Tinubu abokai ne.
Ya ce: “Abokai ne mu kuma za mu ci gaba da zama abokai. Idan ina buƙatar wani abu daga gare shi, zan iya tambayarsa.
“Bari na faɗi gaskiya a idon duniya. ’Yata ce ta yi amfani da wayata ta kira Shugaban Ƙasa, shi kuma ya yi zaton ni ne. Sai suka ce ’ya’yana ne, suka sanar da shi al’amura sun yi tsanani.”
Ya ƙara cewa: “Sun faɗa wa Tinubu cewa ‘mahaifinmu ba zai iya wannan ba, amma ya faɗa mana kai abokinsa ne.’
“Ɗaya daga cikinsu ta ce ta kammala NYSC amma ba ta samu aiki a NUPRC wacce Gbenga Komolafe ke jagoranta.
“Tinubu ya ‘kira Komolafe, ya ce ku bai wa ’yar abokina aiki.’ Shi ya sa ta ke son zuwa Makkah don yi wa Allah da Shugaban Ƙasa godiya.”
Galadima ya kuma bayyana cewa ’yarsa ta yi aiki a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na tsawon shekara huɗu ba tare da an taɓa biyanta albashi ba.
Ya ce: “’Yata ta yi aiki da shi (Buhari) har na tsawon shekara huɗu, kuma ya bayar da umarnin kada a biya ta albashi.
“Sai dai duk wata a kawo takardar da ke nuna an biya ta. Ta yi aiki da Buhari shekara huɗu a ofishin Osinbajo ba tare da ta karɓi ko sisin kwabo ba,” in ji shi.
Galadima, ya kuma ce shi kansa ya yi aiki tare da Buhari na tsawon shekara goma sha uku.
Wannan kalamai sun bai wa mutane da dama mamaki, musamman ganin cewa Galadima ya shahara wajen sukar gwamnatin APC a fili.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Jagora: Sojojin Iran ba zasu sararawa Isra’ila ba
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce sojojin kasar Iran ba za su sararawa gwamnatin Isra’ila ba.
Jagoran ya bayyana hakan ne a wani sakon bidiyo ga al’ummar Iran ranar Juma’a biyo bayan hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ta yi kan kasar wanda ya kashe fararen hula, masana kimiyya da kwamandojin soji.
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa gwamnatin Isra’ila ba za ta kubuta daga wannan aika-aika ba, yana mai tabbatar wa al’ummar Iran cewa ba za a yi sakaci kan hakan ba.
Jagoran ya jaddada cewa muguwar gwamnatin sahyoniya ta tafka babban kuskure, sannan kuma shelanta yaki ne kan Iran.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: dukkanin jami’an kasar Iran da bangarori daban-daban na siyasa da kuma al’ummar Iran suna da ra’ayi daya dangane da wajabcin daukar wani mataki mai karfi wajen tunkarar gwamnatin sahyoniya ta ‘yan ta’adda.
Jagoran ya kara da cewa, bai kamata gwamnatin Isra’ila ta yi tunanin cewa ta ci bulus ba, kuma komi ya wuce.