Miliyoyin mutane sun gudanar da jerin gwanon ranar Qudus
Published: 28th, March 2025 GMT
Miliyoyin al’umma daga sassa daban daban na duniya sun gudanar da jerin gwanon zagayowar ranar Kuds ta duniya wacce ta gudana yau.
An dai kebance ranar ce domin nuna goyan baya ga al’ummar falasdinu, kuma ana gudanar da ita ne a ko wacce Juma’ar karshe ta watan ramadana bisa fatawar jagoran juyin juya halin musulinci na Iran Ayatollah Khumeiny.
A Iran ma kamar sauren sassan duniya jama’a sun fito kan tituna domin gudanar da bukukuwan ranar Qudus ta duniya, inda suke bayyana goyon bayansu ga Falasdinawa tare da yin tir da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza.
An kuma yi irin wannan gangamin a kasashe da dama na yankin yammacin Asiya da suka hada da Iraki da Yemen da Lebanon da kuma wasu da dama a fadin duniya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Ci Gaba Da Killace Gaza Da Kashe Mutane, Laifi Ne Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ci gaba da killace Gaza da kuma kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, laifi ne da ba a taba yin irinsa ba a tarihin dan Adam
A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badar Abdel Ati a yammacin jiya Lahadin da ta gabata, Araqchi ya bayyana ci gaba da killace yankin Gaza da rashin abinci da magunguna, tare da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, a matsayin wani laifi da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin dan Adam. Ya dauki Amurka da sauran masu goyon bayan ‘yan sahayoniyya a matsayin masu hannu a kisan kiyashi da laifukan yaki da ake aikatawa a Gaza.
Ministan harkokin wajen na Iran ya jaddada wajibcin tunkarar muggan manufofin yahudawan sahayoniyya na tilastawa al’ummar Gaza da yammacin kogin Jordan yin hijira daga muhallinsu, yana mai bayyana halin ko in kula da kasashen duniya suke nun awa kan wadannan laifuka a matsayin abin mamaki da damuwa.
Araghchi ya kuma yi wa takwaransa na Masar bayani kan ci gaban tattaunawar Iran da Amurka kan Shirin makamashin nukiliya na zaman lafiya da ake takaddama a kai tsawon shekaru.