Turji ya kusa komawa ga mahallici – Sojoji
Published: 4th, April 2025 GMT
A ranar Alhamis ɗin nan ne rundunar sojin Nijeriya ta ce ana cigaba da farautar ƙasurgumin ɗanbindiga, Kachalla Bello Turji wanda sojojin ƙasar suka daɗe suna nema ya kusa komawa ga mahalicci.
Rundunar ta bayyana cewa kuma kwanakinsa sun kusa ƙarewa.
Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta miƙa Janar Tsiga da wasu ga NSA Gobara ta tashi a Jami’ar Northwest da ke KanoTa kuma yi watsi da iƙirarin da ake na cewa sojoji sun rage kai hare-hare kan makiyaya, ’yan bindiga, ɓarayin shanu da sauransu, inda ta ƙara da cewa za ta ci gaba da mayar da hankali wajen kame Turji.
Wannan na zuwa ne kimanin kwana ɗaya bayan Turji ya kashe manoma 11 a garin Lugu da ke ƙaramar Isa ta Jihar Sokoto
An samu rahoton Turji yana dawowa ne daga ziyarar Sallah da ya kai wata unguwa a Isa, lokacin da ya kai harin.
Da yake amsa tambayoyi daga ‘yan jarida a hedikwatar tsaro a yayin ganawa da manema labarai, daraktan watsa labaran na rundunar tsaro ta Najeriya, Manjo Janar Markus Kangye, ya ce za su iya ci gaba da farauta tare da ganin bayan manyan ’yan bindiga da ke cikin dazukan ƙasar nan.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Rundunar Sojoji
এছাড়াও পড়ুন:
An gabatar da kundin dokar hana cin zarafin mata a Gombe
A ƙoƙarinta na daƙile cin zarafin mata da yara, Ma’aikatar Harkokin Mata ta Jihar Gombe, ƙarƙashin jagorancin Kwamishina Asma’u Mohammed Iganus, ta gabatar da kundin dokar hana cin zarafi mata (GBV) ga Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Dokta Abubakar Shehu Abubakar III, domin samun goyon bayan sarakunan gargajiya wajen aiwatar da dokar a matakin ƙasa.
Taron da aka gudanar a zauren Ƙaramar Hukumar Gombe ya samu halartar manyan jami’ai, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma.
LP za ta ceto Nijeriya daga halin da APC ta jefa ta — Nenadi Usman Rashin abinci mai gina jiki ya kashe yara 650 a Katsina — MSFA wajen taron, Kwamishinar ta jaddada cewa dokar na buƙatar goyon bayan al’umma gaba ɗaya, musamman sarakunan gargajiya, waɗanda ke da tasiri wajen sauya tunanin jama’a da inganta tarbiyya.
Da yake karɓar daftarin dokar a madadin Sarkin Gombe, Ɗan Lawan Gombe, Dokta Sani Adamu Jauro, ya bayyana cikakken goyon bayan Masarautar Gombe kan wannan dokar.
Ya ce, “Mai Martaba na tare da wannan yunƙuri, kuma masarauta za ta haɗa kai da gwamnati da ƙungiyoyi wajen kare haƙƙin mata da yara.”
A nata jawabin, Kwamishina Asma’u Mohammed Iganus ta bayyana cewa, “Sarakunan gargajiya suna da matuƙar muhimmanci a wannan yaƙi, domin suna da ikon canza dabi’u da kuma tabbatar da bin doka a cikin al’umma.”
Shugaban Kwamitin Majalisar Dokokin Gombe kan Harkokin Mata, Mista Gabriel Galadima, ya tabbatar da cewa an fara aiwatar da dokar bayan Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya rattaba hannu a kanta.
Ya ce, “Wannan doka ta shafi kowa da kowa wadda ba sani ba sabo ce kuma babu wanda zai tsallaka ta.”
Shi ma, Shugaban Karamar Hukumar Gombe, Barrista Sani Ahmad Haruna, ya nuna goyon bayansa kan dokar tare da alƙawarin wayar da kai, tallafa wa waɗanda abin ya shafa, da kuma inganta sauyin dabi’u a cikin al’umma.