Amurka Ta Ƙara Wa Kayayyakin China Haraji Zuwa Kashi 104
Published: 9th, April 2025 GMT
Ta kuma ce har yanzu ƙasashe sama da 70 daga sassa daban-daban na duniya sun tuntuɓi Amurka domin a yi tattaunawa kan yadda sabbin harajin ke shafar kasuwanci a duniya.
Mene ne Ma’anar Wannan Haraji?Wannan haraji na nufin idan ana shiga da kaya daga China zuwa Amurka, za a ƙara musu kuɗi sosai kafin su isa kasuwannin Amurka.
Wannan zai iya sa farashin kayan ya tashi a kasuwa, kuma zai iya janyo taƙaddama a tsakanin Amurka da China, waɗanda su ne manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki a duniya.
Me Ya Sa Wannan Ke Da Muhimmanci?Wannan rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da China na iya shafar farashin kayayyaki a duniya, musamman a ƙasashen da ke dogaro da kayayyakin da ake ƙera su a China ko Amurka.
Sannan zai iya janyo sauyin hanyoyin cinikayya da shigo da kaya, wanda zai shafi kamfanoni da masu siye da kaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Haraji
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Taya Amusan Da Gumel Murnar Samun Nasarori A Ɓangarori Daban-daban
Shugaban ya yaba da abinda ya kira kwarewa da juriya irin na Amusan, tare da cewa aikinta ya sake misalta irin daukakar da yan Nijeriya za su iya samu ta hanyar aiki tukuru da nuna kwazo, Tinubu ya yi fatan Gumel da Amusan su ci gaba da samun nasara a ayyukansu tare da ba su tabbacin gwamnati za ta ba su cikakken goyon baya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp